< 希伯来书 10 >

1 律法只是即将到来之美好的影子,并非实物本身, 所以永远无法通过年复一年的反复献祭,让那些敬拜上帝之人实现正直良善。
Domin shari'a hoto ce na kyawawan abubuwan da ke zuwa, ba ainihin siffar wadannan abubuwa ba. Wadanda ke gusowa kusa da Allah ba za su taba ingantuwa ta wurin hadayu da firistoci ke mikawa shekara da shekaru ba.
2 如果敬拜的人一次得洁净,良心就不再觉得有罪,那么,献祭的事不是早就停止了吗?
In ba haka ba, ba sai a dena mika hadayun ba? Bisa ga wannan al'amari, inda sun tsarkaka sau daya tak da masu sujada ba su san menene zunubi ba.
3 可事实上,那些祭品却使人每年都想起罪来,
Amma wadannan hadayun sun zama matuni ne na zunubi shekara biye da shekara.
4 因为公牛和山羊的血不能清除罪。
Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awakai su kawar da zunubai.
5 所以,基督到世上来的时候,会说:“祭品和礼物不是你所要的,你为我准备好身体。
Yayin da Almasihu ya zo duniya, ya ce, “Ba hadayu da sadakoki kake marmari ba. Maimakon haka, ka shirya mini jiki domin hadaya.
6 燔祭和赎罪祭不会让你喜悦;
Baka murna domin sadakoki da hadayu na konawa domin zunubi.
7 那时我说:‘上帝!看啊,我来做你让我做的事情,就像经书上记载的那些关于我的事。’”
Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.'''
8 之前说道:“祭品和礼物,燔祭和赎罪祭,都不是你想要的,不会让你喜悦。”(尽管它们都是按照律法要求献祭的)。
Da fari Yace ''ba hadayu, ko sadakoki, ko kuma hadaya ta konawa domin zunubi kake bukata ba. Ba ka kuwa jin dadinsu.'' Wadannan sune hadayun da ake bayarwa bisa ga shari'a.
9 然后他又说:“看哪!我来了,是要做你想做的事情。”他废除了第一个约定,建立第二个。
Sa'annan sai ya ce ''gani na zo domin in aikata nufinka.” Ya kawar da hidimar farko domin ya kafa hidima ta biyu.
10 我们通过这约定,借着耶稣基督一次献上他的身体,就已获得神圣。
A hidima ta biyu, an kebe mu ga Allah ta wurin nufinsa ta wurin hadayar jikin Yesu Almasihu bugu daya ba kari.
11 所有祭司天天事奉,反复献上同样的祭品,那些祭品永远不能清除罪。
Haka, kowanne firist ya ke tsayawa kulliyomi domin ya yi hidima ga Allah. A kullum yana mika hadayu, iri daya, koda shike ba za su taba kawar da zunubai ba.
12 唯有这个祭司,进行一次永远有效的赎罪献祭,然后就在上帝的右边坐下来。
A ta wata hanya kuma, Almasihu ya mika hadaya sau daya tak domin zunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah.
13 现在,他只需等待他的敌人被征服,让他们成为他的脚凳。
Yana jiran har a maida makiyansa matashin sawayensa.
14 因为他的一次献祭,就让那些圣洁之人永远成为正直良善。
Domin ta wurin hadaya guda dayan nan ya kammala har abada ga wadanda suka sadaukar da kansu ga Allah.
15 圣灵也告诉我们,他这样说:
Kuma Ruhu mai Tsarki ya shaida mana. Abu na farko yace,
16 “主说:‘今后,我与他们所立的约是这样的:要把我的律法放在他们的心里面,写在他们的心上。’”他又说:
“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su a bayan kwanakin nan,' inji Ubangiji Zan sa dokokina a cikin zukatansu, kuma zan rubuta su a lamirinsu.
17 “我不再记着他们的恶和不法行为。”
Ba zan sake tunawa da zunubansu da kurakuransu ba.''
18 这一切被赦免后,就不需要为罪献祭了。
Yanzu fa duk in da aka sami gafara domin wadannan abubuwa, babu wata hadaya domin zunubi.
19 所以,兄弟姐妹们,凭着耶稣的血,我们可以自信地进入至圣所。
Saboda haka, yan'uwa, ba mu da shakkar shigowa wurin nan mafi tsarki ta wurin jinin Yesu.
20 他通过其生死给我们开辟一条全新的、永生的道路,穿越帐幔来到上帝面前。
Wannan ita ce sabuwar rayayyar hanya da ya bude mana ta wurin labulen, wato ta wurin jikinsa.
21 我们有一位伟大的祭司管理上帝的家,
Saboda muna da babban firist a gidan Allah.
22 我们良心的邪恶既然被洒净,身体也用清水洗净了,那么,我们就应该怀着真诚的心和完备的信,走近上帝;
Bari mu matso kusa da sahihiyar zuciya, da kuma cikakken gabagadi cikin bangaskiya, da zuciyarmu wadda aka tsarkake daga mummunan tunani, da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta.
23 因此,让我们紧紧抓住对别人讲述的希望,不要犹豫,因为上帝的承诺值得信赖。
Bari mu rike da karfi shaidar bangaskiyar begenmu, ba tare da raurawa ba, domin Allahn, da ya yi alkawari, mai aminci ne.
24 让我们想想如何激励彼此,去爱,去做善事。
Bari mu kuma yi lura yadda za mu iza juna ga kauna da ayyuka masu dacewa.
25 我们不可放弃聚会,好像有些人的习惯一样;要互相劝勉。你们既然知道那日子临近,就更应该这样。
Kada mu fasa zumunci da juna, kamar yadda wadansu sukan yi. A maimakon haka, bari mu karfafa juna a kulluyomin, kamar yada kuke ganin kusantowar ranan nan.
26 如果我们领受了真理的知识,还是故意犯罪,就再没有留下赎罪的祭品了;
Saboda idan mun ci gaba da zunubin ganganci bayan mun rigaya mun sami wannan sanin gaskiyar, hadayar irin wannan zunubi bata samuwa.
27 剩下的只有恐惧,等待即将到来的审判,以及毁灭敌视上帝之人的可怕火焰。
Maimakon haka, sai fargabar babban tsoron hukunci, da kuma wuta mai zafi, da zata cinye makiyan Allah.
28 如果有人违背摩西的律法,凭着两三个证人,他仍然得不到怜悯,需要去死;
Dukkan wanda ya ki bin dokar Musa zai mutu ba tausayi ta wurin shaidu biyu ko uku.
29 何况是践踏上帝之子,无视那让他圣洁的立约之血,把它当作俗物,滥用恩典之灵,你们想想,他会遭受怎样的惩罚?
Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri?
30 我们知道上帝他说过:“我要确保正义得到伸张;我会给人们其应得的东西。”他还说:“主必审判他的子民。”
Domin mun san wanda yace, “Ramako nawa ne; Zan yi sakayya.'' Sa'annan kuma, “Ubangiji zai hukumta jama'arsa.”
31 在永生神的大能下是很可怕的。
Abin tsoro ne a fada cikin hannuwan Allah mai rai!
32 回想从前的日子,那时,你们理解了真理后,忍受了许多痛苦;
Amma ku tuna da kwanakin baya, bayan da ku ka sami haske, yadda kuka jure babban fama cikin wahala.
33 有时会被侮辱和攻击, 又要与那些受苦的人团结地站在一起。
Aka kunyatar da ku a gaban jama'a, ta wurin ba'a da cin mutunci, kuna kuma dandana irin azabar da wadansu suka shiga ciki.
34 你们同情那些遭监禁的人;你们的家业被抢夺的时候,又以欢喜的心接受,因为知道自己有更美长存的家业。
Domin kuna da tausayi ga wadanda suke kurkuku, da farin ciki, kun amince da kwace na dukiyarku da aka yi, kun mallaki madauwamiyar mallaka mafi kyau. Dominn kun ji tausayina sa'adda na ke a kurkuku.
35 所以,你们不可丢弃坦然无惧的心,这样的心必有丰厚赏赐。
Don haka kada ku yarda gabagadinku, wanda ke da babban sakamako.
36 你们还需要忍耐,好让你完成上帝的旨意,可以领受承诺的一切。
Domin kuna bukatar hakuri don ku sami abin da Allah ya alkawarta, bayan kun aikata nufinsa.
37 “还有一点点的时候,他会来,正如他所说的,不会迟延。
“Domin a dan karamin lokaci, mai zuwan nan zai zo ba zai yi jinkiri ba.
38 那些做正确之事的人,会因信上帝而活着;如果他们背弃承诺,他们不会让我感到满意。”
Adalina kuwa zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan yi farin ciki dashi ba.”
39 但我们不是那种退缩并最终迷失的人, 而是那些相信上帝会拯救我们的人。
Amma mu bama cikin wadanda suka ja da baya zuwa hallaka. Maimakon haka, muna cikin wadanda suke da bangaskiya domin kula da rayukanmu.

< 希伯来书 10 >