< Ishaya 57 >

1 Mai adalci yakan mutu, ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa; an kwashe mutanen kirki, ba kuwa wanda ya fahimta cewa an kwashe masu adalci don a tsame su daga mugunta.
The righteous man perisheth, and no one layeth it to heart; And pious men are taken away, and none considereth That because of the evil the righteous man is taken away.
2 Waɗanda suke aikata abin da yake daidai sukan shiga da salama; sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.
He entereth into peace; He resteth in his bed, Every one that walketh in uprightness.
3 “Amma ku, ku matso nan, ku’ya’ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinata da karuwai!
But draw near hither, ye sons of the sorceress, Ye brood of the adulterer and the harlot!
4 Wane ne kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke masa gwalo kuna kuma fitar da harshe? Ashe, ku ba tarin’yan tawaye ba ne, zuriyar maƙaryata?
Of whom do ye make your sport, And at whom do ye make wide the mouth, And draw out the tongue? Are ye not rebellious children, a treacherous brood?
5 Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oak da kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa; kuna miƙa hadayar’ya’yanku a rafuffuka da kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu.
Burning with lust for idols Under every green tree, Slaying children in the valleys, Under the clefts of the rocks?
6 Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku; su ɗin, su ne rabonku. I, gare su kuka kwarara hadayu na sha kuka kuma miƙa hadayu na gari. Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri?
With the smooth stones of the valley is thy portion; These, these are thy lot; Here thou pourest out thy drink-offering, And presentest thy meat-offering; Can I see such things, and be at rest?
7 Kun yi gadonku a dogayen duwatsu masu tsayi da kuma a tudu mai tsawo; a can kuka haura don ku miƙa hadayunku.
Upon a high and lofty mountain settest thou thy bed; Thither dost thou go up to offer sacrifice;
8 A bayan ƙofofi da madogaran ƙofofi kuka kafa alamun gumakanku. Kuka yashe ni, kuka kware gadonku, kuka kwanta a kansa kuka fadada shi; kuka kuma ƙulla yarjejjeniya da waɗanda kuke ƙaunar gadajensu, kuka dubi tsiraicinsu.
Behind the doors and the posts dost thou place thy memorial; Thou departest from me, and uncoverest, and ascendest, and enlargest thy bed. Thou makest an agreement with them; Thou desirest their bed; Thou choosest a place.
9 Kuka tafi wurin Molek da man zaitun kuka kuma riɓaɓɓanya turarenku. Kuka aika jakadunku can da nisa; kuka gangara zuwa cikin kabari kansa! (Sheol h7585)
Thou goest to the king with oil, And takest much precious perfume; Thou sendest thine ambassadors afar, Yea, down to the under-world. (Sheol h7585)
10 Kuka gaji cikin dukan al’amuranku, amma ba ku iya cewa, ‘Aikin banza ne ba.’ Kuka sami sabuntar ƙarfinku, ta haka ba ku suma ba.
In the length of thy journeys thou hast wearied thyself, But thou sayest not, “I will desist”; Thou yet findest life in thy hand, Therefore thou art not discouraged.
11 “Wa ya sa ku fargaba, kuna jin tsoro har kuka yi mini ƙarya, ba ku kuma tuna da ni ba balle ku yi tunanin wannan a zukatanku? Ba don na daɗe ina shiru ba ne ya sa ba kwa tsorona?
On account of whom art thou anxious, and of whom art thou afraid, that thou hast proved false, And hast not remembered me, nor laid it to heart? Behold, I have been silent a long time; Therefore thou fearest me not.
12 Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku, ba kuwa za su amfane ku ba.
But now I announce thy deliverance, And thy works do not profit thee.
13 Sa’ad da kuka nemi taimako, bari tarin gumakanku su cece ku! Iska za tă kwashe dukansu tă tafi, ɗan numfashi kawai zai hura su. Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa zai gāji ƙasar ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”
When thou criest, let thy host of idols deliver thee! But the wind shall bear them all away; A breath shall take them off; But he that putteth his trust in me Shall possess the land, And shall inherit my holy mountain.
14 Za a kuma ce, “Ku gina, ku gina, ku gyara hanya! Ku kawar da abubuwan sa tuntuɓe a hanyar mutanena.”
Men shall say, Cast up, cast up, prepare the road; Remove every obstruction from the way of my people!
15 Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.
For thus saith the high and lofty One That inhabiteth eternity, whose name is Holy: I dwell in the high and holy place; With him also that is of a contrite and humble spirit; To revive the spirit of the humble, And to revive the heart of the contrite ones.
16 Ba zan tuhume su har abada ba, ba kuwa kullum zai yi fushi ba, gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana, shi numfashin mutumin da na halitta.
For I will not contend forever, Nor will I be always angry; For life would fail before me, And the souls which I created.
17 Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa; na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi, duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa.
For the guilt of his covetousness I was angry; I smote him, I hid myself, and was angry; But yet he went on perversely in the way of his heart.
18 Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi; zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi,
I have seen his ways, yet will I heal him; I will guide him, and I will restore comfort To him and to his mourners;
19 ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila. Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,” in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.”
I create the fruit of the lips. Peace, peace to him that is far off, and to him that is nigh, Saith Jehovah; I will heal him.
20 Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, wanda ba ya natsuwa, wanda raƙumansa sukan kawo gurɓacewa da tabo.
But the wicked is like the troubled sea, Which cannot rest, Whose waters cast up mire and dirt.
21 “Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna.
There is no peace, saith my God, for the wicked.

< Ishaya 57 >