< 哥林多前書 2 >
1 弟兄們,就是我從前到你們那裡時,也沒有用高超的言論或智慧,給你們宣講天主的奧義,
Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah [ a yayinda na bada shaida game da Allah].
2 因為我曾決定,在你們中不知道別的,只知道耶穌基督,這被釘在十字架上的耶穌基督;
Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye.
3 而且當我們到你們那裡的時候,又軟弱,又恐懼,又戰懼不安;
Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa.
4 並且我的言論和我的宣講,並不在於智慧動聽的言辭,而是在於聖神和祂德能的表現,
Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko,
5 為使你們的信德不是憑人的智慧,而是憑天主的德能。
saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah.
6 我們在成全的人中,也講智慧,不過不是今世的智慧,也不是今世將要消滅的權勢者的智慧; (aiōn )
Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa. (aiōn )
7 我們所講的,乃是那隱藏的,天主奧秘的智慧,這智慧是天主在萬世之前,為使我們獲得光榮所預定的; (aiōn )
Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu. (aiōn )
8 今世有權勢的人中沒有一個認識她,因為如果他們認識了,決不至於將光榮的主釘在十字架上。 (aiōn )
Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba. (aiōn )
9 經上這樣記載說:『天主為愛祂的人所準備的,是眼所未見,耳所未聞,心所未想到的。』
Amma kamar yadda yake a rubuce, “Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa.
10 可是又主藉著聖神將這一切啟示給我們了,因為聖神洞察一切,就連天主的深奧事理也洞悉。
Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah.
11 除了人內裏的心神外,有誰能知道那人的事呢?同樣,除了天主聖神外,誰也不能明瞭天主的事。
Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah.
12 我們所領受的,不是這世界的精神,而是出於天主的聖神,為使我們能明瞭天主所賜與我們的一切。
Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah.
13 為此,我們宣講,並不用人的智慧所教的言詞,而是用聖神所教的言詞,給屬神的人講論屬神的事。
Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya.
14 然而屬血氣的人,不能領受天主聖神的事,因為為他是愚妄;他也不能領悟,因為這些事只有藉聖神才可審斷。
Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su.
15 惟有屬神的人能審斷一切,但他卻不為任何人所審斷。
Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari'anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari'ar sauran mutane.
16 經上說:『誰知道上主的心意,去指教祂呢?』可是我們有基督的心意。
“Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?” Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.