< Yohanna 14 >

1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.
Não se turbe o vosso coração: crêdes em Deus, crêde tambem em mim.
2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.
Na casa de meu Pae ha muitas moradas; senão, eu vol-o teria dito; vou preparar-vos logar.
3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake.
E, se eu fôr, e vos preparar logar, virei outra vez, e vos levarei para mim mesmo, para que onde eu estiver estejaes vós tambem.
4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”
E já sabeis para onde vou, e sabeis o caminho.
5 Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”
Disse-lhe Thomé: Senhor, nós não sabemos para onde vaes; e como podemos saber o caminho?
6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.
Disse-lhe Jesus: Eu sou o caminho, e a verdade e a vida. Ninguem vem ao Pae, senão por mim.
7 Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”
Se vós me conhecesseis a mim, tambem conhecerieis a meu Pae; e já desde agora o conheceis, e o tendes visto.
8 Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.”
Disse-lhe Philippe: Senhor, mostra-nos o Pae, e isso nos basta.
9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’?
Disse-lhe Jesus: Estou ha tanto tempo comvosco, e não me tendes conhecido, Philippe? quem me vê a mim vê o Pae: e como dizes tu: Mostra-nos o Pae?
10 Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa.
Não crês tu que eu estou no Pae, e que o Pae está em mim? As palavras que eu vos digo não as digo de mim mesmo, mas o Pae, que está em mim, é quem faz as obras
11 Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.
Crêde-me que estou no Pae, e que o Pae está em mim: crêde-me, ao menos, por causa das mesmas obras.
12 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.
Na verdade, na verdade vos digo que aquelle que crê em mim tambem fará as obras que eu faço, e as fará maiores do que estas; porque eu vou para meu Pae
13 Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban.
E tudo quanto pedirdes em meu nome eu o farei, para que o Pae seja glorificado no Filho.
14 Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
Se pedirdes alguma coisa em meu nome, eu o farei.
15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.
Se me amaes, guardae os meus mandamentos.
16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, (aiōn g165)
E eu rogarei ao Pae, e elle vos dará outro Consolador, para que fique comvosco para sempre: (aiōn g165)
17 Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.
O Espirito de verdade, que o mundo não pode receber, porque não o vê nem o conhece: mas vós o conheceis, porque habita comvosco, e estará em vós.
18 Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
Não vos deixarei orphãos; voltarei para vós.
19 Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu.
Ainda um pouco, e o mundo não me verá mais, porém vós me vereis; porque eu vivo, e vós vivereis.
20 A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku.
N'aquelle dia conhecereis que estou em meu Pae, e vós em mim, e eu em vós.
21 Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Aquelle que tem os meus mandamentos e os guarda esse é o que me ama; e aquelle que me ama será amado de meu Pae, e eu o amarei, e me manifestarei a elle.
22 Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”
Disse-lhe Judas (não o Iscariotes): Senhor, d'onde vem que te has de manifestar a nós, e não ao mundo?
23 Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.
Jesus respondeu, e disse-lhe: Se alguem me ama, guardará a minha palavra, e meu Pae o amará, e viremos para elle, e faremos n'elle morada.
24 Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.
Quem me não ama não guarda as minhas palavras; e a palavra que ouvistes não é minha, mas do Pae que me enviou.
25 “Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku.
Tenho-vos dito estas coisas, estando ainda comvosco.
26 Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.
Mas aquelle Consolador, o Espirito Sancto, que o Pae enviará em meu nome, esse vos ensinará todas as coisas, e vos fará lembrar de tudo quanto vos tenho dito.
27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
Deixo-vos a paz, a minha paz vos dou: não vol-a dou como o mundo a dá. Não se turbe o vosso coração, nem se atemorize.
28 “Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.
Ouvistes que eu vos disse: Vou, e venho para vós. Se me amasseis, certamente exultarieis por ter dito: Vou para o Pae; porque meu Pae é maior do que eu.
29 Na faɗa muku tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata.
Eu vol-o disse agora antes que aconteça, para que, quando acontecer, vós acrediteis.
30 Ba zan ƙara yi muku magana ba, gama mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Ba shi da iko a kaina,
Já não fallarei muito comvosco; porque já se approxima o principe d'este mundo, e nada tem em mim.
31 amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni. “Ku zo, mu bar nan.
Mas para que o mundo saiba que eu amo o Pae, e que faço como o Pae me mandou, levantae-vos, vamo-nos d'aqui.

< Yohanna 14 >