< 갈라디아서 1 >

1 사람들에게서 난 것도 아니요 사람으로 말미암은 것도 아니요 오직 예수 그리스도와 및 죽은 자 가운데서 그리스도를 살리신 하나님 아버지로 말미암아 사도 된 바울은
Wannan Bulus manzo ne. Manzancina kuwa, bai zo daga mutane ba ko mutum, amma ta wurin Yesu Almasihu da Allah Uba wanda da ya tashe shi daga matattu.
2 함께 있는 모든 형제로 더불어 갈라디아 여러 교회들에게
Ni da dukan 'yan'uwa da nake tare da su a nan, ina rubuto maku ku iklisiyoyi da ke a Galatiya.
3 우리 하나님 아버지와 주 예수 그리스도로 좇아 은혜와 평강이 있기를 원하노라
Alheri zuwa gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangjinmu Yesu Almasihu,
4 그리스도께서 하나님 곧 우리 아버지의 뜻을 따라 이 악한 세대에서 우리를 건지시려고 우리 죄를 위하여 자기 몸을 드리셨으니 (aiōn g165)
wanda ya ba da kansa domin zunubanmu saboda ya kubutar da mu daga wannan mugun zamani, bisa ga nufin Allah da Ubanmu. (aiōn g165)
5 영광이 저에게 세세토록 있을지어다! 아멘 (aiōn g165)
Daukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin. (aiōn g165)
6 그리스도의 은혜로 너희를 부르신 이를 이같이 속히 떠나 다른 복음 좇는 것을 내가 이상히 여기노라
Na yi mamaki kwarai yadda kuka juya da sauri zuwa wata bishara daban. Na yi mamakin cewa kuna juyawa daga shi wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu.
7 다른 복음은 없나니 다만 어떤 사람들이 너희를 요란케 하여 그리스도의 복음을 변하려 함이라
Ba wata bishara, amma akwai wadansu mutane da suke kawo maku rudani kuma suna so su gurbata bisharar Almasihu.
8 그러나 우리나 혹 하늘로부터 온 천사라도 우리가 너희에게 전한 복음 외에 다른 복음을 전하면 저주를 받을지어다!
Amma, ko da mu ne ko mala'ika daga sama ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda muka yi shelar ta, la'ananne ne.
9 우리가 전에 말하였거니와 내가 지금 다시 말하노니 만일 누구든지 너희의 받은 것 외에 다른 복음을 전하면 저주를 받을지어다!
Kamar yadda muka fadi maku a da, yanzu kuma ina sake fada, “Idan wani ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda kuka karba, la'ananne ne.”
10 이제 내가 사람들에게 좋게 하랴 하나님께 좋게 하랴 사람들에게 기쁨을 구하랴 내가 지금까지 사람의 기쁨을 구하는 것이었더면 그리스도의 종이 아니니라
To yanzu ina neman shaidar mutane ne ko Allah? Ina neman in gamshi mutane ne? Idan har yanzu ina kokarin in gamshi mutane ne, ni ba bawan Almasihu ba ne.
11 형제들아 내가 너희에게 알게 하노니 내가 전한 복음이 사람의 뜻을 따라 된 것이 아니라
Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba.
12 이는 내가 사람에게서 받은 것도 아니요 배운 것도 아니요 오직 예수 그리스도의 계시로 말미암은 것이라
Ban karbe ta daga mutum ba, ba ma wanda ya koyar mani A maimakon haka, ta wurin wahayin Yesu Almasihu ne zuwa gare ni.
13 내가 이전에 유대교에 있을 때에 행한 일을 너희가 들었거니와 하나님의 교회를 심히 핍박하여 잔해하고
Kun riga kun ji game da rayuwa ta a da cikin Yahudanci, yadda da nake da kwazon tsananta wa iklisiyar Allah fiye da misali kuma ina lalatar da ita.
14 내가 내 동족 중 여러 연갑자(年甲者)보다 유대교를 지나치게 믿어 내 조상의 유전에 대하여 더욱 열심이 있었으나
Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina.
15 그러나 내 어머니의 태로부터 나를 택정(擇定)하시고 은혜로 나를 부르신 이가
Amma ya gamshi Allah ya zabe ni daga cikin mahaifiyata. Ya kira ni ta wurin alherinsa.
16 그 아들을 이방에 전하기 위하여 그를 내 속에 나타내시기를 기뻐하실 때에 내가 곧 혈육과 의논하지 아니하고
Ya bayyana dansa a gareni, saboda in yi shelar sa cikin al'ummai. Nan da nan, ban nemi shawarar nama da jini ba
17 또 나보다 먼저 사도 된 자들을 만나려고 예루살렘으로 가지 아니하고 오직 아라비아로 갔다가 다시 다메섹으로 돌아갔노라
kuma ban tafi Urushalima ba wurin wadanda suka zama manzanni kafin ni. Maimakon haka sai na tafi Arebiya, daga nan sai na dawo Dimashku.
18 그 후 삼년만에 내가 게바를 심방하려고 예루살렘에 올라가서 저와 함께 십 오일을 유할쌔
Bayan shekara uku na je Urushalima don in san Kefas, na zauna da shi na kwana goma sha biyar.
19 주의 형제 야고보 외에 다른 사도들을 보지 못하였노라
Amma ban ga ko daya daga cikin manzannin ba sai Yakubu kadai, dan'uwan Ubangiji.
20 보라 내가 너희에게 쓰는 것은 하나님 앞에서 거짓말이 아니로라
Duba, a gaban Allah, ba karya nake yi ba cikin abin da na rubuta maku.
21 그 후에 내가 수리아와 길리기아 지방에 이르렀으나
Daga nan sai na je lardin Suriya da Kilikiya.
22 유대에 그리스도 안에 있는 교회들이 나를 얼굴로 알지 못하고
Har a lokacin babu wanda ya san ni a fuska a iklisiyoyin Yahudiya da suke cikin Almasihu,
23 다만 우리를 핍박하던 자가 전에 잔해하던 그 믿음을 지금 전한다 함을 듣고
amma sai labari kawai suke ji, “Wanda a da yake tsananta mana yanzu yana shelar bangaskiyar da a da yake rusarwa.”
24 나로 말미암아 영광을 하나님께 돌리니라
Suna ta daukaka Allah saboda ni.

< 갈라디아서 1 >