< 希伯来书 1 >
1 很久以前,上帝曾多次通过不同的方式借由先知向我们的祖先说话;
A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,
2 在这最后的岁月中,上帝又通过他的儿子向我们说话。上帝指认他继承万物,借由他创造宇宙。 (aiōn )
amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. (aiōn )
3 他是上帝的荣耀之光,是上帝性格的显化表现,用其强大的号令支撑万物;当他完成清洁罪恶之事,就会坐在天堂至尊者的右边。
Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.
Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.
5 照样,基督也没有因成为大祭司而为荣。是哪——上帝曾对他说“你是我的儿子。今天我已成为你的父亲。”
Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”?
6 上帝派其长子来到这世上,又说:“让上帝所有的天使都膜拜他。”
Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce, “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”
7 关于天使,他说:“上帝以他的天使为风,以他的仆役为火焰。”
Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce, “Ya mai da mala’ikunsa iska, bayinsa kuma harsunan wuta.”
8 但是说到他的儿子,他说:“上帝啊!你的宝座必将永恒存在,你王国的权杖是公平的权杖。 (aiōn )
Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka. (aiōn )
9 你喜爱正义良善,憎恨不法。所以上帝,也就是你的上帝,会为你涂抹欢喜的油膏,以此让你高于其他人。”
Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”
10 “主啊!你最初铺设了大地的根基,天也是你双手的作品。
Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.
11 它们都会终结,你却会长存;它们会像衣服一样逐渐破旧,
Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga.
12 你却会把它们像外套一样卷起来。天地就像衣服一样会被更换;只有你永不改变,你的生命也没有穷尽。”
Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”
13 上帝可曾向哪个天使说:“你坐在我的右边,等我将你的仇敌放在你的脚下”?
Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”?
14 天使呢?天使都是仆从,被派出去为那些将要获得救赎的人效劳。
Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?