< 詩篇 48 >

1 ヱホバは大なり われらの神の都そのきよき山のうへにて甚くほめたたへられたまふべし
Waƙa ce. Zabura ta’ya’yan Kora maza. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
2 シオンの山はきたの端たかくしてうるはしく喜悦を地にあまねくあたふ ここは大なる王のみやこなり
Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki.
3 そのもろもろの殿のうちに神はおのれをたかき櫓としてあらはしたまへり
Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
4 みよ王等はつどひあつまりて偕にすぎゆきぬ
Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare,
5 かれらは都をみてあやしみ且おそれて忽ちのがれされり
sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.
6 戰慄はかれらにのぞみ その苦痛は子をうまんとする婦のごとし
Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.
7 なんぢは東風をおこしてタルシシの舟をやぶりたまふ
Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
8 曩にわれらが聞しごとく今われらは萬軍のヱホバの都われらの神のみやこにて之をみることをえたり 神はこの都をとこしへまで固くしたまはん (セラ)
Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. (Sela)
9 神よ我らはなんぢの宮のうちにて仁慈をおもへり
Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
10 神よなんぢの譽はその名のごとく地の極にまでおよべり なんぢの右手はただしきにて充り
Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.
11 なんぢのもろもろの審判によりてシオンの山はよろこびユダの女輩はたのしむべし
Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka.
12 シオンの周圍をありき徧くめぐりてその櫓をかぞへよ
Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta,
13 その石垣に目をとめよ そのもろもろの殿をみよ なんぢらこれを後代にかたりつたへんが爲なり
ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa.
14 そはこの神はいや遠長にわれらの神にましましてわれらを死るまでみちびきたまはん
Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.

< 詩篇 48 >