< Ru’uya ta Yohanna 10 >
1 Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta.
Sa'anan na ga wani babban mala'ika yana zuwa daga sama. Yana lullube cikin girgije, a bisa kansa akwai bakangizo. Fuskarsa kamar rana, kafafunsa kamar ginshikan wuta.
2 Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa,
Yana rike da karamin littafi a hannunsa, da aka bude, sai ya sa kafarsa ta dama a bisa teku, kafarsa ta hagu kuma a kan kasa.
3 ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana.
Sai yayi ihu da babbar murya kamar zaki mai ruri. Lokacin da ya yi ihu, tsawan nan bakwai suka yi magana da karar su.
4 Sa’ad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.”
Da tsawan nan bakwai suka yi magana, ina dab da rubutu, amma na ji wata murya daga sama cewa, “Ka rike asirin abin da tsawan nan bakwai suka fada. Kada ka rubuta shi.”
5 Sai mala’ikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama.
Sai mala'ikan da na gani tsaye bisa teku da kasa, ya daga hannun damarsa sama.
6 Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! (aiōn )
Sai ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin - wanda ya halicci sama da duk abinda ke cikinsa, da duniya da duk abin da ke a kanta, da teku da dukan abin da ke cikinsa, sai mala'ikan ya ce, “Babu sauran jinkiri. (aiōn )
7 Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
Amma a ranar da mala'ika na bakwai yana dab da busa kahonsa, a lokacin ne asirin Allah zai cika, daidai da yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
8 Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.”
Muryar da na ji daga sama ta sake magana da ni: “Tafi, ka dauki budadden littafin da ke hannun mala'ikan da ke tsaye bisa teku da kan kasa.”
9 Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’”
Sai na tafi wurin mala'ikan na ce da shi ka bani karamin littafin. Yace dani, “Dauki littafin ka ci. Zai sa cikinka ya yi daci, amma a bakinka zai yi zaki kamar zuma.”
10 Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami.
Na dauki karamin littafin daga hannun mala'ikan na ci. Ya yi zaki sosai a bakina kamar zuma, amma da na ci, sai cikina ya zama da daci.
11 Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.”
Wani yace mani, “Dole ka sake yin annabci kuma game da mutane masu yawa, da al'ummai, da harsuna da sarakuna.”