< Yohana 9 >

1 U Yesu ka si hi, nato iguri u fyen wa ndi a yar shishi tu rji ni wa ba ngrji'a.
Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa.
2 U almajere ma ba miyen wu, “Mala, ahi nha mba latre, ahi gu'a ka a ba Itma ba Iyimma, wa ba ngrji ti fyen naki?”
Sai almajiransa suka tambaye shi, “Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?”
3 Yesu hla ni bawu, ana igu'a na a na, Itima bi Iyima na wa ba la tre na, ani ndu iIti Irji tsira.
Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
4 A gbigbi ndu ta ki ti ndu wa a ton me rji ni mumla. Ichu ni ye iwa idiori na tindu na.
Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki.
5 Ni wa mi he ni gbungbulu'a ime yi mi ikpan u gbungbulu'a.
Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya.”
6 Ni kogon wa Yesu hla ikpi biyi a ti ten yo meme, na tsie iten ni meme'a, na vu gban ni shishi gu'a.
Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar.
7 Na hla niwu hi, ni hi ngla ni takpo ma u Siloan (wa ani hla ndi mi ton).” Igu'a luhi na ka ngla, a kaban ye na ni to.
Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike).” Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani.
8 U indji bi igon kanhlan mba ni bi wa ba zi to rji ni sisenmu'a ani bre, u ba tre, “ana igu yi'i wa ani son na ni bre'a na?”
Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, “Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?”
9 Bari ba tre, a wawuyi, bari ba tisan, 'A'a, a rju wawu yi,' iwawu tre, ahime wawuyi.”
Wadansu suka ce, “shi ne.” Wadansu suka ce, “A'a, amma yana kama da shi.” Amma shi ya ce, “Ni ne wannan mutum.”
10 U ba tre niwu, ba bu'u shishi'a ni he?
Suka ce masa, “To yaya aka bude maka idanu?”
11 I wa sa ni bawu, iguri wa ba yo ni Yesu a hu meme na gban ni mu shishi na hla nimu, hi ni ne Siluwan ni ngla u mi hi ka ngla, u shishi lu ni to.
Sai ya amsa, “Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani.”
12 U ba miyen, “Ahe ni tsen?” wa hla, mina to na.”
Suka ce masa, “Ina yake?” Ya amsa, “Ban sani ba.”
13 U ba nji igu hi iwa ana indji u fyen ni Farisawa.
Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa.
14 Ahe ni ivi u asabar wa Yesu a hu meme na bu'u shishi niwu.
A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu.
15 U Farisawa ba la miyen ngari ya da a fe nito bubu, a hla bawu, a yo meme ni mu shishi u mi nglau zizan ni to.”
Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, “Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani.”
16 Ba ni mi Farisawa ba tre, iguyi a indji Rji na, ana ni to ivi u asabar na.” U bari ba tre, “Indji u latre ni ti ni heri na to ti gban biki?” ba ga kpa ti hari.
Wadansu daga cikin farisawa suka ce, “Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. “Wadansu suka ce, “Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?” Sai rabuwa ta shiga tsakanin su.
17 U ba la miyen indji u fyen ngari, “U tre ni ngeri ni tuma'a tu rji chachu iwa a bu'u shishi me?” Indji nfyen tre, ahi Anebi.”
Sai suka tambayi makahon kuma, “Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?” Makahon ya ce, “shi annabi ne.”
18 Ye zizan me Farisawa ba me ba na kpa yeme nda ahi wawuyi indji u nfyen na wa ba bu'u shishima na se wa ba yo ba Time ni ba Iyi ma iwa a shishima bu'a.
Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin.
19 U ba miyen ba Tima ni Yima, iwa yi ahi vren bi wa bi tre bi ngrji ni fifyen? Ani he mba ani to zizan?”
Su ka tambayi iyayen, “Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?”
20 U ba Tima ba hla, “Ki to iwa yi a vren mbu wa ki ngrji ni fyen.
Sai iyayen suka amsa masu, “Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi.
21 Ati ni nani ya, kina to na, miyen a sen ndi, ani ya tre kima.”
Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa.”
22 Ba tima ba tre biyi, nitu wa ba si tie sisir Yahudawa. Yahudawa ba ba riga zi indji iwa a tre ikpe wa ani hu gon ma andi ahi Kristi, ba ban ta yo ni mi ta kpoma.
Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a.
23 Nitu kima, ba itima ba tre, “A sen ndi ye, miyen.”
Domin wannan ne, iyayensa suka ce, “Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24 Ngari ba la yo u gyu u ha ba la yo igu fyen na hla niwu, “No Rji ni kon. Ki to igu yi a ndi u latre.”
Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, “Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne.”
25 I gu ki hla bawu, mina to na ka a hi ndji u latre na. Ikpe riri mi to na'a mina ndji u fyen, u zizan mi to.”
Sai wannan mutum ya amsa, “Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani.”
26 U ba tre ahi geri a ti niwu?” ani he a bu'u shishi niwu?
Sai su ka ce masa, “Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?”
27 Wa hla, “Mi hla ni yiwu ye, bina wo na ahi geri bi son bi wo ngari?
Ya amsa, “Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
28 U ba mren na hla, u almajerema, ki ta ki almare u Musa.
Sai suka kwabe shi suka ce, “kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne.
29 Ki to Irji a tre ni mu, ki na to i wurji wa iwayi a rji'a na.”
Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba.”
30 Igu'a sa bawu na tre, iwayi a kpe u shan (mamaki), iwa bina to iwurji iwa a rji'a na, me a bu'u shishi mu.
Mutumin ya amsa masu ya ce, “Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu.
31 Ki to Irji na wo indji bi latre na, indji wa anita no tuma na ni tie ikpe wa ani son, ani wo wu.
Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa.
32 Rji ni tuntru mu ni gbugbulu'a ki ti bre wo ndi idiori bu'u shishi ni indji wa ba ngrji ni fyen na. (aiōn g165)
Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba. (aiōn g165)
33 Ide indji'a ana rji ni Rji na, ana ya ti kperi na.”
In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba.”
34 U ba sa niwu nha hla niwu, wawu'u ba ngrji ni latre, i u la si tsoro ta? U ba ban ta rju ra.
Suka amsa suka ce masa, “an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?” Sai suka fitar da shi.
35 Yesu a wo andi ba zu rju nimi hekeli'a a wau na tre, u kpayenme ni Vren Ndji?
Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, “Kana bada gaskiya ga Dan Allah?”
36 Wa sa na tre, “Ahi nha, Bachi, wa mi kpayenme niwu?”
Sai ya amsa masa yace, “Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?”
37 Yesu hla niwu, “U to, ahi wawuyi wa a si tre niwu.”
Yesu yace masa, “Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai.”
38 Igu'a tre, Bachi, mi kpayenme, wa no ninkon ma (kwu gbarju niwu).
Mutumin ya ce, “Ubangiji, Na bada gaskiya.” Sai ya yi masa sujada.
39 Yesu tre, “A tron miye, miye ni gbungbulu yi ni ndu biwa ba na to na ndu ba to, U bi wa ba ta to ndu ba yarshi (tifyen).”
Yesu ya ce, “Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi.”
40 Bari ni Farisawa ba, wa ba heni wu'a ba wo wayi, na miye, “Ki me ki yarshi?”
Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, “Muma makafi ne?”
41 Yesu hla bawu, bina yarshi, bina to na, zizan bi tre, kito, naki latre bi riheri.
Yesu ya ce masu, “Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.

< Yohana 9 >