< Katwa Nono Katwa 24 >
1 Na ayiri atat in kata, Ananiyas udya na Priest, among akune nin, nin mong una yirun liru lissame Teritullus, nya udu kite. Ale anite da nin vurun liru litin Bulus.
Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna.
2 Na Bulus in yissina in bun gumne, Teritullus tunna aghanan vurzughe in liru aworo ugumne, “Bara fe tidi nin lissosin limang; tutung ukpiluzung in bunfe in danin nimon icene in nmyen bit;
Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, “Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu;
3 nani nin godo udya tikpana vat nin nimon ilenge na usu, Felix uniti udindya.
don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus.
4 Bara na ayedi in yissafi kang ba, indin potufi acara, lanzai baat nin kunene.
Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan.
5 Bara tikpaghe nin kulapin tizu na Yahudawa vat nanya nyii inari uduka. Amere udya nanan dortu kunan Nazeret.
An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa.
6 Amani mala uti kutii inlira kudyawe facak; unare tinani kpaghe.
Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. [Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu.]
7 Amma ugo likume Lisiyas wa dak, a da kpalkinghe nin likara na cara bite.
Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu.
8 Asa utiro Bulusku kitenen tipinpin tone, fewang manin yinnu imon irika na tidin bellu litime.”
Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai.
9 A Yahudawe ligowe vat joro Bulus iworo, uliru ulele kidegenghari.
Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne.
10 Ama na ugumne woro Bulus ku alirin, Bulus kawa, “Inyinno nwo fedi unan mawucuwucu nmyen mone inworsu, bara nani nin kibinayi kibo inma bell uliru litining.
lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, “Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani.
11 Use uyinnu in woro na isa kata ayiri likure nin naba ba nin duning u'Urushalima indi su usujada;
Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada.
12 na inung wase mengku nanya kutii in lira kudywe, na meng wasu mayardang nin mong mine ba, tutung na meng na tulu ligozin nanit ba, na inansu nani kutii in lira kudywe ba, a na inna su nani nanya kagbri ba;
Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba.
13 tutung na inung wasa durofi ulire na idin vuszi mung ba nene.
Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau.
14 Ama meng yinna nbunfe nworu, kitene libauwe na inung din yiccu umon ubi, in loli libau lirumere ndin su Kutelle nacif ning katwa. Meng di lau nanya vat nimon ile na idin duka nin nana liru nin nuu Kutelle.
Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
15 Meng dinin yinnu urumere kiti Kutelle, nafo na ale anite din caa ndakin fituzu nanan kul, nan vat nanit alau nin nanan dinong;
Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu;
16 tutung nanya nile imon, ndi katwa nwo in yitta nin kibinayin sali nalapi nbun Kutelle nin nanit nanyan vat nimon.
a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura.
17 Nene kimalin katu nakus gbardan inna dak nin bunnu udya a ufillu nikubu bara anit ning.
Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai.
18 Na nwa din sunani, among a Yahudawa in Asiya wasei nanya lidun kusu litining nanya kutii inlire, na nwa di nin ligozin sa ufiu nayi ba.
Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba.
19 Ale anite na idin bunfe, na ibellin imon irika na idumun kibinayi ninmi, adi idimun nimonimon.
Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na.
20 Sa na anit alele bellin utanu ule na inasei mun kubi ko nq nwq yissin kudaru na Yahudawe;
In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa;
21 andi na macas ile imon irume na nwa ghatin liwui nbelle kube na nwa yissin nbun mine, 'Ubelen fitu nanan kularita udi mawucuwucu kitimone.'”
sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'”
22 Iwa bellu Felix ku gegeme kitene libauwe, bara nani ata a Yahudawe so ncaa. Aworo, “Vat kubi ko na Lasiya udya nasoje da unuzun Urushalima imanin wusu uliru mine.”
Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, “Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci.”
23 Anin woro kusoje asu ucaa in Bulus, tutung na awayita gangang ba, yenje awa nazu adondon me nin bunghe sa uda lissughe.
Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi.
24 Na ayiri baat in kata, Felix kpila nin Durisilla uwani me, kunan Jewess, anin to iyiccila Bulus ku, anin lanza kitime ubelle yinnu sa uyenu kitene Kristi Yesu.
Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu.
25 Ama na Bulus lira ninghe kitene lissosin lilau, ukifu litin, nin dakin shara, fiu kpa Felix ku; anin kawa, “Can nene, asa nse kubi tutung inma yicculu fi.”
Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, “Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka.”
26 Kubi kurum kone, awadin su Bulus ma ninghe ikurfu, unare asa to idak ninghe anin lira ninghe.
A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi.
27 Ama na akusu aban kata, posiyus Fistus so ugumna kimal in Felix, Felix wadi ninsu ase useru kitin na Yahudawa, asuna Bulus ku alii ubun nanya tursu.
Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.