< Mika 6 >

1 Ku saurari abin da Ubangiji ya ce, “Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu; bari tuddai su ji abin da kuke so ku faɗa.
Hear now what the LORD says: “Arise, plead your case before the mountains, and let the hills hear your voice.
2 “Ku saurara, ya ku duwatsu game da tuhumar da Ubangiji yake muku, ku ji, ku daɗaɗɗun tushin duniya. Gama Ubangiji yana da ƙara a kan mutanensa; yana tuhumar Isra’ila.
Hear, O mountains, the LORD’s indictment, you enduring foundations of the earth. For the LORD has a case against His people, and He will argue it against Israel:
3 “Ya ku mutanena, me na yi muku? Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini.
‘My people, what have I done to you? Testify against Me how I have wearied you!
4 Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.
For I brought you up from the land of Egypt and redeemed you from the house of slavery. I sent Moses before you, as well as Aaron and Miriam.
5 Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”
My people, remember what Balak king of Moab counseled and what Balaam son of Beor answered. Remember your journey from Shittim to Gilgal, so that you may acknowledge the righteousness of the LORD.’”
6 Da me zan zo a gaban Ubangiji in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah? Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya?
With what shall I come before the LORD when I bow before the God on high? Should I come to Him with burnt offerings, with year-old calves?
7 Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai da kuma rafuffukan mai dubbai goma? Zan ba da ɗan farina ne don laifina, ko’ya’yan jikina domin zunubin raina?
Would the LORD be pleased with thousands of rams, with ten thousand rivers of oil? Shall I present my firstborn for my transgression, the fruit of my body for the sin of my soul?
8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
He has shown you, O man, what is good. And what does the LORD require of you but to act justly, to love mercy, and to walk humbly with your God?
9 Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni, a ji tsoron sunana kuwa hikima ce, “Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.
The voice of the LORD calls out to the city (and it is sound wisdom to fear Your name): “Heed the rod and the One who ordained it.
10 Har yanzu zan manta, ya muguwar gida da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi?
Can I forget any longer, O house of the wicked, the treasures of wickedness and the short ephah, which is accursed?
11 Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya, da kuma buhun ma’aunan ƙarya?
Can I excuse dishonest scales or bags of false weights?
12 Attajiranta masu fitina ne; mutanenta kuma maƙaryata ne harsunansu kuwa suna yaudara.
For the wealthy of the city are full of violence, and its residents speak lies; their tongues are deceitful in their mouths.
13 Saboda haka, zan hallaka ku in lalace ku saboda zunubanku.
Therefore I am striking you severely, to ruin you because of your sins.
14 Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba, cikinku zai zama babu kome Za ku tattara amma ba za ku yi ajiyar kome ba, gama abin da kuka yi ajiya zan ba wa takobi.
You will eat but not be satisfied, and your hunger will remain with you. What you acquire, you will not preserve; and what you save, I will give to the sword.
15 Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba; za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba, za ku tattaka’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.
You will sow but not reap; you will press olives but not anoint yourselves with oil; you will tread grapes but not drink the wine.
16 Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri da dukan ayyukan gidan Ahab kun kuma bi al’adunsu. Saboda haka, zan maishe ku kufai in mai da ku abin dariya a cikin mutane, za ku sha reni a wurin al’ummai.”
You have kept the statutes of Omri and all the practices of Ahab’s house; you have followed their counsel. Therefore I will make you a desolation, and your inhabitants an object of contempt; you will bear the scorn of the nations.”

< Mika 6 >