< 2 Pita 3 >
1 ziza me hhan vuvue ni yi wu be suhmu i wayi a hi hhan vuvumu u hari me soh ti yi kade chu yi ni immere u njaaji du yi ka de che yi ni immere u njaaji
Yanzu, ina rubata maku, kaunatattu, wannan wasika ta biyu domin in tunashe ku, in kuma zuga tunaninku na gaskiya,
2 du yi tika illan tere annabawa tsratsra wa bs hla ni bau ni mummla ni kpakyeme irji bu ni wa kpeta chuwo ni tu mazanibua
don ku tuna da kalmomin da annabawa tsarkaka suka fada a da, kuma da umurnin Ubangijinmu da mai ceto da aka bayar ta wurin manzaninku.
3 be itoh ni mummla mba hla de bi zah di mba ye ni toh u kaikle mba ta zayi nda kakpi u sonkpa mba yo koshi shi mba
Ku san wannan da farko, cewa masu ba'a za su zo a kwanakin karshe. Za su yi ba'a kuma su ci gaba bisa ga sha'awowinsu.
4 mba tere kwmaye ma ahe tse wa mba tere a ni kwmye? ni toh wa mba tibu be sisemu mba qhu ikpiomba he wawu na u mummla na wa mbati mba
Za su ce, “Ina alkawarin dawowarsa? Tun lokacin da kakaninmu suka mutu, dukkan abubuwa sun kasance yadda suke, tun farkon halitta.”
5 ni nayeh mba tere mba kparisu de shulu ni meme mba na he ni mima tu ni sisemu ni kpa kyeme u irji
Da gangan suka manta cewa sama da kasa sun kasance daga ruwa, kuma ta wurin ruwa, da dadewa ta wurin umarnin Allah,
6 ni toh khima ikpi be gbugblu mba kaba su ni gbugbu ima u tsufana
kuma cewa ta wurin wadannan abubuwa duniyar wancan zamani ta halaka, da ambaliyar ruwan tsufana.
7 ni meme u ziz a ti mba zi si gbi ilu ni kpakyeme khi ma mba ti baki ni gbe ivi u bla tre ni ni kasu ni be wa bana hhu iko na
Amma sama da kasa na yanzu, an tanada su domin wuta ta wurin wannan umarnin. An tanada su domin ranar shari'a da halakar marassa ibada.
8 na kparisu wayi na be sonmu ivi iri ni trji a he na ise dubd ni irji isei dubu a he na ivi riri mba he naki
Kada ku manta da wanan, kaunatattu, cewa rana daya a gun Allah kamar shekaru dubu ne, kuma shekaru dubu kamar rana daya suke.
9 irji na kaci ni yo nyun ma na wa beri mba mba ya kaci ni tu kima ani vu sonro ni yi ana sondu ko riri bi du kasuna ani yi toh du yiye kpa ti njaaji.
Ubangiji baya jinkiri game da alkawaransa kamar yadda wadansu ke ganin jinkiri. Maimakon haka, yana hakuri da ku. Ba ya so ko dayanku ya hallaka, amma kowanenku ya kai ga tuba.
10 na ki ivi u ye irji ani ye na idi u yibi ishulu ni kasu ni gudjur u gbagba ilu ni gon ikpi u gbugblu wa mba he ni mima mba djur ni rah
Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar barawo. Sammai za su shude da kara mai karfi. Wuta zata kone komai da komai, kuma duniya da dukkan ayyukan da ke cikinta zasu bayyanu.
11 tu de ikpi beyi mba kasu na ki bebe idi mba ki a mla de khi he naki? amka de khi sonson u tsara tsran hwu.
Da shike dukkan wadanan abubuwa za a hallaka su haka, wadanne irin mutane yakamata ku zama? Ya kamata kuyi rayuwar tsarki da ta ibada.
12 son ni yo isorobi de irji a ni ye gbagbla ni vikima mba kaa shulussu ni ilu naki koge ni koge i shan ni huu lu u varvara me
Ku zauna cikin bege da kuma hanzarta zuwan ranar Allah. A ranan nan, za a hallaka sammai da wuta, kuma dukkan komai da komai zai narke cikin zafi mai tsanani.
13 naki ni tu yo nyuma khi gbi shulu isama ni gbublu isama wa didimani he ni mima
Amma bisa ga alkawarinsa, muna jiran sabuwar sama da sabuwar duniya, inda adalci zai kasance.
14 nakima be sonmu tude be yo sonro ni kpi beyi be ti ni gbegble be du mba na toye ni tsi chudu ni dhi na ko ni kpi meme ma na ni koshshi mai du mba toyi ni mi si sonro
Saboda haka, kaunatattu, tun da kuna da begen wadannan abubuwa, ku yi iyakacin kokarinku a same ku marassa tabo da marasa aibu a gabansa, cikin salama.
15 na ki be ka vu sonro irji a he u kpachu yi na wa Bulus isironro vayi bu a hanatawu ni toh ma wa mba noa
Kuma, ku dauki hakurin Ubangiji domin ceto ne, kamar yadda kaunataccen danuwanmu Bulus ya rubuta maku bisa ga hikima da aka ba shi.
16 Bulus a tere ni tu kpi beki wawu wa mba he ni mi han vuvumaa ni muma ikpi bari mba he ni ya toh be wa mba na toh kpi ana ni idi be wa mbana son kpieme na ba kwma tere siran na ki nda guru bsri yo niko mba du mbawuu kpamba.
Bulus yayi magana akan wadanan abubuwa cikin dukkan wasikunsa, a ciki akwai abubuwa da suke da wuyar ganewa. Jahilai da mutane marassa natsuwa sukan juya ma'anarsu, kamar yadda suke yi wa sauran nassoshi, don hallakar kansu.
17 na ki be sonmu be rigga de toh ikpi be yiyei be ka ya kpabi na duba guru yi na ni guru u idi be wa mbana huu dika hre de na toh kpakyeme ini mi bi na
Saboda haka, kaunatattu, tun da kun san wadannan abubuwa, ku kula da kanku kada a badda ku ta wurin rudun mutanen da ba su bin doka, har ku rasa amincinku.
18 e u be ka gburon ni mi dede ni toh irji mba yesu Almasihu wa a kpata chuwo du gbira san du he ni tuma zizi nikaseisei anakima. (aiōn )
Amma ku yi girma a cikin alheri da sanin Ubangijinmu da mai ceto Yesu Almasihu. Bari daukaka ta tabbata a gare shi yanzu da har abada. Amin. (aiōn )