< Titus 1 >
1 Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah
Павло́, раб Божий, а апо́стол Ісуса Христа, по вірі ви́браних Божих і пізна́нні правди, що за благоче́стям,
2 duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, (aiōnios )
в надії вічного життя, яке обіцяв був від вічних часів необма́нливий Бог, (aiōnios )
3 da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu,
і ча́су свого з'явив Слово Своє в пропові́данні, що дору́чене було мені з наказу Спасителя нашого Бога, —
4 Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.
до Тита, щирого сина за спільною ві́рою: благодать, милість та мир від Бога Отця й Христа Ісуса, Спасителя нашого!
5 Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka.
Я для того тебе полиши́в був у Кріті, щоб ти впорядкував недокінчене та пресвітерів настанови́в по містах, як тобі я звелів, —
6 Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba.
коли хто бездога́нний, муж єдиної дружи́ни, має вірних дітей, недокорених за блуд або неслухня́ність.
7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.
Бо єпи́скоп мусить бути бездоганний, як Божий доморя́дник, не самолюбний, не гнівли́вий, не п'яни́ця, не заводія́ка, не кори́сливий,
8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse.
але гостинний до при́ходнів, добролюбець, поміркований, справедливий, побожний, стри́маний,
9 Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.
що трима́ється вірного слова згідно з наукою, щоб мав силу й навчати в здоровій науці, і переконувати противних.
10 Gama akwai’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya.
Багато бо є неслухня́них, марносло́вців, зводників, особливо ж з обрізаних, —
11 Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba.
їм треба уста́ затуляти: вони ці́лі доми баламу́тять, навчаючи, чого не належить, для зиску брудно́го.
12 Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiretawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.”
Сказав один з них, їхній власний пророк: „Крітяни за́вжди брехливі, люті звірі, черева́ні ліниві“!
13 Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya,
Це свідоцтво правдиве. Ради цієї причини докоряй їм суворо, щоб у вірі здорові були́,
14 ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba.
і на юдейські байки́ не вважали, ані на нака́зи людей, що від правди відверта́ються.
15 Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne.
Для чистих все чисте, а для занечищених та для невірних не чисте ніщо, але занечи́стилися і розум їхній, і сумління.
16 Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.
Вони тве́рдять, немов знають Бога, але відкидаються вчинками, бувши бридкі́ й неслухняні, і до всякого доброго діла нездатні.