< James 4 >
1 a hinge ni ji vii ni hama ni katu kabi ye ni mi mbi/
Me ke kawo gaba da rashin jituwa a tsakanin ku? Ba yana tasowa ne daga muguwar sha'awa da ke yaki a cikin ku ba?
2 son ndi na nafe na bi wuundu tiengu bina fena bi tsi ni vii u zizan bina fena don bina mye na
Kuna sha'awa, kuma ba ku da shi. Kuna kisa da kyashi, kuma ba za ku iya samu ba. Kuna danbe da fada. Har wa yau baku samu ba domin baku tambaya ba.
3 bi bre ndi na fe na don bina bre ni kon ndindi ma na bi son ndi bi tie ndu niwu ni kon meme ma
Kun roka kuma ba a baku ba saboda kuna roko ta hanya mara kyau, kuna so ku yi amfani da shi domin miyagun sha'awoyin ku.
4 biyi bii tie kan binato na tie kpan ni ngbungblu ahi kwatre rji?
Ku mazinata! Baku sani ba, abokantaka da duniya, tawaye ne ga Allah? Don haka duk wanda ya shiga abokantaka da duniya ya zama magabcin Allah.
5 bisi ya ndi ikpe wa nasi hla ahe megen? ibrji tsratsra wa a he ni i mbua nitie ngu kpukpo me?
Ko kuna zaton nassi ya fadi haka a banza ne, “Ruhun nan da ke a cikinmu yana da kishi matuka?”
6 irji nno zizi babran itre rji tre ndi irji ni kamani ndrji u sentu ani tie zizi ni ndrji u katugyi
Amma Allah ya bayar da karin alheri, shi ya sa nassi ya ce, “Allah yana gaba da mai girman kai, Amma yana ba da alheri ga mai tawaliu.”
7 nnotumbi ni rji kambi ni shetan ani tsutsu di kon yuwuu
Saboda haka ku mika kan ku ga Allah. Ku yi tsayayya da shaidan, zai kuma guje maku.
8 whie ye ni rji u wawu me ni whie ni yi ngla wo mbi biyi bi latre ngla sron mbi biyi bi sron ha
Ku matso kusa da Allah, shi kuma za ya matsa kusa da ku. Wanke hannayen ku, ku masu zunubi, ku tsabtace zukatan ku, ku masu zuciya biyu.
9 losron kpukpome losron yi ndu nza mbi kati losron ngyri mbi ndu kati yi
Ku yi bakin ciki, makoki, da kuka! Ku mayar da dariyar ku ta koma bakin ciki, farin cikinku kuma zuwa ga bakin ciki.
10 ka tu mbi gji ni shishi rji u wawu ni nzuyi wlunde.
Ku kaskantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuma za ya daukaka ku.
11 na tretre meme nitu vayi me na mrlivayi indji wa a tretre meme ma nitu vayima ko atron nitu vayi ma ani tretre meme ma nitu du nda ni bla tre nitu du a tsro ndi u na to ni nfutu na ukati indji u bla
Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci.
12 indji riri nno du nda tretre wawuyi nito kpa cuwo nda kpa tie meme
Mai ba da shari'a da yin hukunci daya ne. Shine mai iya ceto kuma ya hallakar. Kai wanene, da ke hukunta makwafcin ka?
13 wo mba biyi a bi tre ndi iuwa komble ki hi ni gbu mu ndi tie se ri nikima ndi le ndi fe gbugbuu
Saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu tafi wancan birnin mu yi shekara guda a wurin, muna kasuwanci, mu kuma yi riba.”
14 ahi nhato kpe wa ni te imblea ka son me ni he ni he u he na kpalu wa ani rij niton fie me nda ka kadoa
Wa ya san abin da zai faru gobe, kuma yaya rayuwan ka zai kasance? Kai kamar hazo ne mai bayyana bayan dan lokaci kadan ya bace.
15 nawa u katre ndi baci nita kpa yine u ki he ni mi bi vrli ki tie wayi ndi tie wamu
Maimakon haka, sai ka ce, “Idan Ubangiji ya nufa, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan.”
16 zizan u wuro ni san ni kpe wa uyo nimi sron mea bi bi wuro ni san kima ahi kpe memema
Amma yanzu kana fahariya da shirye shiryen ka na takama. Irin wannan fahariya, mugunta ce.
17 u indji wa ato kpe wa abi ndutiea nda na tieu na a hi latre ni wuu
Saboda haka ga wanda ya san abin da ya kamata ya aikata amma bai yi ba, ya zama zunubi a gare shi.