< Ndu Manzaniba 5 >
1 Ndhiri bayo ndi Ananias mba wama safira ba ban bubumba ri le.
Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu,
2 Nda zi mbru nkle wa ba kpa`a (uwama ngame a to), nda nji mbru nkle ka zi ni za manzaniba.
Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin.
3 Bitrus a tre ndi, “Ananias wu ti he ni du brij shusron me nda du, u tiche ni Ruhi Tsatsra ni kma mbru nkle bubua'a zi ni tume?
Amma Bitrus ya ce, ''Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin?
4 Niwa wuna rhihe u banle'a ana wumena, u niwa wu banle ana rhihe ni wome na? A nha yo kpeyi ni suron me? wuna tiche ni ndhi na, ama ni irjhi”.
Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa.”
5 Niwo tre`a Ananias a ku rhoku u veri ma ka klekle, u biwa ba wo kpe yi ba ti sisiri kpukopme.
Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu
6 Mri rize ba balu banwu cibi nda lo u nda ba u rhu ka rhu.
Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi.
7 Niwa nton tra ati, uwama a riye, ana to ka ngye si grensi zren na.
Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba.
8 Bitrus a tre niwu ndi, “Hla nitawu bi le ni bubumbi mba nitu kpe to yi?” A tre ndi “Ehh, nitu toki.”
Sai Bitrus ya ce mata, ''ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?'' Sai ta amsa, ''ta ce kaza ne.”
9 Mle Bitrus alha niwu ndi, “Ahi ngyeti du yi zontu ni kpambi ndi tsra Ruhu Baci?, ya, za ndhi wa baka rhu lon me ba he ni kontra, ba banwu hi rhu.”
Sa'annan Bitrus ya ce mata, ''Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu.''
10 A kri ku rhoku ni za ma nda gbron vri ma wu kle. Niwa mir nzeba ba ri ye nimi ba to a que nda banwu rhu ka rhu ni kosan bei lonma.
Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta.
11 sisir rigra ma a ti eklisiya wawu ni biwa bawo kpi biyi”a.
Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura.
12 ikpi gbugbuwu wa bana taba to ni son ba na ni chu tro nkankan ba kiya faru ni cikin ndi tawuri mazani ba. Ba ki wawumba ni trankon solomon.
Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu,
13 Mbru ndhi ba bana hini gbengble suron u huba hikina ama ndhiba ba to ba ni nfutu.
Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a.
14 Nikima, ndhi ba ta ye nda ni kpa Bau; ndi lilon baba mba gbugbuwu.
Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata,
15 Nda duba vu bi lilo thuka zi nitu nkon tu bubu kru ko ni bla krumba, ndi i dan Bitrus si zren zu, iwhi ma ni ku nitu bari mba.
har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu.
16 Kpandhi ngame ba ye rhi ni gbu biwa ba ne we were ni urishilima, ni bi lilo baba biwa meme brjhi loba, ba kpa si kpa mba
Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka.
17 Nikima, niko firist alu kri, ni wawu biwa ba heniwu'a (biwa ba he ni derika sadukiawa); ba shuni ngu,
Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka
18 nda yo wo vu manzani ba ka tro ni buba tro. “
suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
19 Nikimame, niwa chu ati malaika u Baci a bwunko wu bubu tro'a nda njiba rhu ra, nda tha bawu ndi
A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
20 “Hi, kri nimi Haikali ni tre ndi ndhiba wawu nitu lantre wu nu vriji”.
“Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.”
21 Niwa ba wo tre yi a, ba ri hi ni haikalia tsra ni bwunble nda tsroba. I a ninkon firt a ye baba biwa baheni wu'a nda yo son shubi bi ninkon gbu baba datibai ndhi bi Israila wawumba, nda tonba hi ni ko tre duba hi nii manzani ba ye.
Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
22 Ofisa wa ba tonbarba hi ka waba hamani ko tro'a nda kima ye lha bawu.
Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto,
23 “Kika to nkotraba baki ni tro vrenme, ni bi ki gben ba ni kontra. Ama niwa ki bwu ni ri, kina to ndior nimi na.
Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba.
24 Ni wo tre yi, captin wu haikalia mba ninko first wawu, ba ku sisiri nitu mba, don kpe wa ni wu gon ma.
Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar.
25 Mle ndhiri a ye nda ye lha bawu ndi, “Ndhi wa bi vu sru ni ko tro ba kri si tero ndhi ni mi haikali.”
Sai wani ya zo ya ce masu, ''Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a.''
26 Kaptin babamir binduma ba wru hi nda ka vu ba ye, hama ni gbiba ni gbeneblen, nitu ba ti sisiri ko ndhi ba ta ba ni tita.
Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu.
27 Niwa ba njiba ye'a ba zi ba shishi bi ninkon'a,
Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su,
28 Nikon first a tsra ba ni mye ndi, “we mha yi ndife yi ton du yi na tsro ni nde yi na, ama bi ka gbu urishilima ni tsro mbi ndi nison nji yi guyi ye sa nitumbu.”
cewa ''Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu.”
29 Bitrus baba manzaniba ba sa ndi, kita ki hu tre irjhi zan tre ndhi.
Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, ''Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba.
30 Irjhi ba timbu a nzu Yesu hi, wandi bi klo wuu ni kunkro.
Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace,
31 Irjhi a nzu u hon hi ni woko ko rhima na uren u tuchu mba wu kpachuwo, don du buw kon tuba ni mir Israila, nda wru latre mba lhe.
Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai.
32 kita ki biwa ki to kpibiyi, ni ruhu tsatsra ngame, wandi Irjhi a nu bi wa ba hu tre ma'a.
Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi.''
33 Niwa, bi ninko wa ba son'a da trea nfu a toba, u bata son wuu manzani ba.
Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.
34 Ama igu pharisawa ri wu nde ma hi Gamalial ndhi wu tsro doka, wandi ndhi wawu ba kpanyme ni wu'a, a lu kri ni minba nda ti gbuchu du manzani ba rhu dinko ni bawu wu ton fime ri.
Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci.
35 Wa alu kri lha ni son ndi, “ndhi Israila, mal ya kpe wa bi tre bi ti ni ndhi biyi.
Sai ya ce masu ''Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan,
36 Kafi du vi biyi ye, Theudus a lu wru nda gbresan ndi wawu hi ndior, u ndhi bari, ba derinzia ba zontu hu. Ba wuu, duka biwa bata hu'a ba vra hi kankan ni zremba ngame a na ti tu na.
A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu.
37 Bay ki ma u, Juda wu Galile a lu kri ni vi wa ba bla ndhi nda gbron bari baka hu. wawu ngame a que kado u biwa bata hu'a ba vera hi kan kan.
Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse.
38 Zizan mi lhayiwu, rhu ni nkon ndhi biyi di don ba toome, idan shiri yo ko ndu yi, hi wundi ana kri gban me na nda vralhe.
Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace.
39 Anita ndu Irjhi, bina iya yi nasara ni ba na bi klna to bisi tsi ni Irjhimu.” Toki ba kpanyme ni tre ma.
Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah.'' Sai suka rinjayu.
40 Mle ba yo manzaniba ri ni son nda lhobatsi nda hla ndi du ba na tre ni nde Yesu na, nda du ba hi kpamba.
Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi.
41 Ba rhu rhi ni son bi ninko'a ni takpe don ba he ni mi biwa ba mla duba ti ba ya nitu ndema.
Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan.
42 Hu kima, chachu, ni mi haikali mba ni ko hi ni ko, ba zi tsro ndani d'bu ni lha njo ndi Yesu wawuyi hi Kristi.
Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.