< Zabura 17 >
1 Addu’a ce ta Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.
A Prayer of David. Hear the right, O LORD, attend unto my cry; give ear unto my prayer from lips without deceit.
2 Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai.
Let my judgment come forth from Thy presence; let Thine eyes behold equity.
3 Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
Thou hast tried my heart, Thou hast visited it in the night; Thou hast tested me, and Thou findest not that I had a thought which should not pass my mouth.
4 Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali.
As for the doings of men, by the word of Thy lips I have kept me from the ways of the violent.
5 Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.
My steps have held fast to Thy paths, my feet have not slipped.
6 Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.
As for me, I call upon Thee, for Thou wilt answer me, O God; incline Thine ear unto me, hear my speech.
7 Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki, kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu da hannunka na dama.
Make passing great Thy mercies, O Thou that savest by Thy right hand from assailants them that take refuge in Thee.
8 Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka
Keep me as the apple of the eye, hide me in the shadow of Thy wings,
9 daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
From the wicked that oppress, my deadly enemies, that compass me about.
10 Sun rufe zukatansu marar tausayi, da bakunansu suna magana da fariya.
Their gross heart they have shut tight, with their mouth they speak proudly.
11 Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni, a shirye suke, su jefa ni a ƙasa.
At our every step they have now encompassed us; they set their eyes to cast us down to the earth.
12 Suna kama da zaki mai yunwan abinci, kamar babban zaki mai fako a maɓuya.
He is like a lion that is eager to tear in pieces, and like a young lion lurking in secret places.
13 Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.
Arise, O LORD, confront him, cast him down; deliver my soul from the wicked, by Thy sword;
14 Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so;’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa’ya’yansu.
From men, by Thy hand, O LORD, from men of the world, whose portion is in this life, and whose belly Thou fillest with Thy treasure; who have children in plenty, and leave their abundance to their babes.
15 Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.
As for me, I shall behold Thy face in righteousness; I shall be satisfied, when I awake, with Thy likeness.