< Yohana 13 >
1 Igan idin tsatsra rigyen u ye, u Yesu to andi inton tsra wa a lu ni gbungblu hi ni Ti'a. Niwa ani son bi ma wa ba he ni gbungblu, a son ba ye ni kekle.
Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe.
2 Ibrji yo ni sron Yahuda Iskariyoti ivren Saminu, aka Yesu le.
Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu.
3 Ato ndi Iti a ka kongeri no ni woma, na rji ni Rji, ani la kma hi ni Rji.
Ya san cewa Uba ya bada kome a hannunsa, kuma ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah.
4 A lunde ni bubu ri biri, na ju kpima, na ban inklon u se ma kpa na ka kpa ma niwu.
Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi.
5 Wa sur ima ni konko na si ngla za ni almajere ma ba na se za ba wu ni inklon u se kpa wa a ka kpama niwu'a.
Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi.
6 Na ye ni Siman Bitrus, u Bitrus tre niwu, “Bachi, u ngla za mu me?”
Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa,”Ubangiji, za ka wanke mani kafa?”
7 Yesu sa niwu na tre, “Ikpe wa mi si ti'a una to na zizan? U to ni ton u ye (ajima).
Yesu ya amsa ya ce, “Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta.”
8 Bitrus hla niwu, una ti bre ngla za mu.” Yesu hla niwu, “Mita ngla niwu na, una he ni san me ni me na.” (aiōn )
Bitrus ya ce masa, “Ba za ka taba wanke mani kafa ba.” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni”. (aiōn )
9 Siman Bitrus hla niwu, “Bachi, na ngla zamu migyen na, ngla womu ni tu mu.”
Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina.”
10 Yesu hla niwu, “Indji wa a sukpa'a ana wa sukpa na, se ka ngla za, wa ahi tsatsra ndji wawu bi tsatsra, ama ani wawu mbi na.
Yesu ya ce masa, “Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba.”
11 (Yesu a to indji wa ani kawu le, kima sa wa tre naki, ana wawu mbi bi tsatsra na).
(Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, “Ba dukanku ne ke da tsarki ba.”)
12 Ni kokon wa Yesu ngla za bawu, a ban konlon ma na kuson ngari, na hlabawu, “Bito kpe wa mi ti ni yiwu'a?
Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, “Kun san abin da na yi muku?
13 Bi yo me ni 'Mala' ni 'Bachi,' u bi yo me tsra, a naki mi he.
kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake.
14 U to Me wa mi Bachi ni Mala, u mi ngla za mbi, biyi ngame bika ngla za ni kpambi.
Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu.
15 U mi tsro yi misali, ni ndu ti na wa mi tie ni yiwu.
Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku.
16 Gbigbi njanji mi si hla ni yiwu, igran na zan tiko ma ni ninkon na, ivren u ton ndu ana zan indji wa ton'u ndu ninkon na.
Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba.
17 Bita to kpi biyi, bi-bi lulu ni nde bi ti ba.
Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su.
18 Mi na si tre yi wawu na; Mi to biwa mi chu ba'a - nitu ndi nassi tsra indji wa a tan bredi a tayar nimu.
Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'.
19 Mi si hla wa yi ni yiwu zizan ri ni ndu ka ti naki ni ndu yi ka kpa-nyeme ni me ni nton wa ani ti naki'a.
Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne.
20 Njanji, njanji, mi si hla ni yiwu, indji wa a kpa ndi wa mi ton'wu, ahi Me a kpa, indji wa a kpa Me, a kpa Indji wa a ton Me.
Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni.
21 Ni kogon wa Yesu tre naki, na lo sron ni (Ruhu), na ti gban (shada) andi, gbigbi njanji, mi si hla ni yieu ndi iri ni mibi ani le ni me.”
Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni.”
22 Almajire ba ba kma ya kpa mba, na ni tamre, ka ahi nha ni mi mba a si tre ni tu ma.
Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana.
23 Iri nimi almajire ma, wa Yesu ni son, ahe ni tebru, na kunyre ni san Yesu.
Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu.
24 Siman Bitrus hla ni almajire bika minye, “Ndu hla tawu a hi nha a si tre ni tu ma.”
Siman Bitrus ya ce wa almajirin, “ka fada mana ko akan wa ya ke magana.”
25 Wa hla bru kunyre ni san Yesu, na tre niwu, Bachi, ahi nha?
Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, “Ubangiji, wanene?”
26 U Yesu hla niwu, a wawu yi wa mi ka cichon bredi sun ni kano. Naki ri na ka bredi sun, na ka no Yahuda ivren Siman Iskariyoti.
Sannan Yesu ya amsa, “Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi.” Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti.
27 Ni kogon bredi'a u ibrji a ri ni wu, u Yesu hla niwu, “Ikpe wa u son ti'a, uka ti gbagbla.”
To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, “Abinda kake yi, ka yi shi da sauri.”
28 Indrjori na la he ni tebru na, wa ani to ikpe wa yo'a hla niwu naki'a.
Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan.
29 Bari mba ba ya ndi, a Yahuda yi ni nji imbu nklen Yesu hla niwa, “Le ikpe wa ki son ti ndu niwu ni idin,” ko ka no ikpe ni bi wa ba kunyre'a.
Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, “Ka sayi abinda muke bukata don idin”, ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu.
30 Ni kogon wa Yahuda a kpa bredi'a, wa rju gbagbla gbagbla me ni chu me.
Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa.
31 Ni kogon wa Yahuda hi'a, Yesu tre, zizan ba no Vren Indji ni kon, ngari ba no Irji ninkon ni mi ma.
Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, “Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa.
32 Irji ni no ninkon ni mi ma, ani no ninkon zizan zizan.
Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan.
33 Imri bi tsitsa mi he ni yi ni vi ton tsa me, biwa me na wa mi hla Yahudawa, bubu wa me mi hi bi na ya hi na. Zizan mi hla wa yi ni yiwu.
'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan.
34 Mi si no yi indu ri sama, son kpa mbi, na wa mi son yi, na bi ka son kpambi.
Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna.
35 Na ko nha ni to yi ndi bi almajire mu, inde bi son kpambi.”
Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna.”
36 Siman Bitrus tre niwu, Bachi, u hi ni ntsen?” Yesu hla ni wu, bubu wa mi si hi'a, una ya hina me zizan hi na, u wuka ye hu me ni kogon.”
Siman Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya.”
37 Bitrus hla niwu, “Bachi, a ngyeri mba sa mi na hu zizan na? Mi no re (ivri) mu ni tu me.”
Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka.”
38 Yesu hla niwu, u ka re (ivri) me no ni tu mu? Gbigbi njanji, mi si hla niwu, u kame ni me ni kpatron ingyu tra ri ndu mble ndu kpan
Yesu ya amsa ya ce, “Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku.”