< Zabura 128 >

1 Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
שיר המעלות אשרי כל-ירא יהוה-- ההלך בדרכיו
2 Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.
יגיע כפיך כי תאכל אשריך וטוב לך
3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai’ya’ya a cikin gidanka;’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
אשתך כגפן פריה-- בירכתי ביתך בניך כשתלי זיתים-- סביב לשלחנך
4 Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.
הנה כי-כן יברך גבר-- ירא יהוה
5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
יברכך יהוה מציון וראה בטוב ירושלם--כל ימי חייך
6 bari kuma ka rayu ka ga’ya’ya’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.
וראה-בנים לבניך שלום על-ישראל

< Zabura 128 >