< 列王紀下 11 >

1 阿哈齊雅的母親阿塔里雅見自己的兒子已死,便起來消滅王室所有的後裔。
Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta.
2 但約蘭王的女兒,阿哈齊雅的姊姊約舍巴,將阿哈齊雅的兒子約阿士,從被殺的王太子中偷了出來,把他和他的奶媽安置在寢室內,藏了起來,沒有讓阿塔里雅看見:這樣纔沒有被殺。
Amma Yehosheba,’yar Sarki Yoram,’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.
3 約阿士和他的奶媽,在上主的殿內隱藏了六年,當時由阿塔里雅主持國政。
Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
4 第七年,約雅達派人將眾百夫長,加黎人隊長和衛隊長召來,領進上主的殿,與他們立約,在上主殿內起誓,然後引君王的兒子出來與他們相見,
A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.
5 同時吩咐他們說:「你們應這樣行事,在安息日進宮值班的三分之一,要照例守衛王宮,
Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki,
6 另三分之一守衛穌爾門,另三分之一把守守衛者的後門;仍照舊值班守衛聖殿。
kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan,
7 在安息日從上主殿內下班的兩隊,仍應在上主的殿內戒備,
ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.
8 各人要手裡拿著武器環繞君王。擅入防線的,即將他殺死;君王出入時,你們要緊隨不離。」
Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”
9 百夫長就按照司祭約雅達所吩咐的一切去行,各自帶領在安息日值班,和在安息日下班的士兵,來見司祭約雅達。
Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.
10 司祭便將上主殿內屬達味王的刀槍和盾牌,交給了眾百夫長。
Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.
11 衛兵每人所持武器,自殿右至殿左,面對祭壇和聖殿,環立在君王四周;
Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.
12 然後引出太子來,給他加冕,將約書交給他,立他為王,給他傅油,在場民眾都鼓掌歡呼:「君王萬歲! 」
Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”
13 阿塔里雅聽見民眾叫喊聲,就進上主的殿,到民眾前。
Sa’ad da Ataliya ta ji surutun matsara da na mutane, sai ta tafi wurin mutanen a haikalin Ubangiji.
14 她一看,見君王照儀式站在高台上,官長和吹號角的,都站在君王兩旁,所有當地人民歡樂吹號;阿塔里雅就撕裂了自己的衣服,喊叫說:「反了,反了! 」
Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”
15 約雅達司祭即吩咐帶領軍隊的眾百夫長說:「將她從行列中趕出去,凡跟隨她的,都用刀殺死。」原來司祭曾吩咐說:不可在上主的殿內殺她。
Yehohiyada ya umarci komandodin sojoji waɗanda suke lura da mayaƙa, ya ce, “Ku fitar da ita daga cikinku, ku kuma kashe duk wanda ya bi ta.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada a kashe ta a cikin haikalin Ubangiji.”
16 於是眾人捉住她;當她由馬門進入王宮時,就地將她殺了。
Saboda haka suka kama ta yayinda ta kai inda dawakai sukan shiga filin fada, a can kuwa aka kashe ta.
17 此後,約雅達使君王和人民與上主立約,作上主的人民;又使君王與人民立約。
Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane.
18 然後,所有當地人民都到巴耳廟去,將廟拆毀,將祭壇推翻,將神像完全打碎,在祭台前斬了巴耳的司祭瑪堂。司祭約雅達又調派士兵把守上主的殿,
Sai dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba’al suka rushe shi. Suka farfasa bagadai da kuma gumaka, suka kuma kashe Mattan wanda yake firist na Ba’al a gaban bagade. Sa’an nan Yehohiyada firist ya sa matsara a haikalin Ubangiji.
19 以後,率領眾百夫長、加黎人、衛兵和所有當地人民,請君王從上主的殿下來,經衛兵門進入王宮,請他坐在王座上。
Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta,
20 全國人民都歡樂喜慶,京城也很平靜。至於阿塔里雅,已在王宮用刀殺死。
dukan mutanen ƙasar suka yi murna. Birnin ya sami salama don an kashe Ataliya da takobi a fada.
21 約阿士即位時,纔七歲;
Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya fara mulki.

< 列王紀下 11 >