< Ndu Manzaniba 22 >
1 “Mri vayi baba bati, sren ton ni vri kpachuwo mu, wa mi ti yiwu.”
“Yanuwa da Ubanni, ku saurari kariya ta zuwa gare ku yanzu.”
2 Niwa jbu indji ba ba wo Bulus si tre niba ni lan Ibraniyawa, ba ti whime, A tre ndi,
Da taron sun ji Bulus na magana a harshen Ibraniyawa sai sun yi tsit. Ya ce,
3 Me mi nji Yahudawa, ngrji wu Tarsus ni Cilicia, mi kpa tsro mu ni kikle gbu yi ni za Gamaliel. Mi kpa tsro nitu nkon tsatsra wu du ba ti ti mbu. Mi hu nkon Irji ngyengyere, to wa biyi wawu mbi bi he luwa.
Ni Bayahude ne daga garin Tarwasa na Kilikiya, amma a karkashin Gamaliyal aka ilimantar da ni. An horar da ni sosai bisa ga bin hanyar dokokin kakkaninmu. Ina da himma ga bin Allah kamar yadda ku ma kuna da ita.
4 Miyo bi hu nkon'a iya ka tsra ni kwu, vu ba lo ndi tru ba sru ni kotro, lilon baba mmba,
Na tsananta wa wannan Hanyan har ga mutuwa; na daure maza da mata sa'annan na jefa su cikin gidan yari.
5 me wa kikle Prist baba bi chiche wawu ba vu bla nituma. Mi kpa nha vunvu rhi ni ba hi ni mri vayi wa ba he ni Damascus, I mi hiki nitu hi vuba lo nji ye ni Urushelima ni duba fubaton.
Hakannan ma babban firist da dukan dattawa za su ba da shaida cewa na karbi izini daga wurinsu domin 'yan'uwa da ke a Dimashku, saboda in tafi can. Haki na shine in daure mabiyan Hanyan nan, in kawo su Urushalima domin a hukunta su.
6 A he niki mba niwa mi zren ti weiweire ni Damascus, mla tsutsu irji, mle kikle kpan rji ni shulu a lu kri kpan kagon mu.
Sa'anda ina cikin tafiya, ina kuma kusa da Dimashku, da tsakar rana sai farat daya ga babban haske daga sama ya haskaka kewaye dani.
7 Mi kurjoku ni meme ndi wo ilan a tre ni me, 'Shawulu, Shawulu, nitu ngye wu si time ya?'
Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?'
8 Mi sa ndi, 'Wu nha, Bachi?' A hla mu ndi, 'Mi Yesu wu Nazaret, wa wu si tiwu ya.'
Na amsa, 'Wanene kai, Ubangiji?' Ya ce mani, 'Nine Yesu Banazarat wanda kake tsananta wa.'
9 Biwa bana heni me bato bwu kpan, ndana to tutre lan wa a tre nime na.
Wadanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su gane muryar wanda ya yi magana da ni ba.
10 Mi tre ndi, 'Mi ti ngye zizan Bachi?' Bachi a hla mu, lunde ni rhihi nimi Damascus. Niki wu wo kpe wa mi chuwu du wuti.
Na ce, 'Me zan yi ya Ubangiji?” Ubangiji ya ce mani, 'Tashi ka tafi cikin Dimashku, a can za a fada maka abinda wajibi ne ka yi.
11 Mina lani to bubuna nitu kpanlua, i indji wa ba he ni me'a ba vume zrenji ni wo ye nimi Damascus.
Ban iya ganin wuri ba domin walkiyar hasken, sai na tafi cikin Dimashku ta wurin jagorancin wadanda ke tare da ni.
12 Niki mi zontu ni indji ri wu nde Ananiyas, indji wu kri gbangban ni hu nkon du, mba wa Yahudawa ba pempe wa ba ki niki ba tre ndindi ni tuma.
A can na sami wani mai suna Ananiya, mai tsoron Allah bisa ga sharia, da kyakyawan suna kuma a gaban Yahudawa da ke zama a can.
13 A ye ni me, nda ye kri whi nime, nda tre ndi, 'Vayi Shawulu, kpa to bubu me.' Ni nton kima, mi towu.
Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi.
14 Wa a tre ndi, Irji wu ba titimbu a chu du wu to sron ma, du wu to Tsatsra wu Ma, mba ndi du wo ilan wa rju rju ni nyuma.
Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa.
15 Nitu wu ta bla nituma ni indji wawu, kpe wa wu to ni shishime mba ni woa.
Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji.
16 Zizan wu si gben ngye? lu kri, kpa batisma, ndi gla tre me hi, nisi yo ni ndema.
A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.'
17 Niwa mika kma ye ni Urushelima, nda sia bre ni mi hekali, a he niwa mi kpa to nimi ra.
Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi.
18 Mi ton sia hlamu, 'Sima ni lunde don Urushelima gbagbla, nitu bana kpa bla tre nitumu na.'
Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.'
19 Mi tre ndi, 'Bachi, baba kimba ba to ndi mi vu bi wa ba kpanyimea tro nda tsi ba ni sinagog kagon.
Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada.
20 Niwa ba ka iyi Istifanus wa ata bla nitu me hle, mi sia kri ni hugon, ndani kri ya nklon biwa ba wuu a.
A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.'
21 I a hlamu ndi, 'Hi, nitu mi ton hi gbagban mu ni bi kora'a.'”
Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.'
22 Ba srenton niwu ka tsra niwa a tre kima. Mle ba nzu gro kpa nda tre ndi, “njii bibi kima rhuni gbungblu meme, nitu a na bi du he ni sisren na.”
Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.'
23 Niwa ba sia kpa gro nda ju nklon mba ni the, nda ni vra iwru,
Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska,
24 kikle kaptin a duba nji Bulus rihi ni bubu wu mla ri. A nu nyu tre nda du ba shle myeu tre no tiwu ya, nitu du wawume du to ka a hi ngye duba ni kpagro nituma toki.
babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka.
25 Niwa ba loo ni rjirji ntan, Bulus a tre ni ninkon wu ndji ya bi lokpa deri ri, wa a kri nha niki, “A tsra ni du yi ti indji Roma ya biyi, hama ni yo ni tsra?
Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, “Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?”
26 Niwa Centurion a wo toki, a hi ni ninkon kaptin a nda ka hlawu ndi, “A hi ngye wu si son ti? Indji yi hi vren meme Roma.”
Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, “Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne.”
27 Kikle kaptin a ye tre niwu ndi, “Hlamu, wu vren meme Roma? Bulus a tre ndi, “Ee.”
Babban hafsa ya zo ya ce masa, “Gaya mani, kai dan asalin Roma ne?” Bulus ya ce, “Haka ne.”
28 Kikle kaptin a sa ndi, “Ana ni gbugbu nklen mba mi kpanyime son vren meme.”I Bulus a tre ndi, “Ba ngrji me vren me Roma.”
Babban hafsan ya amsa masa, “Da kudi masu yawa na sayi yancin zama dan kasa.” Amma Bulus ya ce, “An haife ni dan kasar Roma.
29 Niki indji wa bata hi shle miu trea ba kawu don hari. Kikle kaptin a ti sissri, niwa a wo ndi Bulus hi ndji meme Roma, nitu wa a vuu lo.
“Sai mutanen da sun zo su tuhume shi sun bar shi nan da nan. Babban hafsa shi ma ya tsorata da ya gane Bulus dan asalin Roma ne, domin ya riga ya daure shi.
30 Ni vi wa ahu kia, kikle kpatin a ta son to tukpe wa Yahudawa ba bahe niwu nitu Bulus. Niki a duba si chuwo ni lo nda du kikle Prist baba bi son nitra bi ninkon gbua kuson. Niki, ba nji Bulus grji ye zi ni mi mba.
Washegari, babban hafsan ya so ya san gaskiyar tuhuma da Yahudawa suke yi a kan Bulus. Sai ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu. Sai ya kawo Bulus ya sa shi a tsakiyarsu.