< 彼得前书 5 >
1 我想鼓励你们中的长老们。我也是一名长老,是基督受难的见证人,那即将到来的荣耀将有我的一份。
Ina yiwa dattawan da ke cikinku gargadi, ni da nike dan'uwanku dattijo, mashaidin shan wuyar Almasihu, ni kuma mai samun rabo ne daga cikin daukakar daza a bayyana.
2 看好上帝赐予你、让你照顾的羊群,不是因为你被迫这样做,而是因为高兴,因为上帝希望你这样做。你要心甘情愿地这样做,而不是想从中获利。
Saboda haka na gargade ku dattawa, kuyi kiwon garken Allah dake tare da ku. Ku kula da su, ba a kan dole ba, amma domin kuna son yin haka, bisa ga yin Allah. Ku kula da su, ba don cin ribar banza ba amma sabo da yardar rai.
3 不要狂妄自大,凌驾于被你照顾之人之上,而是要成为羊群的榜样。
Kada ku zama kamar masu iko akan mutanen dake hannunku, amma ku zama abin koyi ga garken.
Sa'adda za a bayyana Sarkin Makiyaya zaku karbi rawanin da darajarsa bata dushewa.
5 年轻人,按照长老的吩咐去做。事实上,你们所有人都应该谦卑地为彼此服务,因为“上帝反对骄傲之人,偏爱谦卑之人。”
Hakannan, ku kuma samari kuyi biyayya ga dattawa. Dukanku kuyi damara da tawali'u, kuna bauta wa juna, domin Allah ya na tsayayya da mai girman kai, amma yana yiwa masu tawali'u alheri.
6 在上帝强大的手面前要谦卑,这样他就会在适当的时候把你举起来。
Saboda haka ku kaskantar da kanku karkashin hannuwan Allah mai iko duka domin ya daukaka ku a madaidecin lokaci.
Ku jibga masa duk taraddadin zuciyarku, domin yana kula da ku.
8 要负责任,保持警惕。魔鬼是你的敌人,像咆哮的狮子一样四处游荡,寻找可以吞噬之人。
Ku natsu, ku zauna a fadake. Magabcinku, ibilis, kamar zaki mai ruri yana zazzagawa, yana neman wanda zai cinye.
9 要坚定地反对他,相信上帝。记住,世界各地其他和你一样的信徒,也正在经历类似的问题。
Ku yi tsayayyiyar gaba da shi. Ku yi karfi cikin bangaskiyarku. Ku sani fa abokan tarayyarku da suke cikin duniya suna jimrewa da shan wuyan nan irin taku.
10 你受苦一小段时间之后,那所有恩典的上帝,那曾召唤你、让你与基督一样走进其永恒荣耀的上帝,就会亲自将你恢复,支持你,给你力量,并给你一个坚实的基础。 (aiōnios )
Bayan shan wuyarku na dan lokaci kadan, Allah mai alheri mara iyaka, wanda ya kiraye ku zuwa ga madawwamiyar daukakarsa cikin Almasihu, zai kammalaku, ya kafa ku, ya kuma karfafa ku. (aiōnios )
11 愿力量永永远远属于他!阿门。 (aiōn )
Mulki ya tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. (aiōn )
12 我是在西尔瓦努斯的帮助下,将这封信寄给你们,他是我值得信赖的兄弟。通过我所写的这些文字,我想鼓励你们并见证这是上帝真正的恩典。要坚定地站在上帝的恩典中!
Na amince da Sila amintaccen dan'uwa ne, kuma na rubuto maku a takaice ta hannunsa. Ina yi maku gargadi ina kuma shaida maku cewa abin da na rubuto alherin Allah ne na hakika. Ku kafu a cikinsa.
13 在 “巴比伦”这里的信徒,和你一起被选中,向你问候,就像我的儿子马克一样。还有我的儿子马克也问候你们。
Ita matar da ta ke a Babila zababbiya tare da ku, ta na gaisheku, da Markus, dana, yana gaisheku.
14 以爱的吻互相问候。愿你们所有与基督同在之人都能够平安。
Ku gai da juna da sumbar kauna. Salama ta tabbata a gare ku dukanku da ke cikin Almasihu.