< Luka 13 >

1 Kubi kone among anit bellinghe kitene na Galiliyawa, alenge na Bilatus wa munu nmyi mine, kitin ngutunu nmyi.
A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya gauraye jininsu tare da jinin hadayunsu.
2 Yesu kauwa aworo nani, “Ulin kpilizu nafo a Galitiyawa ale katin kagizine nin kulapi, nara idin niu nlo libau we?
Yesu ya amsa ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala?
3 Na nani ba, meng nbelling munu, asa na anung su udiu kutyin ba vat mine iba nanu nloli libauwe lineme.
Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.
4 Sa anit likure nin kulir nanyan Nsiliyom, ale na kisoro wa diu ki molo nani, idin kpilizu nafo inung wa din kulapi ikatina vat nanit Urshalima?
Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5 Na nani ba, meng bellin munu, asa na anung su udiu katyin ba vat mine ba nanu tutun.”
Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”
6 Yesu belle nani tinan tigoldo, “Umang wa bilisu kupau nanya kunen me, ada pizira kumate na ase ba.
Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi’ya’ya ba.
7 Unite belle unan ncaa kunene, 'Yene akus atatari ale asa nda nnan da se kumat kutca kone, na nse imonku ba, werne kunin, bara iyang ku wa nanza kunene?'
Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman’ya’yan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’
8 Unan ncaa kunene kauwa aworo, 'Suna kunin nlo likuse, mang ba wuzu kuwu, in tighe utanki.
“Mutumin ya amsa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka bar shi, in yi masa banƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya.
9 Asa natah kumat likus ndake, ucaun, asa na ana ba, uwerne kunin!'”
In kuwa ya ba da’ya’ya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’”
10 Nene Yesu wadin ndursuzuwe nanya kutyin nlirag namon Asabbath,
Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a,
11 umon uwani wa duku kikane, wenge na adimun nakus likure nin kulir, uruhu unazang, nkuzu kidowo wa seghe, aso kangarang awasa ayisina dert ba.
a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan.
12 Kubi na Yesu nyene ghe, ayicila ghe aworo, “Shino nin nkuzu kidowo fe.”
Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an’yantar da ke daga rashin lafiyarki.”
13 A tarda ucara me kitene me, dedei ayisina dert, azazina Kutelle.
Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
14 Inung ago nanya kutyin nlirag, lanza ayi, bara Yesu nnaghe ushinu liyiru nasabar. Ago we kauwa, iworo ligoze, “Ayiri kutocin duku alonge na iwasa isu katuwa, dan lelan shin ninghinu a na liyiri Nasabbath ba.”
Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”
15 Cikilari kauwa aworo nani, “Anan rusuzu nati, na anug sa itere nijaki sa innah kite mine, idi ni nani nmyen liri Nasabbath ba?
Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, yă kai shi waje yă ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba?
16 Bara tutun ule ushono Ibrahim, ulenge na Sheitan ntereghe akus likure nin kulir, itereghe na iwasa ibunku ghe liyiri Nasabbath ba?”
Ashe, bai kamata a’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”
17 Na abelle ile imone, vat nale na idi nivira nanghe lanza incing, vat ligoze wadi su liburi liboo, kitene nimon ididia na asu.
Sa’ad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi.
18 Ame Yesu woro nani, “Kipin tigoo Kutelle di nafo iyaghari? Nin nyaghari nba gwadu kinin muna?
Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi?
19 Kidi nafo fimus kuku, fongo na unit nyawna amin nfilo nanya kunen me, in foni nkuno fiso kutca kudia, anyin kusho ani nda kee addo mine tilanghe.”
Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.”
20 Tutun aworo, “Min nyanghari nba gwadu kipin tigoo Kutelle muna?
Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?
21 Kidi nafo uyist na uwani nyauna, amunu nin nayanga atat an nbulun, udu kubi na umuzo.”
Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.”
22 Yesu wa do lizzi nanya kipin nin nigbir libau udu Urshulima a dursuzo nani.
Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa.
23 Umong woroghe, “Cikilari, anan nse ntucu ba karnu ba?” A belle nani,
Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu,
24 “Suun nnono inan pira kibulun kishuut, bara anit gbardang ba piziru, na iba se upiruwe ba.
“Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba.
25 Kubi na unan kilari nnuzu, amin ntursu kibulun, anung ba yisinu ndas inin riyuu kibulun woro, 'Cikilari, Cikilari, tiba piru.' Ame ba kauwu aworo munu, 'Na meng yiru munu, sa inuzu nwere.'
Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’
26 Aning ba woru, 'Tina tii tisono nbun fe, udursuzu tibau bite.'
“Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’
27 Ame ba kauwa nani, 'Meng bellin minu, na meng yiru kika na inuzu ku ba. Cacanan kupo nighe, anan magunta.'
“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’
28 Kubi ba dak na iba su kuculu nin yaru nayini, kubi na iyene Ibrahim, Ishaku, Yakubu, nin vat na nan nliru nin nnu Kutelle, nanya kipin tigo me, - anung inutun munu ndas.
“Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.
29 Iba da duru unuzu nasari annass inyi, inani nshino idin nlii nimonli kutebul kipin tigoo Kutelle.
Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah.
30 Yinon nani, unan ncizinu ba so unan kidung, unan kidung da so unan ncizinu.”
Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”
31 Kubi baat, amon Afarsayawa da kiti me iworo, “Caan suuna kikane bara Hirudus dinin su amollufi.”
A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”
32 Yesu woro “Caan idi bellin kinyinyo kane, 'Ndin kaluzu nagbergenu nshizhino nin tikonu, kitimone nin nkui, a liyiri lin tat, nba malu katuwa nighe.'
Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina.
33 Nanya nko yang, usoyi doli, ntunun kitimone nin nkui, nin liyiri ndortine, na iyinna imolu unan nliru nin nnu Kutelle ndas nin Urshulima ba.
Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’
34 Urshulima, Urshulima, te na udin molusu anan nliru nin nnu Kutelle ufiliso alenge na ina tu nani kitife. Ndinin su npitirin nono fe, nafo kukuru na asa a pitirino nono me nanya nagilit nafe nyinna nani ba.
“Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!
35 Yene nfillo kilari fe, meng bellin fi, na iba kuru uyenei ba, se ubelle, 'Unan nmariarife ulenge na uba dak nanya lisan Cikilare.'”
Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’”

< Luka 13 >