< 1 John 2 >

1 bi be yo lomi ma mulang kume woti kati yilo ko ma bwiranka benno kange ma bwiranka ri, bon wi nii fiye te wiyeu, co Yeecu Almacuhu nii be, kebe cakcaen.
'Ya'yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci.
2 co ni fanko mur bwiranka be, kebe kabe ki kwace, la kange dor bitine roce gwam.
Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka.
3 la nyeu co ma nyumom la bon nyumomco na bo bwang ten werfuner cerori.
Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa.
4 nii wo ki con “nyumom kwama,” la bwangten bo werfuner cereri nii cwerke bilenkero mani wercer.
Duk wanda yace, “Na san Allah” amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa.
5 la nii wo bwanten kercereri, bi com cwika kwama ko dii ti nii wo nin la nyo bo nyumom biki no more ce,
Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa.
6 na nii wo ki co ki no mor kwamari, tam ca yam bo wo Yeecu Almacifu yau.
Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi.
7 nubo ma cwi- cwiyeu kebo werfunero fwir ma mulan kumentiye, lan co werfundo carko ka nuwam ki kabau.
Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko.
8 na weu maki mulangkumen werfundo fwir, wom bilen nere mor Almacihu ti cuyi, filanko ti,
Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa.
9 nii wo ki co ki no mor filangeu na ko kece tiye, ki no mor kumtacili duwal
Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan'uwansa, yana cikin duhu har yanzu.
10 wo na cwi ke ce tiyeri, ki no mor filange, dike a dor kottanka tiyeu mani cinen
kuma wanda yake kaunar dan'uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa.
11 na wo ko kece tiyeri ki no mor kumtacili yila ki ya kumtacili, nyombo fiye co yom doreu, wori kumtacili fikanum mwe ceu
Amma duk wanda yake kin dan'uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi.
12 ma mulan kumen wo kom bi beyo lomi ma cwi-cwiyeu wo ni cin cutam kumen bwiran ke kume wi ker denece.
Na rubuta maku, ya ku kaunatun 'ya'yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa.
13 man mulang kumen tebbo, wori kom nyumom co, wuro wi tun ki kabau. man mulang kumen kom bi bei bayolobeu wori kom wi kibi kwan la ker kwamaro yimwi more kume, wokom cam turani kange bwerko. man mulan kumen bi be yo, wori kom nyumom teeu.
Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban.
14 man mulan kumen tebbo, wori kom nyumom co won wi fiya ki kabau, man mulang kumen bi bei ba yilo bei wori kom wi kibi kwan la ker kwamaro yim more kume, la kom cam turani ki bwirko
Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun.
15 ko cwire kalewo, kaka dike mor kalewo, no na kange cwi kale wori cwika teeka mani more ce.
Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa.
16 wori dikero gwam fo dor bitinereu, kuru bwiye, dike nuwe dilan tiyeu, kange yim kangka doreko bwir, kebe wo teece na dorbitinero ti cui kange dilanka ceko
Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha'wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne.
17 dor bitinero ti cui kange dilanka ceko na nii ma dike kwama cwitiyeu con nowi kwatti diri (aiōn g165)
Duniya tana wucewa tare da sha'awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada. (aiōn g165)
18 bi beyo bi dutinum, kaleu kwemum na wo ka nuwa nii kiye Almacifu wi bou ti la wo nyeu nob kiyeu nob kiyeb Almacifu kila kwerin biye ken la nyeu co nyo nyumom ciko nyoki kaleu kwenume.
Yara kanana, sa'a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa'a ta karshe ce.
19 ci cer bore be, kwati yeu na ci kebo na be, la ci na ci be ri na citin ca kaba kange bo, la na wo cin cerumeu, won nungi ci kebo more be
Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane.
20 la kumeu kon yom cor ka mwengek yuwa tang be kwama ko nin, la gwam kume kom nyumom bilenke,
Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya.
21 ma mulang kumem bo miki ka nyom bo bilenker wori kom nyumom la kange cwerke cerubo wibilenkenin
Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya.
22 we nii cwerkeu, co nii yi Yeecu kebo kiritti nii wo co nii kiye Almacifu. wori co ciya tee co ciya bo bweceu
Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan.
23 kange nii mani wo ciya bo bwere, wite tee nii wo ciya ki bweri wi ki teu
Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma.
24 la kange komtak, iako dobti dike ka nuwa ki kabau ayi more kume, na dike ka nuwa ki kaban yikam more kumeri, kom kenen kan yi mor”bwe nin kange mor teeu”
A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban.
25 noro co nebeu dume diiriyeu, (aiōnios g166)
Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada. (aiōnios g166)
26 ma mulngkumen kom nure.
Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku.
27 wo kumeu, corka nuwangekowuro ka yo cineneu wi more kume, ka do kange nii bou na meram kumen. la na cor ka mwangeko ka yo cineneu kurang kumen dikero gwam la bilenker, cwerke mani wi more ci
Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa.
28 na weu bi be yo lomi ma cwi-cwiyeu, ko no wi more ce kambo ca cer kangu tiyeri bou mana yilam ki yonenri, kebo ki kwen, duwe, kalum cem, ca bou tiyeu.
Yanzu fa, 'ya'ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa'adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa'adda zai zo.
29 na kom nyumom co cak-cakri, kom nyumom nuwa wo yin yim bo cak-cake tiyeu, cin bom bowe cinen.
Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.

< 1 John 2 >