< Mark 2 >

1 Da a kumaye ni Capernaum ni mi vi fie mee, ndi ba woh da hei niko.
Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida.
2 Gbugbu ndi ba tsutsu da shuni bubua, ikon 'u” zu no ri koha ana heina, Yes sibla tre nibawu.
Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana.
3 Indi nzah ba jin vayi mba wa a chronchu ye ni Yesu.
Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi.
4 Bana to ikoh “u” ri hi ni Yesu na, ba hon zu ni tukan, da ghlen tukan, da ban ndi “u” chronchu rini Yesu.
Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai.
5 Yesu toh gbegble suron ba da tre ivre ba wur lahtre me hle ni wu.
Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, “Da, an gafarta maka zunuban ka”.
6 Se bibla vuvu wa ba sun ni ki, ba si rimre nisuron ba di Yesu lahtre,
Amma wadansu marubuta da ke zaune a nan, suka yi tunani aransu.
7 Ba indi da ani wur lahtre ndi hlega, sai Irji nikankrima ni wur lahtre ndi hlega
Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?”
8 Yesu toh misuron ba da miyen ba agye nji meme mmre ba ye ni yi wu?
Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, “Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku?
9 Niwa ba kpa lahtre wurhle ni ba wu, ni wa ba hla ban blame ni hi kpame, a time agan?
Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'?
10 Yesu a toh di vre Irji a hei ni gbengbenlen “u” wur lahtre hle ga, da hla ni ndi wu chronchu,
Amma domin ku san cewa Dan mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya, ya ce wa shanyayyen,
11 mi hla “u” lude di ban blame di hi koh.
''Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka.”
12 Indi wu chronchu a lude ban blama da hi kpa ma, Indi ba buh iyuen yo woh da tre, kina taba toh Bibi kpei nayi na.
Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, ''suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba.”
13 Yesu rhu hi ni kosan nei, ndi gbugbu ba hu hi ni neila, wa ka si bla tre ni bawu.
Ya sake fita gefen tafki, dukan taron jama'a suka zo wurinsa, sai ya koya masu.
14 Da asi zre da toh Levi ivre Alphaeus a kuson ni bi kpa ban. Yesu du hu wawu, wa lude hu Yesu.
Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, “Ka biyo ni.” Ya tashi, ya bi shi.
15 Yesu si rhi lah mi koh Levi, in bi kpa ban gbugbu, baba bi lahtre wasi rhi no “u” baba mrikon, ndi gbugbu ba hu.
Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi.
16 Farisawa bibla vuvu, ba toh Yesu si ri biri nikoh Levi da miyen mri koh ma a gye sa ti kohbi si ribiri ni bi lahtre?
Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, “Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?”
17 Yesu woh ba da tre indi wa ahei ni gbengbenlen ana wa den na, see ndi “u” lilo niwa den. Mi na ye nitu bi woh tre mu na, mi ye ni tubi lahtre.
Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, “Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi.”
18 Mrikoh Yohana baba Farisawa bata son ni hlama, indi baye da tre ahigye sa mrikoh Yesu bana vu hlana na?
Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, “Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?”
19 Yesu ka hla ni bawu, ayiwu kpukpan ango ba ka son ni hlama
Sai Yesu yace masu, “Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba.
20 Se chachu wa ba ban ango rhu, “u” ba son ni hla ma.
Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi.
21 Ba ndi a niwar klon sisama nitu chiche ma, don ani ya yabba sisama game.
Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa.
22 Ba ndi wa ani ban hi sama sur ni chiche ri, don ani fu hle ga, se ba ka sur sama ni miri sama.
Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka.”
23 Ni chachu sati Yesu si zre zu ni mi rhu, mrikohma ba zi gbusu tan.
A ranar asabar Yesu ya tafi cikin gonakin hatsi, sai almajiransa su ka fara zagar hatsi,
24 Farisawa baka tre ni Yesu du toh ikpie a di mrikoh me ba si ti kpie wa dana bina ni chachu sati.
Sai Farisawa su ka ce masa, “Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?”
25 A miye ba, bina toh ikpie wa Dauda baba ndima ba ti na? iyoun ti ba,
Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi?
26 baka hini Abitha ndi wu ton du Irji, waka noba breadi chachu sati, “u” ba ka tan
Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi.”
27 Yesu tre ba ti chachu sati ni idi, bana ti indi ni chachu sati na.
Yesu yace, “Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba.
28 Ni tu ki Ivre Indi a hi “u” Bachi “u” chachu sati.
Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar.”

< Mark 2 >