< Luke 19 >
1 Yesu ari si zu ni Yeriko.
Yesu ya shiga Yariko ya na wucewa cikinta.
2 U ndji ri he ni ki ni nde Zakka. Ana ndji u kpa haraji nda he wo.
Sai ga wani mutum a wurin mai suna Zakka. Shugaba ne na masu karban haraji, kuma mai arziki ne.
3 A wa nkon wa ani to ka nha hi Yesu amma nda mha njima wokran don gbugbu ndji ba u don aku nkpurju.
Yana kokarin ya ga ko wanene Yesu, amma bai iya gani ba sabo da yawan jama'a, domin shi gajere ne.
4 A tsutsu guchi ni ndji ba hi ko shishi nda ka hon kunkro (Sycamore - durumi) nda ka don towu; don Yesu a tie whiwhre u zu nkon kima.
Sai ya ruga gaba ya hau itacen baure domin ya gan shi, saboda Yesu zai wuce ta wannan hanya.
5 Da Yesu ye ni bubu'a, a nzuya shu nda hla wu, “Zakka, grji ue gbagbla, don luwa gbigbi me son koh me.”
Sa'adda Yesu ya zo wurin, ya kalli sama sai ya ce masa, “Zakka, ka sauko da sauri, domin yau dole in sauka a gidanka.”
6 U wa grji nitsu me nda ye kpa ni ngyiri.
Sai ya sauko da sauri, ya karbe shi da farin ciki.
7 Da ko nha a toh, baka na son na wawu mbawu, nda tre, “A ye hi ziri ni koh ndji u lahtre.”
Sa'adda dukansu suka ga wannan, sai suka yi gunaguni, cewa, “Ya ziyarci mutum mai zunubi.”
8 Zakka kri nda hla ni Bachi, “Toh mba Bachi, nh'ma ha u kpie me he wu'a me nno bi ya, mba u mita mla ndrjo kpieri, me nno nkpu nza rjula.”
Zakka ya tsaya ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji, zan ba matalauta rabin arzikina, idan kuma na cuci wani a kome, zan mai da adadinsa sau hudu.”
9 Yesu hla niwu, “Luwa cheto aye ni koh yi don wawu me ahi Vren Ibrahim.
Yesu ya ce masa, “Yau ceto ya shigo wannan gida, domin shi ma dan Ibrahim ne.
10 E, Ivren Ndji a ye wah nda kpa bi wa ba kado'a chuwo.”
Gama Dan Mutum ya zo ne domin ya nemi, ya kuma ceci batattun mutane.”
11 Da ba wo tre ba, a trenda hla misali ri ni bawu, ka ahe whiwhre ni Wurushelima, u ba ban koh mulki Irji tiewhre u ye.
Da suka ji wadannan abubuwan, ya cigaba da magana, sannan ya fada masu wani misali, domin yana kusa da Urushalima, sai suka yi tsamani mulkin Allah za ya bayyana nan da nan.
12 A tre towa, “Indji ri wa ani to tie a hi ni gburi gbugbanmu nda hi kpa chu nda kma ye.
Sai ya ce, “Akwai wani mutum mai sarauta wanda ya tafi wata kasa mai nisa domin ya karba wa kansa mulki sa'annan ya dawo.
13 A yo mri koh ma wlon nda nno ba pa wlon, nda hla bawu, 'Hi kasran niwu gbien kma yemu.'
Sai ya kira bayinsa guda goma, ya ba su fam goma, sai ya ce masu, 'Ku yi kasuwanci da wannan har sai na dawo.'
14 Amma indji ma ba kranwu nda nton ndji mba bari hu gonma nda hla, 'Kie na kpanyime ndi ndu ndi yi ndu chu mbu na.'
Amma mutanensa suka ki shi sai suka aiki jakadu bayansa, cewa, 'Ba za mu yarda wannan mutum ya yi mulki a kanmu ba.'
15 Ba he wa aka kpa chu nda kma ye, a ndu ba yo gran ma ba wa anno ba inklen nda to riba wa ba tie.
Anan nan sa'adda ya koma kuma, bayan da ya sami mulkin, sai ya ba da umarni a kira masa bayin da ya basu kudi, domin ya san ribar da suka samu wajen kasuwancin da suka yi.
16 U mumla a ye niwu nda tre, 'Bachi mu, pa me'a wa une'a a nji pa wlon ye nha.'
Na farkon ya zo wurinsa, cewa, 'Ubangiji, fam nan na ka ya yi riban fam goma.'
17 Ichu'a hla wu, u toh tie, u gran ndindi, Ni wa u toh tie ni kpie tsitsa ma, u he ni igbu zan wlon wa wu nji mba.'
Masaraucin ya ce masa, 'Madalla, bawan kirki. Domin ka yi aminci a karamin abu, za a baka iko kan birane goma.'
18 U ha ye nda tre, pa me Bachi, a nji pa ton bari ye.'
Na biyun ya zo, yana cewa, 'Fam na ka, Ubangiji, ya yi ribar fam biyar.'
19 Ichu'a hla wu, 'U kpa gbu ton wa wu nji'a.
Sai masarauncin yace masa, 'Ka dauki mulkin birane biyar.'
20 Iri ye nda tre, Bachi, ngye pa me'a yi, mi ka ri mlazi ni mi kpi,
Wani kuma ya zo, yana cewa, 'Ubangiji, ga fam naka da na ajjiye shi da kyau cikin kaya,
21 don mi klu sissri me, don u ndji u nno ya. U ban ni bubu wa una zi'a na.
gama na ji tsoronka, domin kai mutum mai tsanani ne. Kana daukar abu da baka ajiye ba, kana kuma girbin abin da ba ka shuka ba.'
22 U chu'a hla wu, 'Ni tre u nyu me ba me han tre'a nitu me, wu meme gran. Wu toh ndi mi ndji wa mi wa bran, ni ban ikpi wa mi na kazi'a na, u me hi vu ikpie'a mi na chuna.
Masarauncin ya ce masa, 'Da kalmominka zan shari'antaka, kai mugun bawa. Ka sani cewa ni mutum mai tsanani ne, ina daukan abinda ban ajiye ba, ina kuma girbin abinda ban shuka ba.
23 Don ngye una yo nklen ni banki toh mi na kma ye mika kpa nha ni a hon tuma (riba) na?
To don me ba ka kai kudi na wurin masu banki ba, saboda bayan da na dawo zan karbe shi da riba?'
24 Ichu'a hla bawu wa ba kri wu'a, 'kpa pa wa ahe ni wu'a, ndi ka nno u pa wlon'a.'
Masaraucin ya ce wa wadanda suke a tsaye a wurin, 'Ku karba fam da ke a wurinsa, ku ba mai fam goman nan.'
25 Ba hla wu, Bachi, a he ni pa wlon.'
Suka ce masa, 'Ubangiji, yana da fam goma.'
26 Mi hla yiwu, indji wa a he wu'a, ba nno tia, amma uwa a hama wu'a, ba kpa mbru wa ahe niwu.
'Ina ce maku, duk wanda yake da abu za a kara masa, amma wadda bai da shi, za a karba sauran da ke wurinsa.
27 Amma biyi, bi yo shishi nime, bi wa bana nyime ndu me chu mba na, nji ba ye wayi ndi wu ba ni shishi mu.'”
Amma wadannan abokan gabana, wadanda ba sa so in yi mulki bisansu, a kawo su nan a kashe su a gaba na.'
28 Da a hla tre bi yi, a vu gon ma hi Wurushelima
Da ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi gaba, yana tafiya zuwa Urushalima.
29 Ba he me wa a ye whiwhre ni Baitfaji mba Baitanya, nitu ngblu wa ba yo ndi Zaitun, wa ka ton mri koh ma harhi,
Ananan sa'adda ya zo kusa da Baitfaji da Baitanya, a kan tudu da a ke kira Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, cewa,
30 ndi, “Hi nimi vi gbu wa ahe ni ko shishi mbi'a. Bita ta ri, bi toh vren nakpron wa bana honwu to na. Siwu ndi njiwu yemu.
cewa, “Ku tafi cikin kauye da ke gabanku. Sa'adda ku ka shiga, za ku same dan aholaki da ba a taba hawansa ba. Ku kwance sai ku kawo mani shi.
31 Indrjo nita mye yi, 'Bi siwu ni ngye?' Bika hla, Bachi mba ni son.'”
Idan wani ya tambaye ku, 'Don me ku ke kwance shi?' Ku ce, 'Ubangiji ne ke bukatarsa.”
32 Biwa ba ton ba, bahi nda kato vren na pron'a towa Yesu a hla bawu'a.
Wadanda aka aike su suka je sun sami aholakin kamar yadda Yesu ya gaya masu.
33 Baka ki si vren nagro, kikima baka mye ba, “Bi si vren nakpron ni ngye?”
Sa'adda suna kwance aholakin, sai masu shi suka ce masu, “Don me ku ke kwance aholakin?”
34 U ba tre, “Bachi ni son.”
Suka ce, “Ubangiji yana bukatar sa.”
35 Ba nji ye ni Yesu, nda lba ba kpi mba ni tu vren nakpron nda ban Yesu sa tuma.
Suka kawo wa Yesu, suka shimfida tufafinsu akan aholakin sai suka dora Yesu akansa.
36 Da si zren, baka lba ikpi bi sru kpa mba ni tu nkon.
Da yana cikin tafiya, suka shimfida tufafinsu akan hanya.
37 A tie whiwhre ni blaba ngblu Zaitun, u gbuj'bu mri koh ma baka ku'u ngyiri nda ni gbre Irji san ni ngyiri kpukpo me nitu wa ba toh ikpie wa atie'a wa nno ba sissri,
Da ya yi kusa da gangaren tudun Zaitun, sai dukan taron almajiransa suka fara yin murna suna kuma yabon Allah da murya mai karfi domin dukan ayukan al'ajibi da suka gani,
38 nda tre, “Lulu a hi'u chu wa asi ye nimi nde TieTie! Salama ni shulu daraja wa a zan dauka!”
cewa, “Albarka ta tabbata ga sarki da ke zuwa cikin sunan Uba! Salama a sama da daraja mafi daukaka kuma!”
39 Farisawa bari nimi jbu hla wu, “Ticha yra nha ba”
Wadansu Farisawa daga cikin taron jama'a suka ce masa, “Malam, ka tsauta wa almajiranka.”
40 Yesu a sa bawu, Mi hla yiwu njanjimu, biyi bata ki ngbangbi, tita ba yra gro.”
Yesu ya amsa ya ce, “Ina gaya maku gaskiya, in wadannan sun yi shiru, duwatsu za su yi shewa.”
41 Wa Yesu tie whiwhre ni gbu'a, ayi nitu ma,
Sa'adda Yesu yana kusatowa, sai ya yi kuka akan birnin,
42 nda tre, Bina toh wiyi, ko bina toh ikpi wa ba nji salama ye yiwu! Amma zizan ba riba ni shishi mbi.
cewa, “Da kun san wannan rana, ko ku ma, abubuwan da ke kawo maku salama! Amma yanzu an boye su daga idanunku.
43 Ivi ni ye niwu wa bi kamba niwu ba me gle kagon me, nda mau krju tie.
Gama rana zata ta zo a gareki, da makiyan ki zasu gina ganuwa a kewaye da ke, su kuma fada maki daga kowace gefe.
44 Ba tsenu hlega meme ni mri me. Ba don tita ri nitu ri na, don una toh inton wa Irji sison zo nda kpa'u chuwo.”
Za su sare ki kasa tare da 'ya'yanki. Ba za su bar wani dutse akan dan'uwansa ba, domin ba ki lura da lokacin da Allah ya na kokarin ceton ki ba.”
45 Yesu a ri ni tra Irji nda tsihi ka zu bi le
Yesu ya shiga Haikalin sai ya fara korar masu sayarwa,
46 nda hla bawu, “Ba nha zi, Ikoh yi ani koh u aduwa amma u bi ka tie iwru bi y'bi.”
ya na ce masu, “A rubuce yake, 'Gida na zai zama wurin addu'a,' amma kun mayar da shi kogon mafasa.”
47 Yesu ahe nda zi tsun ni tra Irji cacuwu, Amma, Firist bi ninkon ba ni nha ni bi ninkon u nda ba, ba wa nkon u wu-u,
Yesu yana nan yana koyarwa kowace rana a cikin haikali. Amma manyan firistoci da marubuta da shugabanin jama'a suna so su kashe shi,
48 amma bana toh nkon na, don indji ba siya wowu.
amma ba su sami hanyar yin wannan ba, domin mutane suna sauraron sa sosai.