< Zabura 54 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka. 2 Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina. 3 Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. (Sela) 4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni. 5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su. 6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau. 7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

< Zabura 54 >