< 歌羅西書 1 >

1 因天主的旨意作基督耶穌的宗徒的保祿與弟茂弟兄,
Bulus manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah da Timoti dan'uwanmu,
2 致書給在哥羅森的聖徒及在基督內忠信的弟兄, 恩寵與平安由天主我們的父賜與你們!
zuwa ga masu bada gaskiya da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Bari alheri da salama su kasance tare da ku daga wurin Allah Ubanmu.
3 我們在祈禱時,常為你們感謝我們的主耶穌基督的天主和父,
Muna godiya ga Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kuma kullum muna addu'a dominku.
4 因為我們聽說:你們在基督耶穌內的信德,和你們對眾徒所有的愛德:
Mun ji bangaskiyar ku cikin Almasihu Yesu da kaunar da kuke da ita wa dukan kebabbu ga Allah.
5 這是為了那在天上給你們存留的希望,對這希望你們由福音真理的宣講人早已聽過了。
Kuna da kaunar nan domin bege na hakika ga abin da aka tanadar maku a sama. Kun riga kun ji game da begen nan na hakika maganar gaskiya da bishara,
6 這福音一傳到你們那裏,就如在全世界上,不斷結果,並在真理內認識了天主的恩寵那天以來,也是一樣;
wanda ta zo maku. Wannan bishara tana ba da yaya tana kuma hayayyafa da kuma girma a cikin dukan duniya. Tana yin haka a cikinku kuma tun ranar da kuka ji ta kun kuma yi koyi game da alherin Allah cikin gaskiya.
7 這福音也是由我們親愛的同僕厄帕夫辣所學的,他為你們實在是基督的忠僕役,
Wannan itace bishara kamar yadda kuka koye ta a wurin Abafaras, kaunataccen abokin bautar mu, wanda ke amintacce mai hidimar Almasihu a madadin mu.
8 也就是他給我們報告了聖神所賜與你們的愛。
Abafaras ya bayyana mana kaunarku a Ruhu.
9 為此,自從我們得到了報告那天起,就不斷為你們祈禱,懇求天主使你們對祂的旨意有充分的認識,充滿各種屬神的智慧和見識,
Saboda da wannan kauna, tun daga ranar da muka ji haka, ba mu fasa yi maku addu'a ba. Muna ta roko domin ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima da fahimta ta ruhaniya.
10 好使你們的行動相稱於天主,事事叫祂喜悅,在一切善功上結出果實,在認識天主上護得進展,
Muna ta addu'a domin ku yi tafiya da ta cancanci Ubangiji a kowace hanya da za ta faranta masa rai. Muna ta addu'a cewa za ku ba da 'ya'ya cikin kowanne aikin nagari kuma za ku yi girma cikin sanin Allah.
11 全力加強自己,賴他光榮的德能,含忍容受一切,欣然
Muna addu'a ku karfafa a cikin kowanne iyawa bisa ga ikon daukakarsa zuwa ga matukar jimrewa da hakuri.
12 感謝那使我們有資格,在光明中分享聖徒福分的天父,
Muna addu'a za ku yi godiyar farinciki ga Uban, wanda ya sa kuka samu rabo cikin gado na masu bangaskiya cikin haske.
13 因為是祂由黑暗的權勢下救出了我們,並將我們移植在祂愛子的國內,
Ya kwato mu daga mulkin duhu ya kuma maishe mu ga mulkin kaunataccen Dansa.
14 我們在祂內得到了救贖,獲得了罪赦。
Ta wurin Dan ne muka sami fansa, gafarar zunubai.
15 祂是不可見的天主的肖像,是一切受造物者的首生者,
Dan shine surar Allah mara ganuwa. Shine farkon dukan hallitta.
16 因為在天上和在地上的一切,可見的與不可見的,或是上座者,或是宰制者,或是率領者,或是掌權者,都是在祂內受造的:一切都是藉著祂,並且是為了祂而受造的。
Domin ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa, wadanda ke sama da wadanda ke duniya, masu ganuwa da marasa ganuwa. Ko kursiyai ko mulkoki ko sarautai ko ikoki, dukan abubuwa shi ya hallice su kuma dominsa.
17 祂在萬有之先就,有萬有都賴祂而存在;
Ya kasance kafin dukan abubuwa, a cikinsa ne kuma komai yake hade.
18 祂又是身體──教會的頭:祂是元始,是死者中的首生者,為使祂在萬有之上獨佔首位,
Kuma shine kan jikin, ikilisiya. Shine farko da kuma dan fari daga cikin matattu, don haka yana da wuri na fari a cikin dukan abubuwa.
19 因為天主樂意叫整個的圓滿居在祂內,
Domin Allah ya yi farinciki cewa dukan cikarsa ta kasance a cikinsa,
20 並藉著祂使萬有,無論是地上的,是天上的,都與自己重歸於好,因著祂十字架的血立定了和平。
kuma ya sulhunta kowanne abu zuwa gare shi ta wurin Dan. Allah ya kawo salama ta wurin jinin giciyensa. Allah ya sulhunta duka zuwa gare shi, ko abubuwan da ke duniya ko abubuwan da ke sama.
21 連你們從前也與天主隔絕,並因邪惡的行為在心意上與祂為敵;
Domin a da ku baki ne ga Allah, kuma makiyansa ne cikin zuciya da cikin mugun ayyuka.
22 可是現今天主卻以祂血肉的身體,藉著死亡使你們與自己和好了,把你們呈獻在祂跟前,成為聖潔,無瑕和無可指摘的,
Amma yanzu, ya sulhunta ku ta wurin mutuwarsa ta jiki. Ya yi haka domin ya mika ku tsarkakaku, marasa aibu da marasa abin zargi a gabansa,
23 只要你們在信德上站穩,堅定不移,不偏離你們由聽福音所得的希望,這福音已傳與天下一切受造物,我保祿就是這福音的僕役。
idan kuka ci gaba cikin bangaskiya, kafaffu da tsayayyu, marasa kaucewa daga begen ku na hakika na bishara da kuka ji. Wannan itace bishara da aka yi wa kowanne halitaccen taliki a karkashin sama. Wannan itace bishara wadda ni, Bulus, na zama bawa.
24 如今我在為你們受苦,反覺高興,因為這樣我可在我的肉身上,為基督的身體──教會,補充基督的苦難所欠缺的;
Yanzu ina murna da wahala ta domin ku. A jikina cika abin da ya rage cikin wahalar Almasihu domin jikinsa wadda itace ikilisiya.
25 我依照天主為你們所授與我的職責,作了這教會的僕役,好把天主的道理充分地宣揚出去,
Saboda wannan ikilisiya na zama bawa, bisa ga haki da Allah ya ba ni domin ku, domin cika sakon Allah.
26 這道理就是從世世代代以來所隱藏,而如今卻顯示給祂的聖徒的奧祕。 (aiōn g165)
Wannan shine asirin gaskiya da yake a boye shekara da shekaru da zamanai. Amma a yanzu an bayyana shi ga wadanda suka gaskanta da shi. (aiōn g165)
27 天主願意他們知道,這奧祕為外邦人是有如何豐盛的光榮,這奧祕就是基督在你們中作了你們覺得光榮的希望。
A gare su ne Allah ya so ya bayyana yalwar daukakar asirin gaskiyarsa a tsakanin al'ummai. Ya nuna Almasihu ne ke cikin ku, tabbacin daukaka mai zuwa.
28 我們所傳揚的,就是這位基督,因而我們以各種智慧,勸告一切人,教訓一切人,好把一切人,呈獻於天主前,成為在基督內的成全人;
Wannan shine wanda muke shella. Muna gargadar da kowanne mutum, muna kuma koyar da kowanne mutum tare da dukan hikima, don mu mika kowanne mutum cikakke cikin Almasihu.
29 我就是為這事而勞苦,按祂以大能在我身上所發動的力量,盡力奮鬥。
Domin wannan nake aiki da himma bisa ga karfinsa da yake aiki a cikina da iko.

< 歌羅西書 1 >