< Firistoci 15 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
L’Éternel parla ainsi à Moïse et à Aaron:
2 “Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne.
"Parlez aux enfants d’Israël et dites-leur: Quiconque serait affligé de gonorrhée, son écoulement est impur.
3 Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa,
Voici quand aura lieu cette souillure de l’écoulement: si sa chair laisse distiller le flux, ou si elle est engorgée par le flux, sa souillure aura lieu.
4 “‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki.
Toute couche sur laquelle repose celui qui a le flux, sera souillée; tout meuble sur lequel il s’assied, sera souillé.
5 Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
Quiconque toucherait à sa couche, devra donc laver ses vêtements, se baigner dans l’eau, et restera souillé jusqu’au soir;
6 Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
et qui s’assoira sur le meuble où s’assied celui qui a le flux, lavera ses vêtements, se baignera dans l’eau et sera souillé jusqu’au soir.
7 “‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
Si l’on touche au corps de celui qui a le flux, on lavera ses vêtements, on se baignera dans l’eau et l’on sera souillé jusqu’au soir.
8 “‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
Si celui qui a le flux vient à cracher sur un individu pur, celui-ci lavera ses vêtements, se baignera dans l’eau et sera souillé jusqu’au soir.
9 “‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu,
Tout harnais servant à la monture de celui qui a le flux, sera souillé.
10 kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
Quiconque touche à un objet placé sous lui, sera souillé jusqu’au soir; et qui transporte un de ces objets lavera ses vêtements, se baignera dans l’eau, et restera souillé jusqu’au soir.
11 “‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
Quiconque serait touché par celui qui avait le flux et qui n’a pas encore nettoyé ses mains dans l’eau, lavera ses vêtements, se baignera dans l’eau, et restera souillé jusqu’au soir.
12 “‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa.
Un vaisseau d’argile, touché par celui qui a le flux, sera brisé; un vaisseau de bois, quel qu’il soit, sera nettoyé dans d’eau.
13 “‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke.
Quand cet homme sera délivré de sa gonorrhée, il comptera sept jours depuis son rétablissement; puis il lavera ses vêtements, baignera son corps dans une eau vive, et sera pur.
14 A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist.
Le huitième jour, il se procurera deux tourterelles ou deux jeunes colombes, se présentera devant l’Éternel, à l’entrée de la Tente d’assignation, et les remettra au pontife.
15 Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.
Le pontife les traitera, l’une comme expiatoire, l’autre comme holocauste; et il l’absoudra, devant l’Éternel, de son écoulement.
16 “‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.
Un homme qui aura laissé échapper de la matière séminale devra baigne dans l’eau tout son corps, et sera souillé jusqu’au soir.
17 Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.
Toute étoffe, toute peau, où il se trouverait de cette matière, sera nettoyée avec de l’eau et restera souillée jusqu’au soir.
18 Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma.
Et une femme avec laquelle un homme aurait habité charnellement, tous deux se baigneront dans l’eau et seront souillés jusqu’au soir.
19 “‘Sa’ad mace take al’adarta ta ƙa’ida, rashin tsabtarta ta al’adar zai ɗauki kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓa ta, zai ƙazantu har yamma.
Lorsqu’une femme éprouvera le flux (son flux, c’est le sang qui s’échappe de son corps), elle restera sept jours dans son isolement, et quiconque la touchera sera souillé jusqu’au soir.
20 “‘Duk abin da ta kwanta a kai a lokacin al’adarta zai ƙazantu, kuma duk abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.
Tout objet sur lequel elle repose lors de son isolement, sera impur; tout objet sur lequel elle s’assied, sera impur.
21 Duk wanda ya taɓa gadonta dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
Quiconque touchera à sa couche devra laver ses vêtements, se baigner dans l’eau, et restera souillé jusqu’au soir.
22 Duk wanda ya taɓa wani abin da ta zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
Quiconque touchera à quelque meuble où elle s’assoirait, lavera ses vêtements, se baignera dans l’eau, et restera souillé jusqu’au soir.
23 Ko gado ne, ko kuwa wani abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi, zai ƙazantu har yamma.
Si, en y touchant, il était lui-même sur la couche où elle est assise, il serait souillé jusqu’au soir.
24 “‘In namiji ya kwana da ita, al’adarta kuwa ta taɓa shi, zai ƙazantu na kwana bakwai; duk kuma gadon da ya kwanta a kai, zai ƙazantu.
Mais si un homme vient à cohabiter avec elle, de sorte que son Impureté se communique à lui, il sera souillé sept jours, et toute couche sur laquelle il reposera sera souillée.
25 “‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta.
SI le flux sanguin d’une femme a lieu pendant plusieurs jours, hors de l’époque de son isolement, ou s’il se prolonge au-delà de son isolement ordinaire, tout le temps que coulera sa souillure, elle sera comme à l’époque de son Isolement: elle est Impure.
26 Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta.
Toute couche sur laquelle elle repose pendant toute la durée de cet écoulement sera, à son égard, comme la couche où elle reposait lors de son isolement; tout meuble sur lequel elle s’assied sera souillé, comme II le serait lors de son isolement.
27 Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
Quiconque les touchera deviendra impur; il devra laver ses vêtements, se baigner dans l’eau, et restera souillé jusqu’au soir.
28 “‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki.
Lorsqu’elle sera délivrée de son flux, elle comptera sept jours, après quoi elle sera pure.
29 A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada.
Au huitième jour, elle se procurera deux tourterelles ou deux jeunes colombes, qu’elle apportera au pontife, à l’entrée de la Tente d’assignation.
30 Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.
Le pontife traitera l’un des oiseaux comme expiatoire, l’autre comme holocauste; et il l’absoudra, devant l’Éternel, de la souillure de son écoulement.
31 “‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’”
Vous devez éloigner les enfants d’Israël de ce qui pourrait les souiller, afin qu’ils n’encourent point la mort par leur contamination, en souillant ma demeure qui est au milieu d’eux.
32 Waɗannan su ne ƙa’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi,
Telle est la règle pour celui qui a le flux, et pour celui qui aurait laissé échapper de la matière séminale, cause d’impureté;
33 ƙa’idodi ne kuma ga mace wadda take al’ada, ga namiji ko macen da take ɗiga, ga kuma namijin da ya kwana da mace marar tsarki.
pour la femme qui souffre, lors de son isolement; pour la personne, homme ou femme, dont le flux se prolonge, et pour l’homme qui cohabite avec une femme impure."

< Firistoci 15 >