< 哥林多后书 2 >

1 正因为如此,我决定还是不要造访你们,再一次为你们带来忧愁。
Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba.
2 如果我让你们忧愁,谁还能让我快乐呢?, 不会是那些我让他们忧愁之人。
Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba?
3 所以我撰写了这封信,免得那些本会让我快乐之人,带给我忧愁。我深信,你们所有人都会分享我的欢乐。
Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka.
4 在撰写这封信的时候,我曾多次留下泪水,内心充满苦痛和沉重。这并不是为了让你们悲伤,而是让你们知道我对你们的爱有多深。
Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku.
5 我并不想言过其实,但那个人带给你们所有人的痛苦,远远超过我。
Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka.
6 因你们中的绝大多数人,那个人遭受了足够的惩罚,
Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa.
7 所以现在你们应该饶恕他,友善对待他,免得他陷入绝望。
Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta'azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi.
8 所以,希望你们要公开地向他表明你们的爱。
Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili.
9 我正是出于这个原因才写了那封信,就是为了解你们的真实性格,是否会凡事顺从。
Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai.
10 你们宽恕谁,我就宽恕谁。无论我宽恕了什么,都已在基督面前为了你们而宽恕。
Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu.
11 这样做才能避免让撒旦有机可乘,我们太了解他的诡计了。
Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba.
12 当年我为传播基督福音到了特罗亚,主便为我开启一扇机会之门。
Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa'azin bisharar Almasihu a can.
13 但那时候的我因为找不到兄弟提多,心里无法感到安宁。于是我辞别众人去往马其顿。
Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan'uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya.
14 但赞美上帝,他总是在基督里带领我们进行胜利的游行。无论我们身在何处,都能通过我们传播上帝知识的芬芳气息。
Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko'ina.
15 我们就像基督先给上帝的气息,从获得拯救以及正在消亡的人群中散发出来。
Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka.
16 对于死亡之人而言,这气息就是腐烂的气息,对于获得拯救的人而言,这气息就是生命的芬芳!
Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan?
17 我们不像大多数人那样,用上帝之道谋取利益。相反,我们真心诚意分享上帝之道,知晓上帝正在观察我们。
Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.

< 哥林多后书 2 >