< 1 טימותי 6 >
כל אשר הם תחת על העבדות יחשבו את אדניהם ראוים לכל כבוד למען לא יחלל שם האלהים והלקח׃ | 1 |
Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa.
ואלה אשר אדניהם בני אמונה אל יקלו אתם על היותם אחים כי אם יעבדום ביותר בעבור כי מאמינים ואהובים הם המשתדלים לגמל חסד את זאת תלמד ותצוה׃ | 2 |
Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa.
האיש אשר יורה תורה אחרת ולא יעמד בדברים הבריאים של אדנינו ישוע המשיח ובלקח החסידות׃ | 3 |
Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba.
נפשו עפלה ולא ידע מאומה כי אם חלה הוא בשאלות ומחלקות מלים המביאים לידי קנאה ומריבה וגדופים וחשד רע׃ | 4 |
Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da
וכוחי הבל של אנשים נשחתי דעת ומחסרי אמת השמים את החסידות לדבר בצע סור מאנשים כאלה׃ | 5 |
yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki.” Ka zame daga wadannan abubuwa.
ואף אמנם יתרון גדול היא החסידות עם לב שמח בגורלו׃ | 6 |
Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce.
כי לא הבאנו מאומה לעולם בידוע שגם לא נוכל להוציא ממנו מאומה׃ | 7 |
Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba.
ועל כן אם יש לנו מזון וכסות נסתפקה בהם׃ | 8 |
A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura.
אבל המבקשים להעשיר יפלו בנסיון ובמוקשים וברב תאות סבלות ומשחיתות המשקיעות את האדם בשחת ובאבדון׃ | 9 |
To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka.
כי שרש כל הרעות אהבת הכסף ויש אשר ערגו לו ויסורו מן האמונה ויעציבו את נפשם במכאבים רבים׃ | 10 |
Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa.
ואתה איש האלהים ברח לך מאלה ורדף צדקה וחסידות ואמונה ואהבה וסבלנות וענוה׃ | 11 |
Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u.
הלחם המלחמה הטובה של האמונה ואחז חיי עולמים אשר נקראת להם והודית הודאה יפה בפני עדים רבים׃ (aiōnios ) | 12 |
Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau. (aiōnios )
הנני מצוך נגד האלהים המחיה את כל ונגד המשיח ישוע אשר העיד ההודאה היפה לפני פנטיוס פילטוס׃ | 13 |
Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti.
כי שמור תשמר את המצוה באין שמץ ודפי עד הופעת המשיח ישוע אדנינו׃ | 14 |
Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
אשר יראנה בעתה המברך והשליט לבדו מלך המלכים ואדני האדנים׃ | 15 |
Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki.
אשר הוא לבדו חי וקים והוא הדר באור נשגב ואיש לא ראהו ולא יוכל לראונו ולו הכבוד וגבורת עולמים אמן׃ (aiōnios ) | 16 |
Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin. (aiōnios )
את עשירי העולם הזה תצוה שלא ירום לבבם גם לא יבטחו בעשר הבוגד כי אם באלהים חיים המספיק לנו די והותר לשבע׃ (aiōn ) | 17 |
Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. (aiōn )
ויגמלו טוב ויעשירו במעשים טובים לתת מהונם ולעזר לזולתם׃ | 18 |
Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake.
ויאצרו להם אוצר ליסוד טוב לעתיד שישיגו את חיי העולם׃ | 19 |
Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai.
אתה טימותיוס שמר את הפקדון והתרחק מדברי הבל הפסולים ומן וכוחי המדע הנקרא כן בשקר׃ | 20 |
Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace.
אשר יש מתפארים בו ויתעו מן האמונה׃ [ (I Timothy 6:22) החסד עמך אמן׃ ] | 21 |
Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.