< Mahukunta 11 >

1 Yefta mutumin Gileyad, jarumi ne ƙwarai. Mahaifinsa ne Gileyad; mahaifiyar kuwa karuwa ce.
Now Jephthah the Gileadite was a mighty warrior, but he was the son of a prostitute. Gilead was his father.
2 Matar Gileyad ta haifa masa’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”
Gilead's wife also gave birth to his other sons. When his wife's sons grew up, they forced Jephthah to leave the house and said to him, “You are not going to inherit anything from our family. You are the son of another woman.”
3 Saboda haka Yefta ya tsere daga’yan’uwansa ya zauna a ƙasar Tob, inda waɗansu’yan iska suka kewaye shi suka bi shi.
So Jephthah fled from his brothers and lived in the land of Tob. Lawless men joined Jephthah and they came and went with him.
4 Ana nan, sa’ad da Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa hari,
Some days later, the people of Ammon made war against Israel.
5 dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob.
When the people of Ammon made war against Israel, the elders of Gilead went to bring Jephthah back from the land of Tob.
6 Suka ce masa, “Ka zo ka zama mana shugaba, don mu yaƙi Ammonawa.”
They said to Jephthah, “Come and be our leader that we may fight with the people of Ammon.”
7 Yefta ya ce musu, “Ba kun ƙi ni kuka kuma kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuke zuwa wurina yanzu sa’ad da kuke cikin wahala?”
Jephthah said to the leaders of Gilead, “You hated me and forced me to leave my father's house. Why do you come to me now when you are in trouble?”
8 Mutanen Gileyad suka ce masa, “Duk da haka, muna juyo wajenka yanzu, ka zo tare da mu mu yaƙi Ammonawa, za ka kuma zama shugaban duk wanda yake zama a Gileyad.”
The elders of Gilead said to Jephthah, “That is why we are turning to you now; come with us and fight with the people of Ammon, and you will become the leader over all who live in Gilead.”
9 Yefta ya ce, “A ce kun dawo da ni in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna, zan zama shugabanku?”
Jephthah said to the elders of Gilead, “If you bring me home again to fight against the people of Ammon, and if Yahweh gives us victory over them, I will be your leader.”
10 Dattawan Gileyad suka ce, “Ubangiji ne shaidanmu; za mu yi duk abin da ka ce.”
The elders of Gilead said to Jephthah, “May Yahweh be witness between us if we do not do as we say!”
11 Saboda haka Yefta ya tafi tare da dattawan Gileyad, mutanen kuwa suka naɗa shi shugabansu da kuma sarkinsu. Ya kuwa maimaita dukan maganarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.
So Jephthah went with the elders of Gilead, and the people made him leader and commander over them. When he was before Yahweh in Mizpah, Jephthah repeated all the promises he made.
12 Sa’an nan Yefta ya aiki jakadu zuwa wurin sarkin Ammonawa su tambaya, “Me ya haɗa ka da ni, da ka kawo wa ƙasata yaƙi?”
Then Jephthah sent messengers to the king of the people of Ammon, saying, “What is this conflict between us? Why have you come with force to take our land?”
13 Sarkin Ammonawa ya ce wa jakadu, “Sa’ad da Isra’ilawa suka fito daga Masar, sun ƙwace mini ƙasa tun daga Arnon zuwa Yabbok, har zuwa Urdun. Yanzu ka mayar mini ita cikin salama.”
The king of the people of Ammon answered to the messengers of Jephthah, “Because when Israel came up out of Egypt, they seized my land from the Arnon to the Jabbok, over to the Jordan. Now give back those lands in peace.”
14 Yefta ya sāke aikan jakadu wurin sarki,
Again Jephthah sent messengers to the king of the people of Ammon,
15 yana cewa, “Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.
and he said, “This is what Jephthah says: Israel did not take the land of Moab and the land of the people of Ammon,
16 Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh.
but they came up from Egypt, and Israel went through the wilderness to the Sea of Reeds and on to Kadesh.
17 Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.
When Israel sent messengers to the king of Edom, saying, 'Please let us pass through your land,' the king of Edom would not listen. They also sent messengers to the king of Moab, but he refused. So Israel stayed at Kadesh.
18 “Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.
Then they went through the wilderness and turned away from the land of Edom and the land of Moab, and they went along the east side of the land of Moab and they camped on the other side of the Arnon. But they did not go into the territory of Moab, for the Arnon was Moab's border.
19 “Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon, ta ce masa, ‘Ka bar mu mu ratsa ƙasarka mu wuce zuwa wurinmu.’
Israel sent messengers to Sihon, king of the Amorites, who ruled in Heshbon; Israel said to him, 'Please, let us pass through your land to the place that is ours.'
20 Sihon dai, bai amince da Isra’ila su ratsa ƙasarsa ba. Ya tattara dukan mutanensa suka yi sansani a Yahza suka kuwa yaƙi Isra’ila.
But Sihon did not trust Israel to pass through his territory. So Sihon gathered all his army together and moved it to Jahaz, and there he fought against Israel.
21 “Sa’an nan Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da Sihon da dukan mutanensa a hannun Isra’ila, suka kuwa ci nasara a kansu. Isra’ila ta ƙwace dukan ƙasar Amoriyawa da suke zaune a ƙasar,
Then Yahweh, the God of Israel, gave Sihon and all his people into the hand of Israel and they defeated them. So Israel took all the land of the Amorites who lived in that country.
22 suka ƙwace dukan yankin Amoriyawa tun daga ƙasar Arnon zuwa Yabbok, daga hamada har zuwa Urdun.
They took over everything within the territory of the Amorites, from the Arnon to the Jabbok, and from the wilderness to the Jordan.
23 “To, da yake Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya kori Amoriyawa a gaban mutanensa Isra’ila, wane’yanci kake da shi da za ka karɓe ta?
So then Yahweh, the God of Israel, has driven out the Amorites before his people Israel, and should you now take possession of their land?
24 Ba za ka karɓi abin da allahnka Kemosh ya ba ka ba? Haka mu ma, duk abin da Ubangiji Allahnmu ya riga ya ba mu, za mu mallake shi.
Will you not take over the land that Chemosh, your god, gives you? So whatever land Yahweh our God has given us, we will take over.
25 Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su?
Now are you really better than Balak son of Zippor, king of Moab? Did he dare to have an argument with Israel? Did he ever wage war against them?
26 Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon, Arower da ƙauyukan kewayenta da dukan biranen da suke gefen Arnon. Me ya sa ba ka karɓe su a lokacin ba?
While Israel lived for three hundred years in Heshbon and its villages, and in Aroer and its villages, and in all the cities that are along the banks of the Arnon—why then did you not take them back during that time?
27 Ban yi maka laifi ba, amma kana musguna mini ta wurin kawo mini hari. Bari Ubangiji yă zama Alƙali, yă yanke hukunci tsakani Isra’ilawa da Ammonawa.”
I have not done you wrong, but you are doing me wrong by attacking me. Yahweh, the judge, will decide today between the people of Israel and the people of Ammon.”
28 Duk da haka sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika ba.
But the king of the people of Ammon rejected the warning Jephthah sent him.
29 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Yefta. Sai ya haye Gileyad da Manasse, ya ratsa ta Mizfa zuwa Gileyad, daga can kuma ya kai wa Ammonawa hari.
Then the Spirit of Yahweh came on Jephthah, and he passed through Gilead and Manasseh, and passed through Mizpah of Gilead, and from Mizpah of Gilead he passed through to the people of Ammon.
30 Yefta kuwa ya yi wa’adi da Ubangiji ya ce, “In ka ba da Ammonawa a hannuwana,
Jephthah made a vow to Yahweh and said, “If you give me victory over the people of Ammon,
31 duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”
then whatever comes out of the doors of my house to meet me when I return in peace from the people of Ammon will belong to Yahweh, and I will offer it up as a burnt offering.”
32 Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa.
So Jephthah passed through to the people of Ammon to fight against them, and Yahweh gave him victory.
33 Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf.
He attacked them and caused a great slaughter from Aroer as far as Minnith—twenty cities—and to Abel Keramim. So the people of Ammon were put under the control of the people of Israel.
34 Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi,’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko’ya.
Jephthah came to his home at Mizpah, and there his daughter came out to meet him with tambourines and with dancing. She was his only child, and besides her he had neither son nor daughter.
35 Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito!’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”
As soon as he saw her, he tore his clothes and said, “Oh! My daughter! You have crushed me with sorrow, and you have become one who causes me pain! For I have made an oath to Yahweh, and I cannot turn back on my promise.”
36 Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.”
She said to him, “My father, you have made a vow to Yahweh, do to me everything you promised, because Yahweh has taken vengeance for you against your enemies, the Ammonites.”
37 Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.”
She said to her father, “Let this promise be kept for me. Leave me alone for two months, that I may leave and go down to the hills and grieve over my virginity, I and my companions.”
38 Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba.
He said, “Go.” He sent her away for two months. She left him, she and her companions, and they grieved her virginity in the hills.
39 Bayan watanni biyu ɗin sai ta komo wurin mahaifinta ya kuwa yi da ita yadda ya yi wa’adi. Ita kuwa ba tă taɓa san namiji ba. Wannan ya zama al’ada a Isra’ila,
At the end of two months she returned to her father, who did with her according to the promise of the vow he had made. Now she had never slept with a man, and it became a custom in Israel
40 cewa kowace shekara’yan mata sukan fita kwana huɗu don yin bikin tunawa da’yar Yefta mutumin Gileyad.
that the daughters of Israel every year, for four days, would retell the story of the daughter of Jephthah the Gileadite.

< Mahukunta 11 >