< Mattiyu 24 >

1 Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali.
Og Jesus gik ud, bort fra Helligdommen, og hans Disciple kom til ham for at vise ham Helligdommens Bygninger.
2 Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”
Men han svarede og sagde til dem: „Se I ikke alt dette? Sandelig, siger jeg eder, her skal ikke lades Sten paa Sten, som jo skal nedbrydes.‟
3 Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?” (aiōn g165)
Men da han sad paa Oliebjerget, kom hans Disciple til ham afsides og sagde: „Sig os, naar skal dette ske? Og hvad er Tegnet paa din Tilkommelse og Verdens Ende?‟ (aiōn g165)
4 Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.
Og Jesus svarede og sagde til dem: „Ser til, at ingen forfører eder!
5 Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
Thi mange skulle paa mit Navn komme og sige: Jeg er Kristus; og de skulle forføre mange.
6 Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.
Men I skulle faa at høre om Krige og Krigsrygter. Ser til, lader eder ikke forskrække; thi det maa ske; men Enden er ikke endda.
7 Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.
Thi Folk skal rejse sig mod Folk, og Rige mod Rige, og der skal være Hungersnød og Jordskælv her og der.
8 Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.
Men alt dette er Veernes Begyndelse.
9 “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.
Da skulle de overgive eder til Trængsel og slaa eder ihjel, og I skulle hades af alle Folkeslagene for mit Navns Skyld.
10 A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,
Og da skulle mange forarges og forraade hverandre og hade hverandre.
11 annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.
Og mange falske Profeter skulle fremstaa og forføre mange.
12 Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,
Og fordi Lovløsheden bliver mangfoldig, vil Kærligheden blive kold hos de fleste.
13 amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
Men den, som holder ud indtil Enden, han skal frelses.
14 Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
Og dette Rigets Evangelium skal prædikes i hele Verden til et Vidnesbyrd for alle Folkeslagene; og da skal Enden komme.
15 “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),
Naar I da se Ødelæggelsens Vederstyggelighed, hvorom der er talt ved Profeten Daniel, staa paa hellig Grund, (den, som læser det, han give Agt!)
16 to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu.
da skulle de, som ere i Judæa, fly ud paa Bjergene;
17 Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida.
den, som er paa Taget, stige ikke ned for at hente, hvad der er i hans Hus;
18 Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa.
og den, som er paa Marken, vende ikke tilbage for at hente sine Klæder!
19 Kaiton mata masu ciki da mata masu renon’ya’ya a waɗancan kwanakin!
Men ve de frugtsommelige og dem, som give Die, i de Dage!
20 Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.
Og beder om, at eders Flugt ikke skal ske om Vinteren, ej heller paa en Sabbat;
21 Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.
thi der skal da være en Trængsel saa stor, som der ikke har været fra Verdens Begyndelse indtil nu og heller ikke skal komme.
22 “Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.
Og dersom disse Dage ikke bleve afkortede, da blev intet Kød frelst; men for de udvalgtes Skyld skulle disse Dage afkortes.
23 A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata.
Dersom nogen da siger til eder: Se, her er Kristus, eller der! da skulle I ikke tro det.
24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.
Thi falske Krister og falske Profeter skulle fremstaa og gøre store Tegn og Undergerninger, saa at ogsaa de udvalgte skulde blive forførte, om det var muligt.
25 Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.
Se, jeg har sagt eder det forud.
26 “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.
Derfor, om de sige til eder: Se, han er i Ørkenen, da gaar ikke derud; se, han er i Kamrene, da tror det ikke!
27 Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.
Thi ligesom Lynet udgaar fra Østen og lyser indtil Vesten, saaledes skal Menneskesønnens Tilkommelse være.
28 Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.
Hvor Aadselet er, der ville Ørnene samle sig.
29 “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
Men straks efter de Dages Trængsel skal Solen formørkes og Maanen ikke give sit Skin og Stjernerne falde ned fra Himmelen, og Himmelens Kræfter skulle rystes.
30 “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
Og da skal Menneskesønnens Tegn vise sig paa Himmelen; og da skulle alle Jordens Stammer jamre sig, og de skulle se Menneskesønnen komme paa Himmelens Skyer med Kraft og megen Herlighed.
31 Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
Og han skal udsende sine Engle med stærktlydende Basun, og de skulle samle hans udvalgte fra de fire Vinde, fra den ene Ende af Himmelen til den anden.
32 “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.
Men lærer Lignelsen af Figentræet: Naar dets Gren allerede er bleven blød, og Bladene skyde frem, da skønne I, at Sommeren er nær.
33 Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.
Saaledes skulle ogsaa I, naar I se alt dette, skønne, at han er nær for Døren.
34 Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru.
Sandelig, siger jeg eder, denne Slægt skal ingenlunde forgaa, førend alle disse Ting ere skete.
35 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.
Himmelen og Jorden skulle forgaa, men mine Ord skulle ingenlunde forgaa.
36 “Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
Men om den Dag og Time ved ingen, end ikke Himmelens Engle, heller ikke Sønnen, men kun Faderen alene.
37 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.
Og ligesom Noas Dage vare, saaledes skal Menneskesønnens Tilkommelse være.
38 Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;
Thi ligesom de i Dagene før Syndfloden aade og drak, toge til Ægte og bortgiftede, indtil den Dag, da Noa gik ind i Arken,
39 ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.
og ikke agtede det, førend Syndfloden kom og tog dem alle bort, saaledes skal ogsaa Menneskesønnens Tilkommelse være.
40 Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
Da skulle to Mænd være paa Marken; den ene tages med, og den anden lades tilbage.
41 Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
To Kvinder skulle male paa Kværnen; den ene tages med, og den anden lades tilbage.
42 “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.
Vaager derfor, thi I vide ikke, paa hvilken Dag eders Herre kommer.
43 Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.
Men dette skulle I vide, at dersom Husbonden vidste, i hvilken Nattevagt Tyven vilde komme, da vaagede han og tillod ikke, at der skete Indbrud i hans Hus.
44 Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.
Derfor vorder ogsaa I rede; thi Menneskesønnen kommer i den Time, som I ikke mene.
45 “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci?
Hvem er saa den tro og forstandige Tjener, som hans Herre har sat over sit Tyende til at give dem deres Mad i rette Tid?
46 Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka.
Salig er den Tjener, hvem hans Herre, naar han kommer, finder handlende saaledes.
47 Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.
Sandelig siger jeg eder, han skal sætte ham over alt, hvad han ejer.
48 Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’
Men dersom den onde Tjener siger i sit Hjerte: Min Herre tøver,
49 Sa’an nan yă fara dūkan’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.
og saa begynder at slaa sine Medtjenere og spiser og drikker med Drankerne,
50 Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.
da skal den Tjeners Herre komme paa den Dag, han ikke venter, og i den Time, han ikke ved,
51 Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.
og hugge ham sønder og give ham hans Lod sammen med Hyklerne; der skal der være Graad og Tænders Gnidsel.

< Mattiyu 24 >