< Ayuba 12 >
2 “Ba shakka ku ne mutanen nan, hikima za tă mutu tare da ku!
“Truly then you are the people with whom wisdom itself will die!
3 Amma ni ma ina da hankali kamar ku; ba ku fi ni ba. Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba?
But I also have a mind; I am not inferior to you. Who does not know such things as these?
4 “Na zama abin dariya ga abokaina, ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini, duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!
I am a laughingstock to my friends, though I called on God, and He answered. The righteous and upright man is a laughingstock.
5 Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa.
The one at ease scorns misfortune as the fate of those whose feet are slipping.
6 Amma wurin zaman’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.
The tents of robbers are safe, and those who provoke God are secure— those who carry their god in their hands.
7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka, ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
But ask the animals, and they will instruct you; ask the birds of the air, and they will tell you.
8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka, ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
Or speak to the earth, and it will teach you; let the fish of the sea inform you.
9 Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
Which of all these does not know that the hand of the LORD has done this?
10 Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan’yan adam.
The life of every living thing is in His hand, as well as the breath of all mankind.
11 Ko kunne ba ya gwada kalmomi kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?
Does not the ear test words as the tongue tastes its food?
12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
Wisdom is found with the elderly, and understanding comes with long life.
13 “Allah ne mai iko da kuma hikima, shawara da ganewa nasa ne.
Wisdom and strength belong to God; counsel and understanding are His.
14 Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba; in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba.
What He tears down cannot be rebuilt; the man He imprisons cannot be released.
15 Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări; in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya.
If He holds back the waters, they dry up, and if He releases them, they overwhelm the land.
16 Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara; mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne.
True wisdom and power belong to Him. The deceived and the deceiver are His.
17 Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.
He leads counselors away barefoot and makes fools of judges.
18 Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso.
He loosens the bonds placed by kings and fastens a belt around their waists.
19 Yakan ƙasƙantar da firistoci yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa.
He leads priests away barefoot and overthrows the established.
20 Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru yakan kawar da hikimar dattawa.
He deprives the trusted of speech and takes away the discernment of elders.
21 Yakan sa masu iko su ji kunya yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi.
He pours out contempt on nobles and disarms the mighty.
22 Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske;
He reveals the deep things of darkness and brings deep shadows into light.
23 yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.
He makes nations great and destroys them; He enlarges nations, then disperses them.
24 Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.
He deprives the earth’s leaders of reason and makes them wander in a trackless wasteland.
25 Suna lallube cikin duhu ba haske; yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.
They grope in the darkness without light; He makes them stagger like drunkards.