< Zakariya 3 >
1 Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi.
Then the Lord showed me Joshua the high priest standing before the angel of the Lord, and Satan standing on his right accusing him.
2 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”
And the Lord said to Satan, “The Lord rebukes you Satan. I, the Lord who has chosen Jerusalem, rebuke you. Isn't he like a half-burned stick snatched from the fire?”
3 Yanzu an sa wa Yoshuwa tufafi masu dauda sa’ad da yake tsaye a gaban mala’ikan.
Joshua was wearing filthy clothes as he stood in front of the angel.
4 Mala’ikan ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku cire masa tufafinsa masu dauda.” Sai ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ɗauke zunubanka, zan sa maka tufafi masu tsada.”
The angel said to those standing there, “Take off his filthy clothes.” Then he said to Joshua, “See how I have taken away your sins from you, and now I am dressing you with fine clothes.”
5 Sai na ce, “Sa masa rawani mai tsabta a kansa.” Aka sa masa rawani mai tsabta a kansa aka kuma sa masa tufafi yayinda mala’ikan Ubangiji yake tsaye a wurin.
Then I said, “Wrap a clean turban around his head.” So they wrapped a clean turban around his head and put the clothes on him while the angel of the Lord stood there.
6 Mala’ikan Ubangiji ya yi wa Yoshuwa wannan gargaɗi.
Then the angel of the Lord solemnly advised Joshua, saying,
7 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘In za ka yi tafiya a hanyoyina ka kuma kiyaye abubuwan da nake so, za ka zama shugaban haikalina, ka kuma lura da ɗakunan shari’ata, zan kuma ba ka wuri cikin waɗannan da suke tsaye a nan.
“This is what the Lord Almighty says: If you follow my ways and observe my commands, then you will govern my Temple and its courtyards. I will allow you to walk among those standing here.
8 “‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe.
Pay attention, high priest Joshua and all your fellow-priests that you teach! You are a sign of good things to come. Look! I am going to bring my servant, the Branch.
9 Dubi dutsen da na ajiye a gaban Yoshuwa! Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse guda, zan kuma yi rubutu a kansa,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘zan kuma kawar da zunubin ƙasan nan a rana ɗaya.
See that I have placed a precious stone in front of Joshua, a single stone with seven faces. Watch, for I myself am going to engrave seven eyes on it, declares the Lord Almighty, and I will wipe away the sins of this land in a single day.
10 “‘A wannan rana kowannenku zai gayyaci maƙwabcinsa yă zauna a ƙarƙashin itacen inabi da kuma na ɓaure,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
On that day everyone will invite their friends to sit in peace under their vines and fig trees, says the Lord Almighty.”