< I Paralipomenon 24 >
1 porro filiis Aaron hae partitiones erunt filii Aaron Nadab et Abiu et Eleazar et Ithamar
Waɗannan su ne sassan’ya’yan Haruna maza.’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
2 mortui sunt autem Nadab et Abiu ante patrem suum absque liberis sacerdotioque functus est Eleazar et Ithamar
Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
3 et divisit eos David id est Sadoc de filiis Eleazar et Ahimelech de filiis Ithamar secundum vices suas et ministerium
Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
4 inventique sunt multo plures filii Eleazar in principibus viris quam filii Ithamar divisit autem eis hoc est filiis Eleazar principes per familias sedecim et filiis Ithamar per familias et domos suas octo
Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
5 porro divisit utrasque inter se familias sortibus erant enim principes sanctuarii et principes Dei tam de filiis Eleazar quam de filiis Ithamar
Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
6 descripsitque eos Semeias filius Nathanahel scriba Levites coram rege et principibus et Sadoc sacerdote et Ahimelech filio Abiathar principibus quoque familiarum sacerdotalium et leviticarum unam domum quae ceteris praeerat Eleazar et alteram domum quae sub se habebat ceteros Ithamar
Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
7 exivit autem sors prima Ioiarib secunda Iedeiae
Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya,
8 tertia Arim quarta Seorim
na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim,
9 quinta Melchia sexta Maiman
na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin,
10 septima Accos octava Abia
na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya,
11 nona Hiesu decima Sechenia
na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya,
12 undecima Eliasib duodecima Iacim
na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim,
13 tertiadecima Oppa quartadecima Isbaal
na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,
14 quintadecima Belga sextadecima Emmer
na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer,
15 septimadecima Ezir octavadecima Hapses
na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez,
16 nonadecima Phetheia vicesima Iezecel
na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel,
17 vicesima prima Iachin vicesima secunda Gamul
na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul,
18 vicesima tertia Dalaiau vicesima quarta Mazziau
na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.
19 hae vices eorum secundum ministeria sua ut ingrediantur domum Domini et iuxta ritum suum sub manu Aaron patris eorum sicut praecepit Dominus Deus Israhel
Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.
20 porro filiorum Levi qui reliqui fuerant de filiis Amram erat Subahel et filiis Subahel Iedeia
Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.
21 de filiis quoque Roobiae princeps Iesias
Game da Rehabiya kuwa, daga’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
22 Isaaris vero Salemoth filiusque Salemoth Iaath
Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
23 filiusque eius Ieriahu Amarias secundus Iazihel tertius Iecmaam quartus
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
24 filius Ozihel Micha filius Micha Samir
Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga’ya’yan Mika maza, Shamir.
25 frater Micha Iesia filiusque Iesiae Zaccharias
Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.
26 filii Merari Mooli et Musi filius Ioziau Benno
’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.
27 filius quoque Merari Oziau et Soem et Zacchur et Hebri
’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.
28 porro Mooli filius Eleazar qui non habebat liberos
Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da’ya’ya maza.
29 filius vero Cis Ierahemel
Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel.
30 filii Musi Mooli Eder et Ierimoth isti filii Levi secundum domos familiarum suarum
Kuma’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.
31 miseruntque et ipsi sortes contra fratres suos filios Aaron coram David rege et Sadoc et Ahimelech et principibus familiarum sacerdotalium et leviticarum tam maiores quam minores omnes sors aequaliter dividebat
Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.