< 야고보서 3 >

1 내 형제들아! 너희는 선생 된 우리가 더 큰 심판을 받을 줄을 알고 선생이 되지 말라
Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani.
2 우리가 다 실수가 많으니 만일 말에 실수가 없는 자면 곧 온전한 사람이라 능히 온 몸에 굴레 씌우리라
Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa.
3 우리가 말을 순종케 하려고 그 입에 재갈먹여 온 몸을 어거하며
Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya.
4 또 배를 보라 그렇게 크고 광풍에 밀려가는 것들을 지극히 작은 키로 사공의 뜻대로 운전하나니
Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so.
5 이와같이 혀도 작은 지체로되 큰 것을 자랑하도다 보라 어떻게 작은 불이 어떻게 많은 나무를 태우는가
Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta.
6 혀는 곧 불이요 불의의 세계라 혀는 우리 지체 중에서 온 몸을 더럽히고 생의 바퀴를 불사르나니 그 사르는 것이 지옥 불에서 나느니라 (Geenna g1067)
Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al'amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi. (Geenna g1067)
7 여러 종류의 짐승과 새며 벌레와 해물은 다 길들므로 사람에게 길들었거니와
Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma.
8 혀는 능히 길들일 사람이 없나니 쉬지 아니하는 악이요 죽이는 독이 가득한 것이라
Amma game da harshe, babu wani a cikin 'yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa.
9 이것으로 우리가 주 아버지를 찬송하고 또 이것으로 하나님의 형상대로 지음을 받은 사람을 저주하나니
Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la'antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah.
10 한 입으로 찬송과 저주가 나는도다 내 형제들아! 이것이 마땅치 아니하니라
Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba.
11 샘이 한 구멍으로 어찌 단 물과 쓴 물을 내겠느뇨
Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya?
12 내 형제들아 어찌 무화과나무가 감람 열매를, 포도나무가 무화과를 맺겠느뇨 이와 같이 짠물이 단물을 내지 못하느니라
''Yan'uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba.
13 너희 중에 지혜와 총명이 있는 자가 누구뇨 그는 선행으로 말미암아 지혜의 온유함으로 그 행함을 보일지니라
Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali'u da hikima ke sawa.
14 그러나 너희 마음 속에 독한 시기와 다툼이 있으면 자랑하지 말라 진리를 거스려 거짓하지 말라
Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya.
15 이러한 지혜는 위로부터 내려온 것이 아니요 세상적이요 정욕적이요 마귀적이니
Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu.
16 시기와 다툼이 있는 곳에는 요란과 모든 악한 일이 있음이니라
Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta.
17 오직 위로부터 난 지혜는 첫째 성결하고 다음에 화평하고 관용하고 양순하며 긍휼과 선한 열매가 가득하고 편벽과 거짓이 없나니
Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma.
18 화평케 하는 자들은 화평으로 심어 의의 열매를 거두느니라
Kuma 'ya'yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.

< 야고보서 3 >