< 启示录 22 +

1 天使展示了生命水的河流,清澈透明,从上帝和羔羊的宝座流出来,
Sai mala'ika ya nuna mani kogin ruwan rai, ruwa mai tsabta. Yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Dan-Rago
2 就在城市主街的中央。河的两边是生命树,每月结果,共结十二次,树叶可以医治列国。
ta tsakiyar titin birnin. A kowanne gefen kogin akwai itacen rai, mai ba da 'ya'ya iri goma sha biyu, kowanne wata. Ganyayen itacen kuma domin warkar da al'ummai ne.
3 不再有任何咒诅。城里有上帝和羊羔的宝座,他的仆人都膜拜他。
Babu sauran la'ana nan gaba. Kursiyin Allah da na Dan Rago za su kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa bauta.
4 他们会看到他的脸。他的名字会写在他们的额头。
Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu.
5 不再有黑夜了,他们不再需要灯之光或太阳之光了,因为主上帝要光照他们,他们要作王,直到永远。 (aiōn g165)
Babu sauran dare; ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba gama Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su yi mulki har abada abadin. (aiōn g165)
6 天使对我说:“这些话可信且真实。那将其灵给了众先知的主上帝,派来他的天使,把快发生的事,指示他的仆人。”
Mala'ika ya ce mani, “Wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya. Ubangiji, Allah na ruhohin annabawa, ya aiki mala'ikansa ya nuna wa bayinsa abin da lallai zai faru ba da dadewa ba”.
7 “我马上到来!遵守这书上预言之人都会获得祝福!”
“Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba! Mai albarka ne wanda ya yi biyayya da kalmomin littafin nan.”
8 我是约翰,听到并看到这一切。当我听到和看到他们时,就俯伏在天使面前膜拜他,因为他向我展示了这一切。
Ni, Yahaya, nine na ji na kuma ga wadannan abubuwa. Sa'adda na ji na gan su, sai na fadi gaban kafaffun mala'ikan da ya nuna mani wadannan abubuwa domin in yi masa sujada.
9 他对我说:“千万别这样!我和你、以及你的兄弟和众先知、以及那些遵守这书上文字的人,都是仆人。你应当膜拜上帝。”
Ya ce mani, “Kada ka yi haka! Ni abokin bauta ne tare da kai, tare da 'yan'uwanka annabawa, da wadanda ke biyayya da kalmomin littafin nan. Yi sujada ga Allah!”
10 他又对我说:“不要封住这书上的预言,因为时间将至。
Ya ce mani, “Kada ka rufe kalmomin anabcin littafin nan, gama lokaci ya kusa.
11 那些不做正确事情之人,让他们保持那样。那些不纯洁的人,让他们保持那样。那些做正确事情之人,让他们保持那样。那些圣洁的人,让他们保持那样。”
Wanda yake mara adalci, bari ya cigaba da yin rashin adalci. Wanda yake mai kazanta bari ya cigaba da kazantar da kansa. Wanda yake mai adalci bari ya cigaba da yin adalci. Wanda yake mai-tsarki, bari yaci gaba da tsarki.”
12 “我马上到来!根据每个人的行为,将我的赏赐带给他们。
“Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba. Sakamakona na tare da ni, zan saka wa kowa gwargwadon aikin da ya yi.
13 我是阿尔法和欧米茄,我是最初也是最后,是开始也是结束。
Nine Alpha da Omega, farko da karshe, mafarin abu da karshensa.
14 那些洗净自己长袍之人获得了祝福!他们可以有权到生命树那里,也可以从门走进城里。
Masu albarka ne wadanda suka wanke rigunansu domin su sami izini su ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta kofofinsa.
15 城外的就是狗,行巫术的,淫乱的,杀人的,拜神像的,以及一切爱编造谎言的人。
A waje akwai karnuka, masu sihiri, masu bautar gumaka, fasikai, masu kisan kai, da duk wanda yake kaunar aikata rashin gaskiya.
16 我耶稣,派我的天使给你们这个见证,与众教会分享。我也是大卫的根和后裔,我是明亮的晨星。”
Ni, Yesu na aiko mala'ikana ya shaida maku wadannan abubuwa saboda ikilisiyoyi. Nine tushe da zuriyar Dauda, tauraron asubahi mai-haske.”
17 圣灵和新娘说:“来吧!”听见的人也要说:“来吧!”口渴的人,来吧!愿意的人, 都可免费接受这生命的水!
Ruhu da Amarya suka ce, “Zo!” Bari wanda ya ji ya ce, “Zo!” Kowanne mai jin kishi, da kowanne mai bukatar ta, bari ya sami ruwan rai kyauta.
18 我郑重地向所有听到这本预言书的人宣布,如果有在其中添加了什么,上帝就会把这本书中描述的灾难,添加在他们身上。
Ina shaida wa duk mai jin kalmomin anabcin wannan littafi: Idan wani ya kara a kansu, Allah zai kara masa annoban da ke rubuce a cikin littafin.
19 如果有人删减这书的预言,上帝必从这书中的生命树和圣城中,删去他那一部分。
Idan wani ya rage daga kalmomin wannan littafin anabci, Allah zai rage rabonsa daga cikin itacen rai daga cikin birni mai-tsarki, wadanda aka rubuta cikin wannan littafi.
20 确认这些事的那个人说:“是的,我马上到来!”阿门!来吧,主耶稣。
Shi wanda ya shaida wadannan abubuwa ya ce, “I! Ina zuwa ba da dadewa ba.” Amin! Zo, Ubangiji Yesu!
21 愿主耶稣的恩典与所有信徒同在!阿门。
Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da kowanne dayanku. Amin.

< 启示录 22 +