< Ndu Manzaniba 21 >
1 Niwa ki hi don ba ni vu zren hu nkon mma, ki hu tri me hi ni gbu Cos, e ni bi wa aka hua ni gbu Rhodes, mba rhini ki hi ni gbu patra.
Da muka rabu da su, muka shiga jirgin ruwa muka mike hanya zuwa birnin Kos, washegari sai birnin Rodusa, daga nan sai kuma zuwa birnin Batara.
2 Niwa ki to jirgima wa a ta ru hini Funisiya, ki ri huba dran hi.
Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa Fonisiya sai muka shiga.
3 Hu wa ki nzu shishi to Cyprus, ki kawdon ni wo mrha wu kpran jirgia, ki dran hi ni Syria, ndi ka kukri ni Tyre, bubu wa kikle jirgi a ta ju kpi wa anjia.
Da muka hango tsibirin Kubrus muka bar shi a hagun mu muka nufi Suriya, muka sauka a birnin Taya domin a nan ne jirgin ruwan zai sauke kayansa.
4 Hu wa ki to mri ko bihuba, ki kii ni ki wu vi tangban. Hu kpere sron brji, basi yo tre ni Bulus du na hi Urushelima na.
Bayan mun sami almajirai sai muka zauna can kwana bakwai. Al'majiran suka ce ma Bulus, ta wurin Ruhu, kada ma ya je Urushalima.
5 Niwa ivimbu niki a kle, ki donba ni kunkon mbu, i wawumbu, baba mbamba ni mri mba ba huta zren rjuni gbu'a. Niki ki kukwu ngbarju ni nyu kpe tre ma'a ni bre Irji,
Bayan 'yan kwanaki muka cigaba da tafiyarmu. Dukansu da matansu da 'ya'yansu suka raka mu har bayan birnin. Sa'annan muka durkusa a bakin gacci muka yi addu'a muka yi sallama da juna.
6 ni tre ndi se vi ri niki ki rini jirgi'a, i ba kma hi komba.
Sai muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gida.
7 Niwa ki kle zren mbu rji ni Tyre, ki ye ni Ptolemais. Niki chi mri vayi ba ni son niba wu vi ri.
Da muka gama tafiyarmu a Taya muka iso Talamayas. A nan ne muka gaisa da 'yan'uwa, muka zamna kwana daya da su.
8 Nivi wa a hu kima ki hi ni Kaisariya. Ki ri ni ko Filibus, ndji wu zren ni bla tre Irji, wa ana iri nimi tangban ba, ndi ka son niwu.
Washegari muka tashi muka tafi Kaisariya. Muka shiga gidan Filibus mai shaida bishara, daya daga cikin bakwai din, muka zauna da shi.
9 Inji yi a he ni mri mba nza wa bana to lilon na, i bata nran kpi bi ye ni ko shishi.
Wannan mutum yana da 'ya'ya hudu mata, budurwai masu yin annabci.
10 Niwa ki kii niki wu vi fon bran, indji ri wa ri to koshishi, ni nde Agabus, grji ye rhi ni Judiya.
Sa'anda muka zauna can 'yan kwanaki, wani annabi ya zo daga Yahudiya mai suna Agabus.
11 A ye nita nda ban rjirji trii Bulus. Niki a lo za mba woma ni rjirji trii'a nda tre ndi, “Ikpe wa Brji Tsatsra ni tre'a, toki Yahudawa bi Urushelima ba lo indji wu rjirji trii yi, i ba vuu yo ni wo Bikora.”
Ya zo wurinmu ya dauki damarar Bulus ya daure tasa kafar da hannayensa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, 'Haka Yahudawa za su daure mai wannan damarar, zasu kuma bashe shi ga al'ummai.'”
12 Niwa ki wo kpi biyi, kita baba indji wa ba ki ni ki, ki krubre Bulus ni du na hi ni Urushelima na.
Da muka ji wannan sakon, sai dukanmu da mazaunan wurin muka roki Bulus kada ya tafi Urushalima.
13 Niki Bulus a sa bawu ndi, “Bisi ti ngye, kpa gro nini yra me sron? Mi kpanyime ndi du ba na lo me negen na, mba du me kwu ngame ni Urushelima nitu nde Bachi Yesu.”
Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me kuke yi, kuna kuka kuna karya mani zuciya? Bama a shirye don dauri kadai nake ba har ma da mutuwa a Urushalima, sabili da sunan Ubangiji Yesu.”
14 Nitu wa Bulus na kma sron ni bre mba na, ki son ngbangbi ni lu tre ndi, “Du kpe wa Irji kpanyime niwu du he toki.”
Tun da Bulus bashi da niyyar a rinjaye shi, muka daina kuka muka ce, “Bari nufin Ubangiji ya tabbata.”
15 Hu vi biyi, ki vu ba mbu zren mbu ni hi ni Urushelima.
Bayan wadannan kwanaki, muka dauki jakkunanmu muka haura Urushalima.
16 Mri ko bi hu bari wa ba rhini Kasariya ba huta ngame. Ba nji indji ri wu nde Mnason, indji wu Cyprus, nha ni kpamba, wa ana he ni mi bi mri ko bi hu, wa ki hi ki niwu.
Wadansu almjirai daga Kaisariya suka bi mu. Sun zo ne tare da wani ana ce da shi Manason, mutumin Kuburus mai bi na farko, wanda za mu zauna da shi.
17 Niwa ki ye ri ni Urushelima, mri vayi ba ba kpata ni wo ha ni ngyiri.
Da muka isa Urushalima, 'yan'uwa suka marabce mu da farin ciki.
18 Nivi wa a ka hu ki, Bulus a njita hi ni ko Yakubu, i bi chiche ba bana he niki.
Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Bitrus, dukan dattawa kuma suna nan.
19 Niwa a chi ba, a vu bla ni yiyri kpi wa Irji a ti nimi Bikora ni nkon ndu wa a ti'a.
Bayan ya gaishe su, sai ya shaida masu daya bayan daya abubuwan da Allah ya yi cikin al'ummai ta wurin hidimarsa.
20 Niwa bawo kima ba gbre san ni Irji, nda hlawu ndi, “Wu to, vayi, ka indji dubu bren ni mi Yahudawa ba ba kpanyime. Ba yo sron kri gbangban ndi ba hu du a.
Da suka ji haka, suka yabi Ubangiji suka ce masa, “Ka gani, dan'uwa, dubban Yahudawa sun bada gaskiya suna kuma da niyyar kiyaye shari'a.
21 Ba hla bawu nitu me, ndi wu tsro Yahudawa wa baki nimi Bikora'a du ba ka Musa don, mba ndi wu hla bawu dubu na yoyi ni mri mba, mba du bana zren nitu nkon ba tii na.
An kuma gaya masu a kanka cewa, kana koya wa Yahudawan da suke zaune cikin al'ummai su yi watsi da Musa. Kana koya masu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, kada kuma su bi tsofaffin al'adu.
22 Ki ti ni he? Njanji ba wo ndi wu ye.
Me ya kamata mu yi? Hakika za su ji ka zo.
23 Nitu ki, wuka ti kpe wa ki hla niwu. Ki he ni indji nza wa ba chu nyu.
Sabo da haka ka yi abin da muka fada maka yanzu. Muna da maza hudu da suka dauki wa'adi.
24 Vuu indji ba ni ngla kpame niba, ni han nklen ni tumba, ni du ba kron nfutu mba. Ko nha ni to ndi kpe wa ba bla nitu me a hi che. Ba to ndi iwu ngame wu son tsra, nini hu du'a.
Tafi da wadannan ka tsarkake kanka tare da su, ka dauki dukan dawainiyar su dana askin kai. Ta haka kowanne mutum zai sani abubuwan da ake fadi a kanka karya ne. Za su sani cewa kai mai kiyaye shari'a ne.
25 I nitu Bikora wa ba kpanyime'a, ki nha nitu krimbu ndi duba chu kpamba ti nkan ni kpi wa ba ton ni kpi bi brji, ni iyi, ni kpe ba wuu ni nkon nduto, mba ni ti fa'a.”
Game da al'umman da suka bada gaskiya mun yi masu wasika, mun bada umarni su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci.
26 Niki Bulus a vuu indji ba, i ni vi wa aka hu'a, a ngla kpama bi ni babaa. Niki ba ri hi ni mi hekali, yo tre ni zi ndi vi wu nglakpa ani ye he toki, i ba nu beko nitu yiyri mba.
Sai Bulus ya dauki mazannan, washegari ya tsarkake kansa tare da su, suka shiga haikali, domin ya sanar da cikar ranakun tsarkakewarsu, wato ranar ba da sadaka domin kowanne dayansu.
27 Niwa vi tangban ba ba ye kle, Yahudawa bari rhini Asiya, ni ku shishi ni bulus ni mi hekalia, chon kpaandji ba nfu, nda yo wo nitu ma.
Da kwanakin nan bakwai suka yi gab da cika, wadansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a haikali, sai suka zuga taro, suka danke shi.
28 Ba sia kpa gro ndi, “Indji bi Israila, zo ta. Indji yi yi ni tsro ndji wawu kagon, kpi wa ahi nkan ni kri mba, ni dua, mba ni bubu yi. Hama kima me, a nji indji bi Greek bari ye ni mi hekali nda kpa bubu tsatsra yi ti meme.”
Suna ta kururuwa, “Mutanen Isra'ila ku taimaka mana. Wannan shine mutumin da ke koya wa dukan mutane ko'ina abubuwa gaba da mutane, da shari'a da kuma wannan wurin. Banda haka ya kawo Helenawa cikin haikalin nan ya kazantar da wannan wuri tsatsarka.”
29 Nitu bana to Trofimus, gu wu Afisus niwu nimi gbua, nda yo ndi Bulus a nji ba ri ni mi hekali.
Domin dama sun ga Tarofimas mutumin Afisa tare da Bulus cikin birni, suka yi zaton ya kawo shi cikin haikali.
30 Igbu'a wawu a chu nzan, i indji ba ba yo tsu ka vu Bulus. Ba gbiwu rju ni hekalia, nda kaa nkon ba gbagbla.
Sai duk gari ya rude, mutane suka runtuma suka danke Bulus. Suka ja shi waje daga cikin haikalin, nan da nan aka rufe kofofin.
31 Niwa ba ta son wuu, tu tre a ye ri ni ton kapti wu bi gben ndji Urushelima wawu ni kri gro tsishishi.
Suna kokarin kashe shi kenan, sai labari ya kai wurin hafsan sojoji cewa Urushalima duk ta yamutse da tarzoma.
32 Niki a tsi kri vu bi lokpa baba bi ya ndji deri ri, nda tsutsu grji nimi jbu indji ba. Niwa indji ba ba to ninkon kaptin mba bi lokpa ba, ba donme ni tsi Bulus.
Nan take ya dauki mayaka da jarumawa, suka sheka da gudu wurin taron. Da mutane suka ga hafsan sojoji da rundunansa sai suka daina dukan Bulus.
33 Niki ninkon kapti a zren hi ka vu Bulus, nda mmha yo ndi du ba lowu ni sraka ha. Niki a mye ka a hi nha mba a hi ngye wa a tia.
Sai hafsan ya tafi ya danke Bulus ya sa aka daure shi da sarkoki biyu. Ya tambaya ko shi wanene da kuma laifinsa.
34 Bari nimi jbu indji ba ba kpagro kperi i bari kpe nkan. Niwa kaptia ana mla to tu tre'a na, nitu hanton mba, a yo ba du ba nji Bulus hi ni bubu wa ba mla ziri.
Wadansu cikin taron suna ta kururuwa wadansu su ce wannan, wadansu su ce, wancan. Tunda hafsan bai fahimci abin da suke fadi ba, sabo da ihunsu, ya dokaci a shigar da Bulus farfajiyar sojoji.
35 Niwa a zren ye ni bubu ban za grji'a, bi lokpa a ba banwu nitu nfu jbu indji ba.
Da suka kai matakala, sojoji suka dauki Bulus sabo da tsananin husatar taron jama'a.
36 Nitu jbu indji ba ba sia huba nda ni kpagro ndi, “Niwu hi.”
Domin taron suka biyo baya suna ihu suna cewa, “A kashe shi.”
37 Niwa bataa nji Bulus ye ni bubu wu mlazia, a tre ni ninkon kaptia, ndi “Wu kpanyime ni du mi hla kpe niwu?” Kaptia a tre ndi, “Wu tre lan Greek?
An kusa shigar da shi farfajiyan kenan sai Bulus ya ce wa babban hafsan, “Ko ka yarda inyi magana da kai?” Hafsan ya ce, “Ka iya Helenanci?
38 Ana wuyi igu masra wa alu kpagbu tsi nda gbron indji dubu nza u bi wuundi rju hi ni miji'a na?”
Ashe ba kai ne Bamasaren nan da kwanakin baya ka haddasa tawaye, ka dauki 'yan ta'adda dubu hudu ka kai su jeji ba?”
39 Bulus a tre ndi, Mi ndi Yahudawa, rji ni gbu Tarsus ni Cilicia. Mina vren meme wu gbu wa a hi fii me na. Mi bre, du me tre ni indji ba.
Bulus ya ce, “Ni Ba'ibrane ne daga birnin Tarsus a Kilikiya. Ni dan kasar babban birni ne. Ka amince mani in yi magana da mutanen.”
40 Niwa kaptin a nu kpanyime'a, Bulus a lu kri ni bubu ban zaa nda ti wo ni indji ba. Niwa bubua a ti gbi me, a tre niba ni lan Ibraniyawa ba. A tre nde,
Da hafsan ya bashi izni, Bulus ya mike a kan matakala ya daga hannayensa sama ya yi nuni su yi shuru. Da wuri ya yi tsit, Bulus ya yi masu magana da Ibraniyanci. Ya ce,