< Leviticus 18 >
1 locutusque est Dominus ad Mosen dicens
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 loquere filiis Israhel et dices ad eos ego Dominus Deus vester
“Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku.
3 iuxta consuetudinem terrae Aegypti in qua habitastis non facietis et iuxta morem regionis Chanaan ad quam ego introducturus sum vos non agetis nec in legitimis eorum ambulabitis
Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa.
4 facietis iudicia mea et praecepta servabitis et ambulabitis in eis ego Dominus Deus vester
Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
5 custodite leges meas atque iudicia quae faciens homo vivet in eis ego Dominus
Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji.
6 omnis homo ad proximam sanguinis sui non accedet ut revelet turpitudinem eius ego Dominus
“‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji.
7 turpitudinem patris et turpitudinem matris tuae non discoperies mater tua est non revelabis turpitudinem eius
“‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.
8 turpitudinem uxoris patris tui non discoperies turpitudo enim patris tui est
“‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.
9 turpitudinem sororis tuae ex patre sive ex matre quae domi vel foris genita est non revelabis
“‘Kada ka yi jima’i da’yar’uwarka, ko’yar mahaifinka ko’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.
10 turpitudinem filiae filii tui vel neptis ex filia non revelabis quia turpitudo tua est
“‘Kada ka yi jima’i da’yar ɗanka ko’yar’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.
11 turpitudinem filiae uxoris patris tui quam peperit patri tuo et est soror tua non revelabis
“‘Kada ka yi jima’i da’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita’yar’uwarka ce.
12 turpitudinem sororis patris tui non discoperies quia caro est patris tui
“‘Kada ka yi jima’i da’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.
13 turpitudinem sororis matris tuae non revelabis eo quod caro sit matris tuae
“‘Kada ka yi jima’i da’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.
14 turpitudinem patrui tui non revelabis nec accedes ad uxorem eius quae tibi adfinitate coniungitur
“‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.
15 turpitudinem nurus tuae non revelabis quia uxor filii tui est nec discoperies ignominiam eius
“‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.
16 turpitudinem uxoris fratris tui non revelabis quia turpitudo fratris tui est
“‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.
17 turpitudinem uxoris tuae et filiae eius non revelabis filiam filii eius et filiam filiae illius non sumes ut reveles ignominiam eius quia caro illius sunt et talis coitus incestus est
“‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma’yarta. Kada ka yi jima’i da’yar ɗanta ko’yar’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.
18 sororem uxoris tuae in pelicatum illius non accipies nec revelabis turpitudinem eius adhuc illa vivente
“‘Kada ka auri’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.
19 ad mulierem quae patitur menstrua non accedes nec revelabis foeditatem eius
“‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.
20 cum uxore proximi tui non coibis nec seminis commixtione maculaberis
“‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.
21 de semine tuo non dabis ut consecretur idolo Moloch nec pollues nomen Dei tui ego Dominus
“‘Kada ku ba da wani daga cikin’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.
22 cum masculo non commisceberis coitu femineo quia abominatio est
“‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.
23 cum omni pecore non coibis nec maculaberis cum eo mulier non subcumbet iumento nec miscebitur ei quia scelus est
“‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.
24 ne polluamini in omnibus his quibus contaminatae sunt universae gentes quas ego eiciam ante conspectum vestrum
“‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu.
25 et quibus polluta est terra cuius ego scelera visitabo ut evomat habitatores suos
Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.
26 custodite legitima mea atque iudicia et non faciat ex omnibus abominationibus istis tam indigena quam colonus qui peregrinatur apud vos
Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama,
27 omnes enim execrationes istas fecerunt accolae terrae qui fuerunt ante vos et polluerunt eam
gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu.
28 cavete ergo ne et vos similiter evomat cum paria feceritis sicut evomuit gentem quae fuit ante vos
Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku.
29 omnis anima quae fecerit de abominationibus his quippiam peribit de medio populi sui
“‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa.
30 custodite mandata mea nolite facere quae fecerunt hii qui fuerunt ante vos et ne polluamini in eis ego Dominus Deus vester
Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”