< Nehemiya 7 >

1 Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa.
Baada ya ukuta kukamilika kujengwa upya na nikaweka milango, mabawabu wa lango, waimbaji, na Walawi waliteuliwa.
2 Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane.
Nikamweka Hanani ndugu yangu kuwa kiongozi wa Yerusalemu, pamoja na Hanania jemadari wa ngome, kwa kuwa alikuwa mtu mwadilifu na mwenye kumcha Mungu kuliko watu wengine.
3 Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”
Nikawaambia, “Malango ya Yerusalemu yasifunguliwe mpaka jua litakapokuwa limepanda. Walinzi wa malango wakiwa bado kwenye zamu, waamuru wafunge milango na waweke makomeo. Pia wateueni wenyeji wa Yerusalemu wawe walinzi, kila mmoja kwenye lindo lake, na wengine karibu na nyumba zao wenyewe.”
4 Birnin Urushalima kuwa tana da fāɗi da girma, amma mutanen da suke zama a cikinta kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje da yawa ba tukuna.
Mji ulikuwa mkubwa, tena wenye nafasi nyingi, lakini walikuwepo watu wachache ndani yake, nazo nyumba zilikuwa bado ni magofu.
5 Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki.
Hivyo Mungu wangu akaweka moyoni mwangu kuwakusanya wakuu, maafisa na watu wa kawaida kwa ajili ya kuorodheshwa kulingana na jamaa zao. Nilikuta orodha ya vizazi ya wale waliokuwa wa kwanza kurudi toka utumwani. Haya ndiyo niliyokuta yameandikwa humo:
6 Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa.
Hawa ndio watu wa jimbo waliotoka uhamishoni, ambao Nebukadneza mfalme wa Babeli alikuwa amewachukua mateka (walirudi Yerusalemu na Yuda, kila mmoja kwenye mji wake,
7 Sun dawo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra’amiya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Nehum da kuma Ba’ana). Ga jerin mutanen Isra’ila.
wakiwa wamefuatana na Zerubabeli, Yeshua, Nehemia, Azaria, Raamia, Nahamani, Mordekai, Bilshani, Mispereti, Bigwai, Nehumu na Baana): Orodha ya wanaume wa Israeli ilikuwa:
8 Zuriyar Farosh mutum 2,172
wazao wa Paroshi 2,172
9 ta Shefatiya 372
wazao wa Shefatia 372
10 ta Ara 652
wazao wa Ara 652
11 ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,818
wazao wa Pahath-Moabu (wa jamaa ya Yeshua na Yoabu) 2,818
12 ta Elam 1,254
wazao wa Elamu 1,254
13 ta Zattu 845
wazao wa Zatu 845
14 ta Zakkai 760
wazao wa Zakai 760
15 ta Binnuyi 648
wazao wa Binui 648
16 ta Bebai 628
wazao wa Bebai 628
17 ta Azgad 2,322
wazao wa Azgadi 2,322
18 ta Adonikam 667
wazao wa Adonikamu 667
19 ta Bigwai 2,067
wazao wa Bigwai 2,067
20 ta Adin 655
wazao wa Adini 655
21 ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98
wazao wa Ateri (kupitia Hezekia) 98
22 ta Hashum 328
wazao wa Hashumu 328
23 ta Bezai 324
wazao wa Besai 324
24 ta Harif 112
wazao wa Harifu 112
25 ta Gibeyon 95.
wazao wa Gibeoni 95
26 Mutanen Betlehem da na Netofa 188
watu wa Bethlehemu na Netofa 188
27 na Anatot 128
watu wa Anathothi 128
28 na Bet-Azmawet 42
watu wa Beth-Azmawethi 42
29 na Kiriyat Yeyarim, Kefira da na Beyerot 743
watu wa Kiriath-Yearimu, Kefira na Beerothi 743
30 na Rama da na Geba 621
watu wa Rama na Geba 621
31 na Mikmash 122
watu wa Mikmashi 122
32 na Betel da na Ai 123
watu wa Betheli na Ai 123
33 na ɗayan Nebo 52
watu wa Nebo 52
34 na ɗayan Elam 1,254
wazao wa Elamu 1,254
35 na Harim 2 320
wazao wa Harimu 320
36 na Yeriko 345
wazao wa Yeriko 345
37 na Lod, da na Hadid, da na Ono 721
wazao wa Lodi, Hadidi na Ono 721
38 na Sena’a 3,930.
wazao wa Senaa 3,930
39 Ga zuriyar Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973
Makuhani: wazao wa Yedaya (kwa jamaa ya Yeshua) 973
40 ta Immer 1,052
wazao wa Imeri 1,052
41 ta Fashhur 1,247
wazao wa Pashuri 1,247
42 ta Harim 1,017.
wazao wa Harimu 1,017
43 Ga zuriyar Lawiyawa. Zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodeba) 74.
Walawi: wazao wa Yeshua (kupitia Kadmieli kupitia jamaa ya Hodavia) 74
44 Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 148.
Waimbaji: wazao wa Asafu 148
45 Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita da Shobai 138.
Mabawabu wa malango: wazao wa Shalumu, Ateri, Talmoni, Akubu, Hatita na Shobai 138
46 Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,
Watumishi wa Hekalu: wazao wa Siha, Hasufa, Tabaothi,
47 da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon,
wazao wa Kerosi, Sia, Padoni,
48 da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai,
wazao wa Lebana, Hagaba, Shalmai,
49 da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar,
wazao wa Hanani, Gideli, Gahari,
50 da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda,
wazao wa Reaya, Resini, Nekoda,
51 da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya,
wazao wa Gazamu, Uza, Pasea,
52 da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa,
wazao wa Besai, Meunimu, Nefusimu,
53 da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur,
wazao wa Bakbuki, Hakufa, Harhuri,
54 da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha,
wazao wa Basluthi, Mehida, Harsha,
55 da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema,
wazao wa Barkosi, Sisera, Tema,
56 da ta Neziya, da kuma ta Hatifa.
wazao wa Nesia na Hatifa.
57 Ga zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, da ta Soferet, da ta Ferida,
Wazao wa watumishi wa Solomoni: wazao wa Sotai, Soferethi, Perida,
58 da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel,
wazao wa Yaala, Darkoni, Gideli,
59 Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Amon.
wazao wa Shefatia, Hatili, Pokereth-Hasebaimu na Amoni.
60 Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392.
Watumishi wa Hekalu wote na wazao wa watumishi wa Solomoni 392
61 Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba,
Wafuatao walikuja kutoka miji ya Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerubu, Adoni na Imeri, lakini hawakuweza kuthibitisha kwamba jamaa zao zilikuwa uzao wa Israeli:
62 zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 642.
wazao wa Delaya, Tobia na Nekoda 642
63 Na wajen firistoci kuwa su ne, Zuriyar Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna).
Na kutoka miongoni mwa makuhani: wazao wa Hobaya, Hakosi na Barzilai (mtu aliyekuwa amemwoa binti wa Barzilai, Mgileadi, naye akaitwa kwa jina hilo).
64 Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.
Hawa walitafuta orodha za jamaa zao, lakini hawakuonekana humo, kwa hiyo waliondolewa kutoka kundi la makuhani, kwa kuwa walihesabiwa kuwa najisi.
65 Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim.
Kwa hiyo, mtawala aliagiza kuwa wasile chochote miongoni mwa vyakula vitakatifu hadi kuwe kuhani atakayehudumu kwa Urimu na Thumimu.
66 Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,
Jumla ya watu wote waliorudi walikuwa 42,360;
67 ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245.
tena zaidi ya hao walikuwepo watumishi wa kiume na wa kike 7,337; pia walikuwamo waimbaji wanaume na wanawake 245.
68 Akwai dawakai 736, alfadarai 245
Walikuwa na farasi 736, nyumbu 245
69 raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720.
ngamia 435 na punda 6,720.
70 Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci.
Baadhi ya viongozi wa jamaa walichangia kazi ya ujenzi. Mtawala alikabidhi kwenye hazina darkoni 1,000 za dhahabu, mabakuli 50, na mavazi 530 kwa ajili ya makuhani.
71 Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki.
Baadhi ya viongozi wa jamaa walikabidhi kwenye hazina darkoni 20,000 za dhahabu, na mane 2,200 za fedha kwa ajili ya kazi hiyo.
72 Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci.
Jumla ya matoleo ya watu wengine yalikuwa ni darkoni 20,000 za dhahabu, mane 2,000 za fedha, na mavazi sitini na saba ya makuhani.
73 Firistoci, da Lawiyawa, da matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da ma’aikatan haikali tare da waɗansu mutane da kuma sauran mutanen Isra’ila, suka zauna a garuruwansu. Da wata na bakwai ya zo, Isra’ilawa kuwa sun riga sun zauna a garuruwansu,
Makuhani, Walawi, mabawabu, waimbaji na watumishi wa Hekalu, pamoja na baadhi ya watu wengine na Waisraeli waliosalia waliishi katika miji yao wenyewe. Ilipotimia miezi saba, nao Waisraeli wakiwa tayari wanaishi katika miji yao,

< Nehemiya 7 >