< لاويّين 19 >
وَقَالَ الرَّبُّ لِمُوسَى: | ١ 1 |
Ubangiji ya ce wa Musa,
«قُلْ لِبَنِي إِسْرَائِيلَ: كُونُوا قِدِّيسِينَ لأَنِّي أَنَا الرَّبَّ إِلَهَكُمْ قُدُّوسٌ. | ٢ 2 |
“Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.
لِيُوَقِّرْ كُلُّ إِنْسَانٍ أُمَّهُ وَأَبَاهُ، وَرَاعُوا سُبُوتِي. فَأَنَا الرَّبُّ إِلَهُكُمْ. | ٣ 3 |
“‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
وَلا تَتَحَوَّلُوا لِعِبَادَةِ الأَوْثَانِ، وَلا تَصُوغُوا لأَنْفُسِكُمْ آلِهَةً مَسْبُوكَةً، فَأَنَا الرَّبُّ إِلَهُكُمْ. | ٤ 4 |
“‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.
وَمَتَى ذَبَحْتُمْ ذَبِيحَةَ سَلامٍ لِلرَّبِّ فَلْتَكُنْ ذَبِيحَةَ رِضًى. | ٥ 5 |
“‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku.
تَأْكُلُونَهَا فِي الْيَوْمِ الأَوَّلِ وَالثَّانِي مِنْ تَقْرِيبِهَا، وَفِي الْيَوْمِ الثَّالِثِ تُحْرِقُونَ مَا تَبَقَّى مِنْهَا بِالنَّارِ. | ٦ 6 |
Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi.
أَمَّا الأَكْلُ مِنْهَا فِي الْيَوْمِ الثَّالِثِ فَذَلِكَ نَجَاسَةٌ مُنْكَرَةٌ. | ٧ 7 |
In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba.
وَالآكِلُ مِنْهَا يُعَاقَبُ بِذَنْبِهِ لأَنَّهُ قَدْ دَنَّسَ قُدْسَ الرَّبِّ فَتُسْتَأْصَلُ تِلْكَ النَّفْسُ مِنْ بَيْنِ شَعْبِهَا. | ٨ 8 |
Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa.
وَعِنْدَمَا تَحْصُدُ مَحْصُولَ حَقْلِكَ لَا تَحْصُدْ زَوَايَاهُ وَلا تَلْتَقِطْ مَا يَتَنَاثَرُ مِنْ حَصِيدِكَ. | ٩ 9 |
“‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.
لَا تَرْجِعْ لِتَجْمَعَ بَقَايَا عَنَاقِيدِ كَرْمِكَ، وَلا تَلْتَقِطْ مَا يَنْفَرِطُ مِنْهَا، بَلِ اتْرُكْهُ لِلْمِسْكِينِ وَلِعَابِرِي السَّبِيلِ، فَأَنَا الرَّبُّ إِلَهُكُمْ. | ١٠ 10 |
Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
لَا تَسْرِقْ، وَلا تَكْذِبْ، وَلا تَغْدُرْ بِصَاحِبِكَ، | ١١ 11 |
“‘Kada ku yi sata. “‘Kada ku yi ƙarya. “‘Kada ku ruɗe juna.
لَا تَحْلِفْ بِاسْمِي كَاذِباً، فَتُدَنِّسَ اسْمَ إِلَهِكَ. فَأَنَا الرَّبُّ. | ١٢ 12 |
“‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.
لَا تَظْلِمْ قَرِيبَكَ، وَلا تَسْلُبْ وَلا تُرْجِئْ دَفْعَ أُجْرَةِ أَجِيرِكَ إِلَى الْغَدِ. | ١٣ 13 |
“‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.
لَا تَشْتُمِ الأَصَمَّ، وَلا تَضَعْ عَثْرَةً فِي طَرِيقِ الأَعْمَى، بَلِ اتَّقِ إِلَهَكَ. فَأَنَا الرَّبُّ. | ١٤ 14 |
“‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
لَا تَظْلِمُوا فِي الْقَضَاءِ، وَلا تَتَحَيَّزُوا لِمِسْكِينٍ وَلا تُحَابُوا عَظِيماً. احْكُمْ لِقَرِيبِكَ بِالْعَدْلِ. | ١٥ 15 |
“‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
لَا تَسْعَ فِي الْوِشَايَةِ بَيْنَ شَعْبِكَ، وَلا تَرْتَكِبْ مَا يُعَرِّضُ حَيَاةَ جَارِكَ لِلْخَطَرِ، فَأَنَا الرَّبُّ. | ١٦ 16 |
“‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.
لَا تُبْغِضْ أَخَاكَ فِي قَلْبِكَ، بَلْ إِنْذَاراً تُنْذِرُهُ لِئَلّا تَكُونَ شَرِيكاً فِي ذَنْبِهِ. | ١٧ 17 |
“‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
لَا تَنْتَقِمْ وَلا تَحْقِدْ عَلَى أَحَدِ أَبْنَاءِ شَعْبِكَ، وَلَكِنْ تُحِبُّ قَرِيبَكَ كَمَا تُحِبُّ نَفْسَكَ، فَأَنَا الرَّبُّ. | ١٨ 18 |
“‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
أَطِيعُوا شَرَائِعِي. لَا تُزَاوِجْ بَهَائِمَكَ مِنْ جِنْسَيْنِ، وَلا تَزْرَعْ حَقْلَكَ مِنْ صِنْفَيْنِ، وَلا تَلْبَسْ ثَوْباً مَنْسُوجاً مِنْ مَادَّتَيْنِ مُخْتَلِفَتَيْنِ. | ١٩ 19 |
“‘Ku kiyaye farillaina. “‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
إِنْ عَاشَرَ رَجُلٌ أَمَةً مَخْطُوبَةً لِرَجُلٍ آخَرَ، وَلَمْ تَكُنْ قَدِ افْتُدِيَتْ أَوْ أُعْتِقَتْ فَلْيُؤَدَّبَا، وَلا يُقْتَلا، لأَنَّهَا لَمْ تَكُنْ مَعْتُوقَةً. | ٢٠ 20 |
“‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a’yantar da ita ba.
وَلْيَأْتِ الرَّجُلُ بِكَبْشٍ إِلَى الرَّبِّ ذَبِيحَةَ إِثْمٍ عِنْدَ مَدْخَلِ خَيْمَةِ الاجْتِمَاعِ، | ٢١ 21 |
Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji.
فَيُكَفِّرُ عَنْهُ الْكَاهِنُ بِكَبْشِ الإِثْمِ أَمَامَ الرَّبِّ مِنْ أَجْلِ خَطِيئَتِهِ الَّتِي ارْتَكَبَهَا، فَيَغْفِرُ لَهُ الرَّبُّ خَطِيئَتَهُ. | ٢٢ 22 |
Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa.
وَمَتَى دَخَلْتُمْ دِيَارَ كَنْعَانَ، وَغَرَسْتُمْ أَشْجَاراً ذَاتَ أَثْمَارٍ تُؤْكَلُ فَاحْسِبُوا مَحْصُولَ سَنَوَاتِهَا الثَّلاثِ الأُولَى مُحَرَّماً، وَتَكُونُ مَحْظُورَةً عَلَيْكُمْ فَلا تَأْكُلُوا مِنْهَا، | ٢٣ 23 |
“‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai’ya’ya na ci, ku ɗauki’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba.
أَمَّا ثَمَرُ السَّنَةِ الرَّابِعَةِ فَيَكُونُ كُلُّهُ مُخَصَّصاً لِتَمْجِيدِ الرَّبِّ، | ٢٤ 24 |
A shekara ta huɗu, dukan’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji.
وَفِي السَّنَةِ الْخَامِسَةِ تَأْكُلُونَ مِنْ ثَمَرِهَا، لِتَزْدَادَ لَكُمْ غَلَّتُهَا، فَأَنَا الرَّبُّ إِلَهُكُمْ. | ٢٥ 25 |
Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
لَا تَأْكُلُوا لَحْماً بِدَمِهِ، وَلا تُمَارِسُوا الْعِرَافَةَ وَالْعِيَافَةَ. | ٢٦ 26 |
“‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “‘Kada ku yi duba ko sihiri.
لَا تَحْلِقُوا رُؤُوسَكُمْ حَلْقاً مُسْتَدِيراً، وَلا تُقَلِّمْ جَانِبَيْ لِحْيَتِكَ. | ٢٧ 27 |
“‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.
لَا تَجْرَحُوا أَجْسَامَكُمْ حُزْناً عَلَى مَيْتٍ، وَلا تَرْسِمْ وَشْماً عَلَيْهِ. فَأَنَا الرَّبُّ. | ٢٨ 28 |
“‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.
لَا تُدَنِّسِ ابْنَتَكَ فَتَبْذُلَهَا لِلْفُجُورِ، لِئَلّا تَزْنِيَ الأَرْضُ وَتَمْتَلِئَ بِالرَّذِيلَةِ. | ٢٩ 29 |
“‘Kada ka ƙasƙantar da’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
رَاعُوا شَرَائِعَ سُبُوتِي، وَأَجِلُّوا مَقْدِسِي، فَأَنَا الرَّبُّ. | ٣٠ 30 |
“‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji.
لَا تَضِلُّوا وَرَاءَ مُسْتَحْضِرِي الأَرْوَاحِ، وَلا تَطْلُبُوا التَّوَابِعَ، فَتَتَنَجَّسُوا بِهِمْ. فَأَنَا الرَّبُّ. | ٣١ 31 |
“‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
قِفْ فِي حَضْرَةِ كِبَارِ السِّنِّ، وَوَقِّرِ الشُّيُوخَ، وَاتَّقِ إِلَهَكَ، فَأَنَا الرَّبُّ. | ٣٢ 32 |
“‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.
إِذَا أَقَامَ فِي أَرْضِكُمْ غَرِيبٌ فَلا تَظْلِمُوهُ، | ٣٣ 33 |
“‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi.
وَلْيَكُنْ لَكُمُ الْغَرِيبُ الْمُقِيمُ عِنْدَكُمْ كَالْمُوَاطِنِ. تُحِبُّهُ كَمَا تُحِبُّ نَفْسَكَ، لأَنَّكُمْ كُنْتُمْ غُرَبَاءَ فِي أَرْضِ مِصْرَ. فَأَنَا الرَّبُّ. | ٣٤ 34 |
Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
لَا تَجُورُوا فِي الْقَضَاءِ، وَلا تَغُشُّوا فِي الْقِيَاسِ أَوِ الْوَزْنِ أَوِ الْكَيْلِ، | ٣٥ 35 |
“‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu.
بَلِ اسْتَخْدِمُوا مَوَازِينَ عَادِلَةً وَعِيَارَاتٍ عَادِلَةً وَمَكَايِيلَ عَادِلَةً، فَأَنَا الرَّبُّ إِلَهُكُمُ الَّذِي أَخْرَجَكُمْ مِنْ دِيَارِ مِصْرَ. | ٣٦ 36 |
Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
فَاحْفَظُوا جَمِيعَ فَرَائِضِي وَأَحْكَامِي وَاعْمَلُوا بِها، فَأَنَا الرَّبُّ». | ٣٧ 37 |
“‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’”