< 歷代志上 7 >

1 [依撒加爾的後代]依撒加爾的兒子:托拉、普瓦、雅叔布和史默龍四人。
’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yashub da Shimron, su huɗu ne duka.
2 托拉的子孫:烏齊、勒法雅、耶黎耳、雅赫買、依貝散和舍慕耳,都是托拉家族的族長,英勇的戰士;再達味時代,依他們的家系,人數有二萬二千六百。
’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600.
3 烏齊的兒子依次辣希雅;依次辣希雅的兒子:米加耳、敖巴狄雅、約厄耳和依史雅......五人,┬歐是族長。
Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya.’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne.
4 按家系和家族歸屬於他們的,尚有三萬六千出征的戰士;因為他們有很多婦女和兒童。
Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da’ya’ya da yawa.
5 連他們的兄弟,即全依撒加爾支派中的英勇的戰士,登記的人數,共計八萬八千。[本雅明的後代]
Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka.
6 本雅明的兒子:貝拉貝革爾、耶狄厄耳三人。
’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne, Bela, Beker da Yediyayel.
7 貝拉的兒子:厄茲朋、烏齊、烏齊耳、耶黎摩特和依黎五人,都是家族的族長;英勇的戰士,按家族統計,共計二萬二千三十四人。
’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034.
8 貝革爾的兒子:則米辣、約阿士、厄里厄則爾、厄里約乃、敖默黎、耶肋摩特、阿彼雅、阿納托特和阿拉默特:以上是貝革爾的兒子,
’Ya’yan Beker maza su ne, Zemira, Yowash, Eliyezer, Eliyohenai, Omri, Yeremot, Abiya, Anatot da Alemet. Dukan waɗannan’ya’yan Beker maza ne.
9 是家族的族長;英勇的戰士,按家族統計共計二萬二百人。
Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200.
10 耶狄厄耳的兒子彼耳漢;彼耳漢的兒子:耶烏士、本雅明、厄胡得、革納阿納、則堂塔爾史士和希沙哈爾:
Ɗan Yediyayel shi ne, Bilhan.’Ya’yan Bilhan maza su ne, Yewush, Benyamin, Ehud, Kena’ana, Zetan, Tarshish da Ahishahar.
11 以上是耶狄厄耳的子孫,家族的族長;英勇的戰士能上陣作戰的,有一萬七千二百人。
Dukan waɗannan’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200.
12 依爾的兒子叔平和胡平;阿赫爾的兒子胡生。納斐塔里支派
Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne.
13 納斐塔里的兒子:雅赫則耳、古尼、耶則爾、沙隆:是彼耳哈的子孫。[默納協支派]
’Ya’yan Naftali maza su ne, Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne.
14 默納協的兒子:馬基爾,是他的一個阿蘭妾給他生的;瑪基爾是基肋阿得的父親。
Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad.
15 瑪基爾娶了妻,妻名叫瑪阿加,她的姊妹名叫責羅斐哈得,她只有女兒。
Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa.’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da’ya’yan mata ne kawai.
16 瑪基爾的妻子瑪阿加生了一個兒子,給他起名叫培勒士;他的兄弟名叫舍勒士。舍勒士的兒子:烏藍和勒耿。
Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh,’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.
17 烏藍的兒子貝丹:以上是默納協的子孫,瑪基爾的兒子基肋阿得的子孫。
Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.
18 他的姊妹摩肋革特生依市曷得、阿彼厄則爾和瑪赫拉。
’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala.
19 舍米達的兒子:阿希楊、舍根、里刻希和阿尼罕。[厄弗辣因支派]
’Ya’yan Shemida maza su ne, Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam.
20 厄弗辣因的兒子:叔特拉;叔特拉的兒子貝勒得,貝勒得的兒子塔哈特,塔哈特的兒子厄拉達,厄拉達的兒子塔哈特,
Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat
21 塔哈特的兒子匝巴得。厄弗辣因的兒子叔特拉和厄則爾以及厄拉得,為加特的土人所殺,因為他們下去劫掠土人的牲畜。
Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu.
22 他們的父親厄弗辣因哀悼他們多日,他的兄弟們也來慰弔。
Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.
23 以後,他又走近了自己的妻子,她懷孕生了一個兒子,給他起名叫貝黎雅說:「我家遭過患難。」
Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.
24 他的女兒舍厄辣建立了上下貝特曷龍和烏曾舍厄辣。
’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce,
25 貝黎雅的兒子勒法黑,勒法黑的兒子勒舍夫,勒舍夫的兒子特拉黑,特拉黑的兒子塔罕,
Refa, Reshef, Tela, Tahan,
26 塔罕的兒子拉丹,拉丹的兒子阿米胡得,阿米胡得的兒子厄里沙瑪,
Ladan, Ammihud, Elishama,
27 厄里沙瑪的兒子農,農的兒子若蘇厄。
Nun da kuma Yoshuwa.
28 他們佔據和居留的地方:貝特耳和所屬村鎮,往東有納阿郎,往西有革則爾和所屬村鎮,舍根和所屬村鎮,直到阿雅和所屬村鎮。
Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.
29 在默納協子孫手中的,有貝特商和所屬村鎮,塔納客和所屬村鎮,默基多和所屬村鎮,多爾和所屬村鎮:以色列的兒子若瑟的子孫住在以上各地。[阿協爾支派]
A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.
30 阿協爾的兒子:依默納、依市瓦、依市偉和貝黎雅,和他們的姊妹色辣黑。
’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishwi da Beriya.’Yar’uwarsa ita ce Sera.
31 貝黎雅的兒子:赫貝爾和瑪耳基耳,後者是彼爾匝依特的父親。
’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit.
32 赫貝爾生雅費肋特、芍默爾、曷堂和他們的姊妹叔亞。
Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma’yar’uwarsu Shuwa.
33 雅費肋特的兒子:帕撒客、彼默哈耳和阿市瓦特:以上是雅費肋特的兒子。
’Ya’yan Yaflet maza su ne, Fasak, Bimhal da Ashwat. Waɗannan su ne’ya’yan Yaflet maza.
34 他兄弟芍默爾的兒子:洛赫加、胡巴和阿蘭。
’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram.
35 他兄弟曷堂的兒子:祚法黑、依默納、舍肋士和阿瑪耳。
’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne, Zofa, Imna, Shelesh da Amal.
36 祚法黑的兒子:穌亞、哈爾乃費爾、叔阿耳、黎依默辣、
’Ya’yan Zofa maza su ne, Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra,
37 貝責爾、曷得、沙瑪、史耳沙、耶特爾和貝厄辣。
Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera.
38 耶特爾的兒子:耶孚乃、丕斯帕和阿辣。
’Ya’yan Yeter maza su ne, Yefunne, Fisfa da Ara.
39 烏拉的兒子:阿辣黑、哈巴耳和黎茲雅:
’Ya’yan Ulla maza su ne, Ara, Hanniyel da Riziya.
40 以上全是阿協爾的子孫,家族出名的族長,英勇的戰士,傑出的將領;能上陣打仗的登記人數,共計二萬六千。
Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne.

< 歷代志上 7 >