< Zabura 49 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
可拉后裔的诗,交与伶长。 万民哪,你们都当听这话! 世上一切的居民,
2 babba da yaro mai arziki da talaka.
无论上流下流,富足贫穷, 都当留心听!
3 Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
我口要说智慧的言语; 我心要想通达的道理。
4 Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
我要侧耳听比喻, 用琴解谜语。
5 Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
在患难的日子,奸恶随我脚跟,四面环绕我, 我何必惧怕?
6 waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
那些倚仗财货自夸钱财多的人,
7 Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
一个也无法赎自己的弟兄, 也不能替他将赎价给 神,
8 kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
叫他长远活着,不见朽坏; 因为赎他生命的价值极贵, 只可永远罢休。
9 da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
10 Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
他必见智慧人死, 又见愚顽人和畜类人一同灭亡, 将他们的财货留给别人。
11 Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
他们心里思想: 他们的家室必永存, 住宅必留到万代; 他们以自己的名称自己的地。
12 Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
但人居尊贵中不能长久, 如同死亡的畜类一样。
13 Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. (Sela)
他们行的这道本为自己的愚昧; 但他们以后的人还佩服他们的话语。 (细拉)
14 Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. (Sheol h7585)
他们如同羊群派定下阴间; 死亡必作他们的牧者。 到了早晨,正直人必管辖他们; 他们的美容必被阴间所灭,以致无处可存。 (Sheol h7585)
15 Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. (Sela) (Sheol h7585)
只是 神必救赎我的灵魂脱离阴间的权柄, 因他必收纳我。 (细拉) (Sheol h7585)
16 Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
见人发财、家室增荣的时候, 你不要惧怕;
17 gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
因为,他死的时候什么也不能带去; 他的荣耀不能随他下去。
18 Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
他活着的时候,虽然自夸为有福 (你若利己,人必夸奖你);
19 zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
他仍必归到他历代的祖宗那里, 永不见光。
20 Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
人在尊贵中而不醒悟, 就如死亡的畜类一样。

< Zabura 49 >