< 提摩太後書 1 >
1 奉天主的旨意,為傳佈在基督耶穌內所恩許的生命,作基督耶穌宗徒的保祿,
Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai da ke cikin Almasihu Yesu,
2 致書給可愛的兒子弟茂德。願恩寵、仁慈與平安,由天主父和我們的主基督耶穌賜與你!
zuwa ga Timoti, kaunataccen da: Alheri, jinkai, da salama daga Allah Uba da Almasihu Yesu Ubangijinmu.
3 當我在黑夜白日的祈禱中,不斷地懷念你時,我就感謝我繼續祖先,以純潔的良心所服事的天主。
Na gode wa Allah, wanda na ke bautawa tun daga kakannina, da lamiri mai tsabta, sa'adda na ke tuna wa da kai cikin addu'o'ina koyaushe (dare da rana).
4 我每想起你的眼淚,我便渴望見你,為叫我滿心喜樂;
Sa'adda na tuna da hawayenka, na yi marmarin ganinka, saboda in cika da farin ciki.
5 我記得你那毫無虛偽的信德,這信德首先存在你外祖母羅依和你母親歐尼刻的心中,我深信也存在你的心中。
An tunashshe ni game da sahihiyar bangaskiyarka, wadda ta samo asali daga kakarka Loyis da mahaifiyarka Afiniki. Na kuma tabbata ta na zaune a cikinka.
6 為了那原故,我提醒你把天主藉我的覆手所賦予你的恩賜,再熾燃起來,
Wannan shine dalilin da ni ke tunashshe ka cewa ka sake rura baiwar Allah da ke cikinka wadda ka samu sa'adda na dibiya maka hannuwana.
7 因為天主所賜給我們的,並非怯懦之神,而是大能、愛德和慎重之神。
Domin Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da kauna da kamun kai.
8 所以你不要以給我們的主作證為恥,也不要以我這為主被囚的人為恥,但要依賴天主的大能,為福音同我共同勞苦。
Saboda haka kada ka ji kunyar shaida ga me da Ubangijinmu, ko ni, Bulus, daurarrensa. Maimakon haka, ka zama a shirye ka sha wahala domin bishara bisa ga ikon Allah.
9 天主拯救了我們,以聖召召叫了我們,並不是按照我們的行為,而是按照衪的決意和恩寵:這恩寵是萬世以前,在基督耶穌內賜與我們的, (aiōnios )
Allah ne ya cecemu kuma ya kira mu da kira mai tsarki. Ya yi wannan, ba ta wurin ayyukanmu ba, amma ta wurin shirinsa da alherinsa. Ya ba mu wadannan abubuwan a cikin Almasihu Yesu kafin farkon zamanai. (aiōnios )
10 如今藉著我們的救主基督耶穌的出現,出現示了出來;衪毀滅了死亡,藉著福音彰顯了不朽的生命。
Amma yanzu an bayyana ceton Allah ta wurin bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu. Almasihu ne ya kawo karshen mutuwa ya kuma kawo rai marar karshe da ya bayyana ta wurin bishara.
Domin wannan, an zabe ni mai wa'azi, manzo da mallami zuwa ga al'ummai.
12 為了這原故,我現在受這些苦難,但我並不以此為恥,因為我知道我所信賴的是誰,也深信衪有能力保管我所受的寄托,直至那一日。
Domin wannan dalili na ke shan wahalar wadannan abubuwa. Amma ban ji kunya ba, domin na san shi, wanda na gaskanta. Na sakankance zai iya adana abinda na mika masa har zuwa ranan nan.
13 你要以信德及在基督耶穌內的愛德,把從我所聽的健全的道理,奉為模範;
Ka adana misalin amintattun sakwanni da ka ji daga gare ni, ta wurin bangaskiya da kauna da ke cikin Almasihu Yesu.
14 且依賴那住在我們內的聖神,保管你所受的美好寄托。
Abu mai kyau da Allah ya danka maka, ka tsare shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da ke zaune a cikinmu.
15 你知道那些在亞細亞的人都離棄了我,其中有菲革羅和赫摩革乃。
Ka dai sani, dukkan wadanda su ke zama a Asiya sun juya mani baya. A cikin kungiyar akwai Fijalas da Harmajanas.
16 願主賜仁慈於敖乃息佛羅的家庭,因為他屢次使我精神快慰,也不以我鎖鏈為恥,
Bari Ubangiji ya yi wa iyalin Onisifaras jinkai, domin ya na yawan yi mani hidima, kuma ba ya jin kunyar sarkata.
17 而且他一到了羅馬,急切地訪尋我,也找到了我。
Maimakon haka, sa'adda ya ke a Roma, ya neme ni da kokarin gaske, ya kuma same ni.
18 願主到那一日,賜他獲得主的仁慈! 他在厄弗所怎樣為我服了務,你們知道得更清楚。
Bari Ubangiji ya sa, ya sami jinkai daga gare shi a wannan rana. Dukkan hanyoyin da ya taimake ni a kasar Afisa, kun sani sarai.