< 使徒行傳 18 >

1 後,保祿就離開雅典,來到了格林多。
Bayan haka sai Bulus ya tafi Antakiya daga nan, ya wuce Korinti.
2 在那裏遇見了一個猶太人,名叫阿桂拉,原藉本都,他同妻子普黎史拉最近從義大利來,因為喀勞狄曾命所有的猶太人都離開羅馬。保祿就投到他們那裏,
A can ya sadu da wani Bayahude mai sunan Akila, dan kasar Buntus ne; bai dade da zuwa garin ba, daga Italiya ya zo da matarsa mai suna Balkisu, saboda Kalaudiyas ya ba da umarni dukan Yahudawa su bar Roma; sai Bulus ya je wurinsu.
3 因為是同業,保祿便留在他們那裏工作;原來他們是以製造帳幕為業的。
Bulus ya zauna a gidansu don sana'arsu daya ce, wato, masu aikin Tanti ne.
4 每逢安息日,保祿就在會堂裏辯論,勸化猶太人和希臘人。
Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa.
5 及至息拉和弟茂德從馬其頓來到後,保祿就專心傳道,向猶太人證明耶穌就是默西亞。
Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne.
6 可是,因為他們反對,而且說褻瀆的話,保祿就拂拭衣服向他們說:「你們的血歸到你們頭上,與我無干,從今以後,我要到外邦人那裏去了。」
Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, “Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai.”
7 於是離開那裏,進了一個名叫弟鐸猶斯托的家裏,這人敬畏天主,他的家緊靠著會堂。
Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a.
8 會堂長克黎斯頗和他的全家都信了主,還有許多格林多人聽了道而相信,也領了洗。
Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma.
9 夜間,主藉異象對保祿說:「不要害怕,只管講,不要緘默,
Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, “Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru.
10 因為有我與你同在,必沒有人向你下手加害你,因為在這城裏有許多百姓是屬於我的。」
Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin.”
11 於是,他就在那裏住了一年零六個月,在他們中講授天主的聖道。
Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah.
12 當加里雍作阿哈雅總督時,猶太人同心合意地起來攻擊保祿,把他帶到法庭
Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a.
13 說:「這個人勸人違法敬拜天主。」
Suna cewa, “Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu.”
14 保祿剛要開口,加里雍就向猶太人說:「猶太人啊!如果有什麼犯法或邪惡的罪行,我自當容忍你們;
Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, “Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta.
15 但問題既是關於道理、名目和你們自己的法律的事,你們自己管罷,我不願作這些事的判官。」
Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku.”
16 就把他們逐出了法庭。
Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a.
17 於是眾希臘人拉住會堂長索斯特乃,在法庭前打了他;而加里雍全不理睬這些事。
Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba.
18 保祿又住了些日子,就與弟兄們辭別,乘船往敘利亞去;和他一起的,有普黎史拉和和阿桂拉,因為保祿許有誓願,在耕格勒剃了頭髮。
Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare.
19 到了厄弗所,保祿便把他們留在那裏,自己進了會堂,同猶太人辯論。
Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su.
20 眾人求他多住些時候,他沒有應允,
Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba.
21 卻辭別他們說:「若是天主願意,我還要回到你們這裏來。」遂從厄弗所開船走了。
Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, “In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana.” Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa.
22 在凱撒勒雅下船,就上耶路撒冷問候教會,然後下到安提約基雅。
Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya.
23 保祿住了一個時期,又出發,挨次經過迦拉達區和夫黎基雅,堅固眾位門徒。
Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai.
24 有一個在亞歷山大里亞出生的猶太人,名叫阿頗羅,是個有口才的人,長於聖經,他到了厄弗所。
A nan dai akwai wani Bayahude mai suna Afolos, dan asalin Iskandariya ne da haihuwa, ya zo Afisa. Shi masani ne a maganar Allah.
25 這人學過主的道理,講論耶穌的事,心神熱烈,教訓人也很詳實,卻只知若翰的洗禮。
Afolos dai ya sami horo daga maganar Ubangiji. Shi mai kokari ne a ruhu, yana wa'azi da koyarwa daidai game da Yesu. Amma ya san da Baftismar Yahaya ne kadai.
26 這人開始在會堂裏放膽講論。普黎史拉和阿桂拉聽了他的講論,就把他接來,給他更詳實地講解了天主的道理。
Afolos ya fara wa'azinsa da gabagadi a cikin majami'a. Da Balkisu da Akila suka ji shi sai suka yi abokantaka da shi, suka kara bayyana masa game da labarin hanyar Allah mafi daidai.
27 阿頗羅有意往阿哈雅去,弟兄們都鼓勵他,並且給門徒寫信,叫他們接待他;他到了那裏,依賴恩寵,給了信友們很多的貢獻,
Da ya so ya wuce zuwa cikin Akaya 'yan'uwa suka karfafa shi, sun rubuta wa almajiran da ke a Akaya, don su karbe shi da hannu biyu. Da ya iso wurinsu, ya kuwa karfafa 'yan'uwa da sun ba da gaskiya ta wurin alheri.
28 因為他經常有力地當眾駁倒猶太人,用聖經指明耶穌就是默西亞。
Afolos ya ba Yahudawa mamaki da irin ikon da yake da shi da gwanintarsa, yadda yake nunawa daga nassoshi cewa Yesu shine Almasihu.

< 使徒行傳 18 >