< Osee Propheta 4 >

1 [Audite verbum Domini, filii Israël, quia judicium Domino cum habitatoribus terræ: non est enim veritas, et non est misericordia, et non est scientia Dei in terra.
Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
2 Maledictum, et mendacium, et homicidium, et furtum, et adulterium inundaverunt, et sanguis sanguinem tetigit.
Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai.
3 Propter hoc lugebit terra, et infirmabitur omnis qui habitat in ea, in bestia agri, et in volucre cæli; sed et pisces maris congregabuntur.
Saboda wannan ƙasar tana makoki, kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace; namun jeji da tsuntsayen sararin sama da kuma kifin teku suna mutuwa.
4 Verumtamen unusquisque non judicet, et non arguatur vir: populus enim tuus sicut hi qui contradicunt sacerdoti.
“Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma, kada wani mutum yă zargi wani, gama mutanenka suna kama da waɗanda suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.
5 Et corrues hodie, et corruet etiam propheta tecum. Nocte tacere feci matrem tuam.
Kuna tuntuɓe dare da rana, annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku. Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,
6 Conticuit populus meus, eo quod non habuerit scientiam: quia tu scientiam repulisti, repellam te, ne sacerdotio fungaris mihi; et oblita es legis Dei tui, obliviscar filiorum tuorum et ego.
mutanena suna hallaka saboda jahilci. “Domin kun ƙi neman sani, ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina; domin kun ƙyale dokar Allahnku, ni ma zan ƙyale’ya’yanku.
7 Secundum multitudinem eorum sic peccaverunt mihi: gloriam eorum in ignominiam commutabo.
Yawan ƙaruwar firistoci, haka suke yawan zunubi a kaina; sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.
8 Peccata populi mei comedent, et ad iniquitatem eorum sublevabunt animas eorum.
Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena suna kuma haɗamar muguntarsu.
9 Et erit sicut populus, sic sacerdos; et visitabo super eum vias ejus, et cogitationes ejus reddam ei.
Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke. Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu in kuma sāka musu saboda ayyukansu.
10 Et comedent, et non saturabuntur; fornicati sunt, et non cessaverunt: quoniam Dominum dereliquerunt in non custodiendo.
“Za su ci amma ba za su ƙoshi ba; za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba, gama sun rabu da Ubangiji don su ba da kansu
11 Fornicatio, et vinum, et ebrietas auferunt cor.
ga karuwanci, ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi, waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
12 Populus meus in ligno suo interrogavit, et baculus ejus annuntiavit ei; spiritus enim fornicationum decepit eos, et fornicati sunt a Deo suo.
Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace suka kuwa sami amsa daga sanda. Halin karuwanci yakan ɓad da su; sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
13 Super capita montium sacrificabant, et super colles ascendebant thymiama; subtus quercum, et populum, et terebinthum, quia bona erat umbra ejus; ideo fornicabuntur filiæ vestræ, et sponsæ vestræ adulteræ erunt.
Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai, a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri, inda inuwa take da daɗi. Saboda haka’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
14 Non visitabo super filias vestras cum fuerint fornicatæ, et super sponsas vestras cum adulteraverint, quoniam ipsi cum meretricibus conversabantur, et cum effeminatis sacrificabant; et populus non intelligens vapulabit.
“Ba zan hukunta’ya’yanku mata sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba, balle surukanku mata, sa’ad da suka yi zina, gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada, mutane marasa ganewa za su lalace!
15 Si fornicaris tu, Israël, non delinquat saltem Juda; et nolite ingredi in Galgala, et ne ascenderitis in Bethaven, neque juraveritis: Vivit Dominus!
“Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
16 Quoniam sicut vacca lasciviens declinavit Israël; nunc pascet eos Dominus, quasi agnum in latitudine.
Isra’ilawa masu taurinkai ne, kamar karsana mai taurinkai. Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?
17 Particeps idolorum Ephraim: dimitte eum.
Efraim ya haɗa kai da gumaka; ku ƙyale shi kurum!
18 Separatum est convivium eorum; fornicatione fornicati sunt: dilexerunt afferre ignominiam protectores ejus.
Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare, sai suka ci gaba da karuwancinsu; masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.
19 Ligavit eum spiritus in alis suis, et confundentur a sacrificiis suis.]
Guguwa za tă share su, hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.

< Osee Propheta 4 >