< 使徒行傳 15 >

1 從猶太下來的幾個人教訓弟兄們說:「若是你們不按梅瑟的慣例行割損,不能得救。」
Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”
2 保祿和巴爾納伯同他們起了不少的爭執和辯論;大家就指定保祿和巴爾納伯,與他們中的幾個人,上耶路撒冷去見宗徒和長老,討論這問題。
Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.
3 他們由教會送走之後,就路過腓尼基和撒瑪黎雅,沿途敘述外邦人歸化的事,使眾弟兄非常喜歡。
Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan’yan’uwa suka yi murna ƙwarai.
4 他們到了耶路撒冷,為教會、宗徒和長老所歡迎,就報告了天主偕同他們所行的一切大事。
Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.
5 卻有幾個信教的法利塞黨人起來說:「必須叫外邦人受割損,又應該命他們遵守梅瑟法律。」
Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”
6 宗徒和長老們就開會商討此事。
Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar.
7 辯論多時之後,伯多祿起來向他們說:「諸位仁人弟兄!你們深知,多時以前,天主就在你們中選定了,要藉我的口,為叫外邦人聽福音的道理而信從。
Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
8 洞察人心的天主,已為他們作了證,因為賜給了他們聖神,如同賜給了我們一樣;
Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
9 在我們和他們中間沒有作任何區別,因他以信德淨化了他們的心。
Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.
10 既然如此,現今你們為什麼試探天主,在門徒的頸項上,放上連我們的祖先和我們自己都不能負荷的軛呢﹖
To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?
11 但是,我們信我們得救,是藉著主耶穌的恩寵,正和他們一樣。」
A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
12 於是眾人都緘默不語,靜聽巴爾納伯和保祿述說天主藉著他們在外邦人中,行了怎樣大的徵兆與奇蹟。
Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu.
13 大家都不出聲之後,雅各伯接著說:「諸位仁人弟兄,請聽我說!
Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni.
14 西滿述說了天主當初怎樣關心外邦人,由他們中選拔一個百姓,屬於自己名下;
Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa.
15 先知的話也正與此相合,如經上記載:『
Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa,
16 以後我要回來,重建達味已傾倒的居所;已坍塌了的,要把它重建而豎立起來,
“‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi,
17 為的是其餘的人,即一切以我的名得名的民族,要尋求上主:
don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’
18 這是很久以前,公佈這事的主說的。』 (aiōn g165)
da aka sani tun zamanai. (aiōn g165)
19 因此,按我的意見,不要再加給由外邦歸依天主的人煩難,
“Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah.
20 只要函告他們戒避偶像的玷污和奸淫,戒食窒死之物和血。
A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.
21 因為自古以來,在各城內都有宣講梅瑟的人,每安息日在會堂中誦讀他的書。」
Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”
22 當時,宗徒和長老同全教會決定,從他們中選幾個人,派他們同保祿和巴爾納伯去安提約基雅。所派的,有號稱巴爾撒巴的猶達和息拉,是弟兄中的領導人物。
Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin’yan’uwa.
23 他們帶去的信如下:「宗徒和長老弟兄們,給在安提約基雅、敘利亞和基里基雅由外邦歸化的弟兄們請安。
Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa,’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.
24 我們聽說有幾個從我們這裏去的,而並非我們所派去的人,講話擾亂你們,混亂了你們的心。
Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce.
25 我們取得同意後,決定揀選幾個人,派他們同我們可愛的巴爾納伯和保祿,到你們那裏去。
Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus
26 此二人為了我們主耶穌基督的名,已付出了自己的性命。
mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.
27 我們派猶達和息拉去,他們要親口報告同樣的事。
Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta.
28 因為聖神和我們決定,不再加給你們什麼重擔,除了這幾項重要的事:
Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa.
29 即戒食祭邪神之物、血和窒死之物,並戒避奸淫;若你們戒絕了這一切,那就好了。祝你們安好!」
Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya.
30 他們去後,就下到安提約基雅,聚集了眾人,遞上公函。
Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.
31 人們讀了,對這勸慰的話都十分歡喜。
Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.
32 猶達和息拉,因為他們也是先知,就講了許多話,勸勉堅固弟兄們。
Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa’yan’uwa.
33 過了一些時候,弟兄們打發他們帶著請安的話,回到派他們的人那裏。
Bayan suka yi’yan kwanaki a can, sai’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.
34 【但是息拉決意留在那裏,只猶達一人回了耶路撒冷。】
35 保祿和巴爾納伯卻留在安提約基雅施教,同別的許多人宣講主的道理。
Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji.
36 過了些日子,保祿向巴爾納伯說:「我們要回去,視察我們曾講過主道的各城,看看弟兄怎麼樣了。」
Bayan’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.”
37 巴爾納伯願意也帶號稱馬爾谷的若望同去,
Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su,
38 但保祿認為不應帶他去,因為他從旁非里雅離開他們,沒有同他們一起去工作。
amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba.
39 二人於是起了爭執,以致彼此分離。巴爾納伯遂帶馬爾谷,乘船往塞浦路斯去了。
Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus,
40 保祿卻揀選了息拉,蒙弟兄們將他託於主的恩寵以後,
amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji.
41 也起身走了,他走遍了敘利亞和基里基雅,堅固各教會。
Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

< 使徒行傳 15 >