< 列王紀下 18 >
1 以色列王厄拉的兒子曷舍亞三年,阿哈次的兒子希則克雅登基為猶大王。
A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki.
2 他登極時年二十五歲,在耶路撒冷作王凡二十九年;他的母親名阿彼雅,是則加黎雅的女兒。
Yana da shekara ashirin da biyar da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Abiya’yar Zakariya.
3 希則克雅行了上主視為正義的事,完全像他祖先達味所行的一樣;
Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda kakansa Dawuda ya yi.
4 他廢除了高丘,毀壞了石柱,砍倒了木偶,打碎了梅瑟所製造的銅蛇,因為直到那時,以色列子民仍向銅蛇焚香,稱為乃胡市堂。
Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)
5 他信賴上主以色列的天主;在他前後的猶大列王中,沒有一個可與他相比的。
Hezekiya ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Ba a yi wani kamar sa ba cikin dukan sarakunan Yahuda; ko kafin shi, ko kuma bayansa.
6 他依靠上主,緊隨不離,謹守上主頒給梅瑟的誡命。
Ya manne wa Ubangiji, bai fasa binsa ba; ya yi biyayya da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa.
7 因此,上主與他同在,他無論作什麼,必都順利,且擺脫了亞述王的羈絆,不再作他的藩屬;
Ubangiji kuma ya kasance tare da shi, ya yi nasara a duk abin da ya sa hannu. Ya yi tawaye ga sarkin Assuriya, ya ƙi yă bauta masa.
8 又擊敗了培肋舍特人,直追到迦薩,佔領了他們的土地,攻取了守望台和堅城。
Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye.
9 希則克雅王四年,即以色列王厄拉的兒子曷舍亞七年,亞述王沙耳瑪乃色來進攻撒瑪黎雅,圍困了這城;
A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.
10 三年年底攻下,即希則克雅王六年,以色列王曷舍亞九年,撒瑪黎雅失陷。
A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila.
11 亞述王遂將以色列人擄往亞述,徙置在哈拉黑和靠近哥倉河的哈波爾,以及瑪待各城內。
Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes.
12 這是因為他們沒有聽從上主,他們天主的聲音,違反了他的盟約:凡上主的僕人梅瑟所吩咐的,他們一概沒有聽從,也沒有遵行。
Wannan ya faru ne domin ba su yi biyayya ga Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsu; da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su saurari umarnin ba, balle su kiyaye su.
13 希則克雅王十四年,亞述王散乃黑黎布前來進攻猶大的一切堅城,都佔領了。
A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su.
14 猶大王希則克雅於是派遣使者,到拉基士去見亞述王說:「我錯了,請你退兵;凡你向我提出的條件,我都接受。」於是亞述王限令猶大王希則克雅繳納三百「塔冷通」銀子,三十「塔冷通」金子。
Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda.
15 希則克雅只得把上主殿內,和王宮府庫所有的銀子都交出來。
Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.
16 同時,猶大王希則克雅將上主殿宇門上的金子和他自己包鑲在門柱上的金子都剝下來,交給了亞述王。
A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.
17 亞述王從拉基士打發元帥、衛隊長和大將軍率領大軍到耶路撒冷去見希則克雅。他們就上到耶路撒冷,一來到,就站在上池的水溝旁,漂布田間的大路上,
Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.
18 求見君王。希耳克雅的兒子厄里雅金家宰,舍布納書記和阿撒夫的兒子約阿黑史官,出來迎接他們。
Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.
19 大將軍對他們說:「你們去告訴希則克雅說:大王,亞述王這樣說:你所依靠的,算得什麼依靠﹖
Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?
20 你想空口說話,就是戰略和戰鬥的力量嗎﹖如今你靠誰來背叛我﹖
Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye?
21 我現在你看,你依靠的埃及是一根破裂的蘆杖;誰依靠這杖,它就刺傷誰的手,且把手刺透;埃及王法郎對所有依靠他的人,就是這樣。
Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.
22 假使你們對我說:我們依靠雅威我們的天主,希則克雅豈不是曾推翻他的高丘和祭壇,且對猶大和耶路撒冷說:你們只應在耶路撒冷的這祭壇前朝拜﹖
Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?
23 如今你可與我的主上亞述王打賭:我給你兩千匹馬,你是否能給這些馬配上騎兵﹖
“‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu!
24 若不能,你怎敢拒絕我主上最小僕人中的一個軍長,而去依靠埃及的戰車和騎兵﹖
Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai?
25 現在,我上來攻打毀滅這地,難道不是雅威的意思嗎﹖雅威曾對我說:你上去攻打這地,加以毀滅! 」
Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’”
26 希耳克雅的兒子厄里雅金、舍布納和約阿黑對大將軍說:「請你對你的僕人說阿剌美話,因為我們都懂;你不要對我們說猶太話,因為城牆上的百姓能聽到。」
Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”
27 大將軍回答說:「難道我的主上打發我來,只對你的主上和你講這些話,而不是對那些坐在城牆上,和你們一樣該吃自己的糞,喝自己的尿的人,講這些話嗎﹖」
Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”
28 大將軍於是站起來,仍用猶太話大聲喊說:「你們聽大王亞述王的話罷!
Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya!
29 大王這樣說:你們別上希則克雅的當,他決不能拯救你們脫離我的手;
Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba.
30 也不要讓希則克雅使你們依靠雅威說:雅威必會拯救我們,這城決不會落在亞述王手中。
Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’
31 千萬別聽信希則克雅! 原來亞述王曾這樣說:你們要與我和好,出來歸順我,各人就可以吃自己的葡萄和無花果,各人也可以喝自己井裡的水,
“Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci’ya’yan inabinsa da’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa,
32 直到我來領你們到一個與你們本國一樣的地方去,一個有五穀和新酒的地方,一個有食糧和葡萄樹的地方,一個產橄欖油和蜂蜜的地方,叫你們生活下去,而不至於死亡。千萬別聽信希則克雅,因為他欺騙你們說:雅威必拯救我們。
har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’
33 萬國的神中,有那一個由亞述王手中,拯救了自己的國土﹖
Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?
34 哈瑪特和阿帕得的神在那裡﹖色法瓦因、赫納和依瓦的神在那裡﹖撒瑪黎雅地的神在那裡﹖難道他們從我手中拯救了撒瑪黎雅﹖
Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna?
35 在這地域中的神,有那一個由我手中救出了自己的國土﹖難道雅威就能由我手中拯救耶路撒冷嗎﹖」
Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”
36 人都不作聲,一句話都沒有回答他,因為君王有命,不要回答他。
Amma mutane suka yi shiru ba su amsa masa ba, domin sarki ya umarta cewa, “Kada ku amsa masa.”
37 當下希耳克雅的兒子厄里雅金家宰、舍布納書記和阿撒夫的兒子約阿黑史官,撕裂了自己的衣服,來見希則克雅,將那將軍的話全部告訴了他。
Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.