< 以西結書 32 >

1 十一年十二月一日,上主的話傳給我說:「
A shekara ta goma sha biyu, a wata na goma sha biyu a rana ta fari, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 人子,你要唱哀歌追悼埃及王法郎,向他說:你曾自比作列國的雄獅,其實你卻似海中的鱷魚,衝入你的河中,用爪攪混了水,弄污了河流。
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.
3 吾主上主這樣說:我要藉列國的聯軍向你張開我的羅網,用我的往把你拖上來。
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Da taron jama’a masu yawa zan jefa abin kamun kifi a kanka, za su kuwa jawo ka da abin kamun kifi.
4 我要把你丟在地上,拋在田野間,使天上的各種飛鳥落在你身上,使地上的各種野獸吃你個飽。
Zan jefar da kai a ƙasa zan jefa ka a fili. Zan sa dukan tsuntsayen sararin sama su zauna a kanka dukan namun jeji na duniya kuma za su ƙosar da kansu a kanka.
5 我要把你的肉丟在山上,用你的屍首填滿山谷,
Zan baza namanka a kan duwatsu in kuma cika kwaruruka da gawarka.
6 用你的流汁灌溉大地,以你的血灌溉至山邊,以你的腐屍填滿溝壑。
Zan jiƙa ƙasar da jininka mai gudu har zuwa duwatsu, magudanan ruwa za su cika da namanka.
7 當你被消滅時,我要遮蔽天空,使星辰也昏暗;以雲彩遮住太陽,使月亮不放光明。
Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu; zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.
8 我要使天上一切照在你身上的光體變為黑暗,使黑暗籠罩你的國土──吾主上主的斷語--
Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka; zan kawo duhu a kan ƙasarka, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9 當我在列國把你滅亡的消息,傳到你不認識的國家時,我要使許多民族心神憂傷。
Zan dami zukatan mutane masu yawa sa’ad da na kawo maka hallaka a cikin al’ummai, a cikin ƙasashen da ba ka taɓa sani ba.
10 當我在他們面前揮動我的刀劍時,我要使許多民族,為了你而驚駭,使她們的君王驚惶失措;在你傾覆之日,他們每人都為自己的性命而戰慄,
Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu. A ranar fāɗuwarka kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa.
11 因為吾主上主這樣說:巴比倫王的刀劍必臨於你。
“‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Takobin sarkin Babilon zai auko maka.
12 我必使你的民眾喪身在眾英雄,即列國中最兇殘之人的刀下;他們必要破壞埃及的光華,消滅她的民眾。
Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane, masu bantsoro na dukan al’ummai. Za su lalatar da girman kan Masar, su kuma tumɓuke dukan jama’arta.
13 我要從大水之旁,把她所有的牲畜滅絕,人腳不再攪混此水,獸蹄也不再使水混濁;
Zan hallaka dukan dabbobinta da suke kusa da ruwaye masu yawa ƙafar mutum ba zai ƙara damunsa ko kofaton dabba ya gurɓata shi.
14 那時,我要澄清他們的水,使他們的河徐徐流下如油一般──吾主上主的斷語──
Sa’an nan zan sa ruwanta su kwanta in sa rafuffukanta su gudu kamar mai, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15 當我使埃及地荒蕪,使其他所有的一切荒廢,打擊其中所有居民時,他們必要承認我是上主。
Sa’ad da na mai da Masar kufai na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi, sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’
16 這是列國女子所要唱的哀歌,她們詠唱此歌憑弔埃及其人民──吾主上主的斷語。」
“Wannan ne makokin da za a yi mata.’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
17 十二年一月十五日,上主的話傳給我說:「
A shekara ta goma sha biyu, a rana ta goma sha biyar ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
18 人子,你要哀悼埃及的民眾,因為我要將她和各強國的女兒推入陰間,同已下到陰府的人在一起。 (questioned)
“Ɗan mutum, yi kuka saboda jama’ar Masar ka kuma tura ta da’yan matan manyan al’ummai zuwa ƙarƙashin ƙasa, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
19 你比誰更華美呢﹖你下去罷! 同未受割損的人臥在一起罷!
Ka ce, ‘Kin fi sauran tagomashi ne? Ki gangara, ki kwanta cikin marasa kaciya.’
20 他們必倒在喪身刀下的人中,刀已交出,必使她和她的群眾一起喪亡。
Za su fāɗi cikin waɗanda aka kashe da takobi. Takobin da an zāre; bari a ja ta a tafi tare da dukan jama’arta.
21 最英勇的戰士和她的同盟,必從陰府中論及她說:他們也下來了,同未受割損的人,同那些喪身刀下的人,臥在一起。 (Sheol h7585)
Daga cikin kabari manyan shugabanni za su yi maganar Masar da abokanta su ce, ‘Sun gangara sun kuma kwanta da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.’ (Sheol h7585)
22 在那裏有亞述,她的民眾都圍繞著她的墳墓:他們都是被殺而喪身刀下的。
“Assuriya tana can tare da dukan sojojinta; an kewaye ta da kaburburan dukan waɗanda aka kashe, dukan waɗanda suka mutu ta wurin takobi.
23 他們的墳墓位於極深的坑中,她的民眾圍繞著她的墳墓:他們都是被殺而喪身刀下的,他們曾在活人地上,散布過恐怖。
Kaburburansu suna cikin zurfafan rami kuma sojojinta suna kwance kewaye da kabarinta. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun mutu, an kashe su da takobi.
24 在那裏有厄藍,她的民眾都圍繞著她的墳墓:他們都是被殺而喪身刀下的,未受割損而降入陰間的;他們曾在活人地上,散布過恐怖,所以他們與已下到深淵的人一同蒙受羞辱。 (questioned)
“Elam tana can, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu sun mutu, an kashe su da takobi. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun gangara wurin marasa kaciya a duniyar da take ƙarƙashi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
25 在喪亡者中為她安置了床榻,她的民眾圍繞著她的墳墓:他們全是未受割損,喪身刀下的,因為他們曾在活人地上,散布過恐怖,所以被安置在被殺的人中,與已下到深淵的人一同蒙受羞辱。
An yi mata gado a cikin matattu, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi. Domin tsoronsu ya bazu cikin ƙasar masu rai, suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami; an kwantar da su tare da waɗanda aka kashe.
26 在那裏有默舍客和突巴耳,她們的民眾都圍繞著她們的墳墓:他們全是未受割損,喪身刀下的;他們曾在活人地上散布過恐怖。
“Meshek da Tubal suna can, tare da dukan jama’arsu kewaye da kaburburansu. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi domin sun haddasa tsoronsu a ƙasar masu rai.
27 他們不得與古代已死的英雄臥在一起,這些人帶著武器降入陰府,人們把他們的刀劍放在他們頭下,盾牌放在他們的骨骸上,因為他們曾在活人地上,散布過恐怖。 (Sheol h7585)
Ba sun kwanta tare da sauran jarumawa marasa kaciyan da aka kashe, waɗanda suka gangara kabari tare da makaman yaƙinsu, waɗanda aka yi musu matashin kai da takubansu ba? Hukuncin zunubansu yana a bisa ƙasusuwansu, ko da yake tsoron waɗannan jarumawa ya manne cikin ƙasar masu rai. (Sheol h7585)
28 至於你,你要臥在未受割損的人中,同喪身刀下的人在一起。
“Kai kuma, ya Fir’auna, za a kakkarye ka za ka kuma kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.
29 在那裏有厄東和她的君王,以及她所有的首長,他們雖然英勇,卻同喪身刀下的人被安置在一起,同未受割損而下到深淵的人臥在一起。
“Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
30 在那裏有北方的一切首領和所有的漆冬人,他們雖然英勇,令人驚駭,也同被殺者一起下去了;他們同未受割損的人和喪身刀下的臥在一起,與已下到深淵的人一同蒙受羞辱。
“Dukan yerima arewa da dukan Sidoniyawa suna can; sun gangara tare da waɗanda aka kashe cikin kunya duk da tsoron da suka haddasa ta wurin ikonsu. Sun kwanta tare da marasa kaciya tare da waɗanda aka kashe da takobi suna kuma shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
31 法郎看見那些人,便為自己所有的人民,感到安慰,因為法郎和他的軍隊也都是喪身刀下的──吾主上主的斷語──
“Fir’auna, shi da dukan sojojinsa, za su gan su zai kuma ta’azantu domin dukan jama’arsa da aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
32 因為他曾在活人地上,散布過恐怖,所以法郎和他所有的人民,也都要臥在未受割損的人中,與喪身刀下的人在一起──吾主上主的斷語。」
Ko da yake na sa ta haddasa tsoro a ƙasar masu rai, Fir’auna da dukan jama’arsa za su kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

< 以西結書 32 >