< 約翰一書 5 >

1 凡信耶穌為默西亞的,是由天主所生的;凡愛生他之父的,也必愛那由他所生的。
Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma.
2 幾時我們愛天主,又遵行他的誡命,由此知道我們真愛天主的子女。
Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa.
3 原來愛天主,就是遵行他的誡命,而他的誡命並不沉重,
Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne;
4 因為凡是由天主所生的,必得勝世界;得勝世界的勝利武器,就是我們的信德。
domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.
5 誰是得勝世界的呢?不是那信耶穌為天主子的人嗎?
Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
6 這位就是經過水及血而來的耶穌基督,他不但以水,而且也是以水及血而來的;並且有聖神作證,因為聖神是真理。
Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya.
7 原來作證的有三個:
Akwai shaidu uku, wato,
8 就是聖神,水及血,而這三個是一致的。
Ruhu, da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.
9 人的證據,我們既然接受,但天主的證據更大,因為天主的證據就是他為自己的子作證。
Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa.
10 那信天主子的,在自己內就懷有這證據;那不信天主的,就是以天主為撒謊者,因為他不信天主為自己的子所作的證。
Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba.
11 這證據就是天主將永遠的生命賜給了我們,而這生命是在自己的子內。 (aiōnios g166)
Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. (aiōnios g166)
12 那有子的,就有生命;那沒有天主子的,就沒有生命。
Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai.
13 我給你們這些信天主子名字的人,寫了這些事,是為叫你們知道:你們已獲有永遠的生命。 (aiōnios g166)
Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. (aiōnios g166)
14 我們對天主所懷的依恃之心就是:如果我們按他的旨意求什麼,他必俯聽我們。
Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu.
15 我們既然知道:我們不拘向他祈求什麼,他會俯聽我們,我們也知道向他所祈求的,必要得到。
In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.
16 誰若看見自己的弟兄犯了不至於死的罪,就應當祈求,天主必賞賜他生命:這是為那些犯不至於死的罪人而說的;然而有的罪卻是至於死的罪,為這樣的罪,我不說要人祈求。
Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba.
17 任何的不義都是罪過,但也有不至於死的罪過。
Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa.
18 我們知道:凡由天主生的,就不犯罪過;而且由天主生的那一位必保全他,那惡者不能侵犯他。
Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.
19 我們知道我們屬於天主,而全世界卻屈服於惡者。
Mun san cewa mu’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.
20 我們也知道天主子來了,賜給了我們理智,叫我們認識那真實者;我們確實是在那真實者內,即在他的子耶穌基督內,他即是真實的天主和永遠的生命。 (aiōnios g166)
Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada. (aiōnios g166)
21 孩子們,你們要謹慎,遠避偶像!
’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka.

< 約翰一書 5 >